Laraba 6 Mayu 2026 - 21:34
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (21) | Faɗin Mulkin Imam Mahdi (AJ) da Cibiyarsa

Hauza/ Akwai hadisai da yawa da suka bayyana sarai cewa mulkin Imam Mahdi (AS) zai zama na duniya ne baki ɗaya.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran  Hauza ya ruwaito, jerin bahasin Mahdawiyya mai taken “Zuwa Ga Al’umma Mai Manufa”, ana gabatar da shi ne domin yada koyarwa da ma’arifofi da suka shafi Imam Mahdi (AJ) ga ku masu daraja.

Babu shakka mulkin Imam Mahdi (AS) mulki ne na duniya baki ɗaya, domin shi ne wanda aka yi wa dukkan bil’adama alkawari kuma shi ne mai cika burin dukkan mutane. Saboda haka dukkan alheri da kyawawan abubuwan da za su bayyana a karkashin mulkinsa za su mamaye dukkan doron ƙasa.

Akwai ruwayoyi da dama da suka nuna a fili cewa mulkin Imam Mahdi (AS) zai kasance na duniya baki ɗaya. Misali, a cikin wata magana daga Manzon Allah (SAWA) an ruwaito cewa Allah Madaukaki Ya ce:

«... وَعِزَّتِي وَجَلَالِي لَأُظْهِرَنَّ بِهِمْ دِينِي وَلَأُعْلِيَنَّ بِهِمْ كَلِمَتِي وَلَأُطَهِّرَنَّ الْأَرْضَ بِآخِرِهِمْ مِنْ أَعْدَائِي وَلَأُمَلِّكَنَّهُ مَشَارِقَ الْأَرْضِ وَمَغَارِبَهَا ...»  (كمال الدين، ج 1، ص 256)

Ma’ana: “Na rantse da girma da ɗaukakata cewa zan bayyanar da addinina ta hannunsu (Imamai goma sha biyu) har ya rinjayi dukkan addinai, kuma ta hannunsu zan ɗaukaka kalmata. Kuma da (tashin) na ƙarshe daga cikinsu (Imam Mahdi AS) zan tsarkake duniya daga maƙiyana, kuma zan ba shi iko a kan gabas da yammacin duniya.” (Kamal ad-Din, j:1, s:256)

Haka kuma Imam Muhammad Baƙir (AS) ya ce:

«الْقَائِمُ مِنَّا ... يَبْلُغُ سُلْطَانُهُ الْمَشْرِقَ وَالْمَغْرِبَ وَيُظْهِرُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ بِهِ دِينَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ فَلَا يَبْقَى فِي الْأَرْضِ خَرَابٌ إِلَّا قَدْ عُمِرَ ...»  (كمال الدين، ج 1، ص 330)

Ma’ana: “Qa’im (AS) daga cikinmu ne (Ahlulbait). Mulkinsa zai kai gabas da yamma, kuma Allah zai bayyanar da addininsa ta hannunsa har ya rinjayi dukkan addinai ko da mushrikai ba su so. A zamanin mulkinsa babu wani wuri a duniya da ya lalace da zai rage ba tare da an gyara shi ba.” (Kamal ad-Din, j:1, s:330)

Cibiyar Mulkin Imam Mahdi (AJ)

Amma cibiyar mulkin duniya na Imam Mahdi (AS) ita ce birni mai tarihi na Kufa. A wancan lokaci birnin zai faɗaɗa sosai har ya haɗa da Najaf, wadda take a ‘yan kilomita kaɗan daga Kufa. Saboda haka ne a wasu ruwayoyi aka ambaci Kufa, a wasu kuma aka ambaci Najaf a matsayin cibiyar mulkin Imam Mahdi (AS).

Imam Ja’afar al‑Sadiƙ (AS) ya faɗa a cikin wata doguwar ruwaya cewa:

«... دَارُ مُلْكِهِ الْكُوفَةُ وَمَجْلِسُ حُكْمِهِ جَامِعُهَا ...» (بحار الأنوار، ج 53، ص 11)

Ma’ana: “Cibiyar mulkinsa (Imam Mahdi AS) ita ce Kufa, kuma wurin da zai yi hukunci shi ne masallacin Kufa.” (Bihar al-Anwar, j:53, s:11)

Ya kamata a lura cewa tun zamanin da birnin Kufa yana da matsayi na musamman a wajen Ahlul Baitin Manzon Allah (SAWA), kuma shi ne fadar mulkin Amirul Muminin Imam Ali (AS). Haka nan masallacin Kufa yana daga cikin manyan masallatai guda huɗu masu daraja a duniyar Musulunci. A cikin wannan masallaci ne Imam Ali (AS) yake yin sallah da kuma karanta huduba, kuma a nan ne yake yin shari’a da hukunci. A ƙarshe ma a cikin mihrabin wannan masallaci ne aka shahadantar da shi.

Wannan bahasi zai ci gaba…

An ciro daga littafin "Negin-e Afarinesh", tare da ɗan gyara.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha