A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal Muslimin Hamid Maliki, mataimakin shugaban Hauzar Ilimi ta Qom, a yayin gudanar da darasin akhlaƙ a makarantar Hauza ta Ayatullah Behjat (RA) a Qom, ya yi ishara da halin da ƙasar ke ciki da kuma muhimmancin kiyaye shirye‑shiryen ilimi da na aikace‑aikace ga ɗaliban Hauza. Ya jaddada ci gaba da karatu tare da kula da bukatun kare ƙasa da jihadi.
Ya bayyana cewa: “Har yanzu ba a samu damar yin zaman makoki ga Imam shahidi ba, kuma muna fata wannan yaƙi zai ƙare cikin nasara bayyananniya nan ba da jimawa ba.” Ya ƙara da cewa bayan ƙarewar wannan yanayi, za a iya nazarin tarihin rayuwa da salon rayuwar shahidai cikin natsuwa domin cin gajiyar darussan da ke cikinsu.
Mataimakin Shugaban Hauzar Ilimi ta Qom ya kuma ce a irin wannan lokaci ya kamata a ƙara komawa ga Imam Mahdi (AJ) domin neman taimako, tare da dagewa kan addu’a da istigasa gare shi.
Ya kuma yaba da yadda makarantar Ayatullah Behjat (RA) ke gudanar da ayyukanta da kuma ƙoƙarin malamai. Dangane da koyar da ɗaliban Hauza a halin yanzu, ya ce: "ainihin manufar ita ce a ci gaba da darussa na asali, amma ta yadda hakan ba zai rage rawar da ɗalibai ke takawa a fagen jihadi da sauran wuraren da ake bukatar su ba.
Ya ƙara da cewa an gudanar da tarurruka da shirye‑shirye da dama, kuma yanke shawara kan ilimi dole ne ya kasance cikin hikima tare da la’akari da bukatun da ke cikin fagen aiki. A halin yanzu akwai wani irin karo tsakanin ci gaba da dukkan shirye‑shiryen karatu gaba ɗaya da kuma halartar fagen aiki; saboda haka ya zama dole a kiyaye darussa na asali, amma ba tare da cutar da ayyukan fage ba.
Hujjatul Islam Wal Muslimin Maliki ya jaddada muhimmancin kula ta musamman da matakan farko, na biyu da na uku na karatun Hauza, yana mai cewa bai kamata ginshiƙin ilimin ɗalibai, musamman darussa na asali ba, ya samu rauni, domin duk wani rauni a wannan mataki zai yi tasiri a gaba.
Ya kuma yi nuni da bukatar tsara shirye‑shirye na lokacin bazara, yana cewa: "idan yaƙin da aka tilasta ya ƙare da wuri, ya kamata a shirya ƙarin shirye‑shiryen karatu a lokacin bazara. A halin yanzu kuma ya kamata a ƙarfafa ilimi tare da kiyaye haɗin kai tsakanin ɗalibai."
Mataimakin Shugaban Hauzar Ilimi ta Qom ya yi ishara da abubuwan da suka faru kwanan nan da kuma hare‑haren da abokan gaba suka kai kan muhimman abubuwan samar da makamashi. Ya ce abokan gaba suna gwada Iran, amma Jamhuriyar Musulunci ta fahimci cewa dole ne ta tsaya da ƙarfi da cikakken shiri a gaban maƙiya marasa hankali, kuma hakan yana ƙara nuna muhimmancin juriya da ƙara yin taka‑tsantsan.
Ya yi nuni da yanayin al’umma da kuma canje‑canjen farkon shekarun juyin juya halin Musulunci na Iran, sannan ya tabo lamarin shahadar Shahid Ayatullah Beheshti. Ya ƙara da cewa: "A ranakun kafin shahadarsa, wasu mutane sun rika yin shagube da sukar sa a tituna, amma bayan shahadarsa, waɗannan titunan ne suka cika da jama’a masu makoki — abin da ya zama alamar ɗaya daga cikin sunnonin Allah da mu’ujizar jinin da ya rinjayi takobi."
Mataimakin Shugaban Hauzar Ilimi ta Qom ya ce: "Abokan gaba a yau ma suna ƙoƙarin, ta hanyar kafafen yada labaran ƴan adawa, su saka tsoro da rashin bege a zukatan al’ummar Iran. Ya bayyana cewa ayar “إِن تَنصُرُوا اللَّهَ یَنصُرْکُمْ” ba ta nufin hana makiya kawai ba, sai dai tana haifar da tasiri da dama kamar ƙarfafa jarumta, tsayin daka, ƙarfafa ruhin juriya da haɓaka ruhaniya."
Malamin na Hauzar Ilimi ya bayyana yadda ɗaliban Hauza ke taka rawa a ayyukan maukib da jihadi, yana mai cewa: "Ruhin juriya ya ƙaru a cikin mutane, kuma a yau, da yawa daga cikin waɗanda da suka gabata suna tsoron mutuwa, rashin tsaro ko rikici, sun koma fage cikin bege, tsayin daka da amincewa da alkawuran Allah."
Mataimakin Shugaban Hauzar Ilimi ta Qom ya jaddada cewa: "Idan jama’a suka ci gaba da juriya da tsayin daka, alkawarin taimakon Allah zai tabbata, kuma nasara za ta kasance a bangaren gaskiya."
Hujjatul Islam Wal Muslimin Maliki ya kuma nuna cewa: "Kowace zuriya ta shaida irin gwagwarmaya da jihadi daban‑daban, kuma yanzu wannan lokaci ya ba sabon ƙarni damar fahimtar ma’anar kasancewa a fage, sadaukarwa da tsayuwa cikin ƙarfi."
Ya ƙara cewa: "Fagen gwagwarmaya na yau ba kawai a filin yaƙi yake ba, har ma a titi, gida da jami’a, waɗanda duk wurare ne na gina mutum. Wannan yanayin, in ji shi, zai iya haifar da tarbiyyar sabuwar ƙarni don shekaru masu zuwa — ƙarni wanda ke ci gaba da tafarkin muƙawama ta hanyar ƙirƙirar tarihi da rubuta ƙwarewa."
Mataimakin Shugaban Hauzar ya bayyana muhimmancin tunannin sojoji da shahidai, yana cewa: "Tunanin su yana da tasiri sosai wajen gina mutum da al’umma. Idan aka rubuta waɗannan kwarewa kuma aka adana su, za su zama ginshiƙi babba a gina makoma. Da yawa daga cikin sojojin sun ayyana ma’anar rayuwarsu ne ta hanyar irin waɗannan tunani da darussan ruhaniya."
Ya kuma bada wani labari lokacin da ya dawo daga fagen yaƙi, inda ya halarci darasin tafsirin Ayatullah Uzma Jawadi Amuli. Ya ce: "a waɗannan ranakun, na fara kallon fagen jihadi da idanu na daban; lokacin da malamin ya ce zuwa fagen yaƙi tamkar biyan bashin mutum ne ga Allah, sai na fahimci ma’anar zurfin jihadi fiye da da."
Malamin na Hauza ya jaddada cewa: "Abin da Jagoran Juyin Juya Hali ya bayyana game da wannan lokaci, yana nuna wahayi da fahimtar zurfin halin da ake ciki. Yanzu kuma al’umma suna cikin fage fiye da da, suna haifar da ɓacin rai ga makiya."
Ya ƙara da cewa: "Abokan gaba sun yi kuskure a lissafinsu, suna tunanin cewa da matsin lamba da barazana za su iya karya zuciyar al’ummar Iran. Amma gaskiya ita ce: mutane suna cikin fage da sabon ƙwarin gwiwa da jarumta, kuma wannan tsayuwa alama ce ta tashin ruhaniya da wahayi a cikin al’umma."
A ƙarshe, Hujjatul Islam Wal Muslimin Maliki ya ce: "Dole ne mu ci gaba da tafarkin muƙawama. Ko da yake wannan yanayi yana da wuya kuma da tsada, amma yana da amfani domin yana gina mutane da motsa al’umma." Ya ƙare da fatan cewa da ci gaba da muƙawama, taimakon Allah zai tabbata.
Ra'ayinka