Jummaʼa 10 Afirilu 2026 - 14:31
Sheikh Zakzaky ya Jagoranci Taron Tunawa da Kwanaki Arba’in da Shahadar Sayyid Qa'id Khamenei a Abuja

Hauza/ Jagoran Harakar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya gudanar da addu’a da taron tunawa da cika kwanaki arba’in da shahadar Sayyid Ali Khamenei (R) a gidansa dake birnin Abuja, a ranar Alhamis 21 ga Shawwal 1447 Hijira (9 ga Afrilu, 2026).

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a sanarwar da ofishin Sheikh Zakzaky ya fitar, malamin ya bayyana a jawabinsa cewa, shahadar Sayyid Qa'id Khamenei ta bayyana wasu gaskoyi irin na filin Karbala, wanda shahadar Imam Husaini (A.S) ta bayyana wa al’ummar Musulmi da hatta bil’adama baki ɗaya.

Ya ce Imam Husaini (A.S) ya sadaukar da rayuwarsa don bayyana iyakar tsakanin gaskiya da ƙarya, inda ya nuna a ina adalci yake da kuma waɗanda suke gefen zalunci. 

Sheikh Zakzaky ya ƙara da cewa: “Abokan gabar Imam Husaini (A.S) sun kewaye shi tare da iyalinsa a tsakar hamadar Karbala suna son su kashe su cikin shiru, amma bayan ɗan lokaci gaskiya ta bayyana, kuma masu laifin sun tozarta kansu.”

Jagoran Harkar Musulunci ya ce Sayyid Qa'id Khamenei ma ya san haɗarin da ke gaba, amma duk da haka bai janye daga gaskiya ba kuma bai bar tafarkinsa ba. 

Sheikh Zakzaky ya tuna da yunƙurin kashe Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da aka yi a shekarar 1980 wanda ya jikkata shi ƙwarai, inda ya ce: “A lokacin hannunsa na dama ya samu mummunan rauni da bai sake yin aiki kamar da ba, amma duk da haka ya ci gaba da fafutukar sa tsawon shekaru.”

Ya kuma bayyana cewa, wadanda suka kasance tare da shi sun san kasadar da ke gabansu, amma kamar yadda sahabban Imam Husaini suka tsaya tare da shi, haka ma suka tsaya tare da jagoransu ba tare da ja da baya ba.  

Sheikh Zakzaky ya ce: “Makiya sun ɗauka cewa da zarar sun kashe jagororin su, motsin gwagwarmaya zai ƙare, amma abin da ya faru daga baya ya nuna akasin haka.”

Sheikh Zakzaky (H) ya yi nuni da hare-haren da aka kai kan fararen hula, yana mai cewa: “Har ma yara da ɗaliban makaranta sun shiga cikin wadanda aka kai wa hari, abin da ke nuna cewa jama’a talakawa ne ainihin abin da ake niyya.”

Ya kuma lura da barazanar da wasu jami’an Amurka suka yi wa Iran, yana cewa hakan ya bayyana ainihin halayensu na ƙiyayya da Musulunci.  

Jagoran Harakar Musulunci ya ƙara da cewa abubuwan da suka faru sun bayyana gaskiya ga al’umma, inda ya ce: “Wannan yana nuna cewa abokan gaba suna adawa ne da juyin juya halin Musulunci da kuma ‘yancin kasashen Musulmi.”

Har ila yau Sheikh Zakzaky ya yaba da juriya da Iran ke nuna wa duk da matsin lamba, yana mai cewa: “Iran ba wai kawai tana kare kanta ba ce, amma kuma tana zama abin koyi ga dukkan al’ummomin da ke neman adalci da ‘yanci.”

A ƙarshe, Sheikh Zakzaky ya ce: “Za mu ci gaba da rike alkawarinmu, kuma ba za mu watsar da tafarkin shuhada da suka sadaukar da rayuwarsu ba.”

A ƙarshen taron, Sheikh Zakzaky ya jagoranci karatun Addu’ar Kumayl, wadda ake karantawa a daren Juma’a, domin neman rahama ga Shahid Sayyid Ali Khamenei (Q) da sauran shahidai, tare da neman kariya ga mujahidai.  

Taron Tunawa da Kwanaki Arba’in da Shahadar Sayyid Qa'id Khamenei da Sheikh Zakzaky ya Jagoranta a Abuja

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha