Asabar 14 Maris 2026 - 00:47
Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Hauza/ Kamar sauran al'ummar Musulmin duniya da ma'abota yanci, ɗaliban Harkar Musulunci karkashin jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) dake karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun halarci Muzaharar Qudus ta shekarar 1447 a birnin Qom domin nuna goyon bayansu da tausayawa ga raunanan al'ummar Falasɗinu.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom tare da haɗin gwiwar Harisawa, Jaishi Shahid Sayyid Ahmad Zakzaky (JASAZ) Intizar da Kasshafatul Imam Mahdi (AF) na Harkar Musulunci karkashin jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) dake karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun shirya tare da gudanar da Muzaharar Qudus ta shekarar 1447 a birnin Qom.

Muzaharar, wadda ita ce kalar ta ta farko da ta haɗa dukkanin ɗaliban ƴan Hauza da kuma na Jami'o'i daban-daban da suke kasar ta Iran, an fara ta ne daga Haramin Sayyida Ma'asuma (SA) da misalin karfe sha daya na safe (11:00am) zuwa masallacin Juma'ar Musallaye Quds Qom inda aka rufe ta.

Mahalarta Muzaharar suna tafe cikin tsari dauke da hotunan Imam Khumaini (Q), Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamenei (R), Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei (H) da Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) da shahidan Harkar Musulunci, sai kuma tutocin Iran, Falasɗinu da Nijeriya suna tafe suna rera taken goyon bayan Palastinu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da jaddada mubaya'a ga sabon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei. A gefe guda kuma suna rera taken la'anta da tsinuwa ga gwamnatin Sahyoniyawa da Amurka da dukkan Azzalumai.

A ƙarshen Muzaharar, Hujjatul Islam wal Muslimin Sheikh Abdullahi Ahmad Fudiyya ya gabatar da jawabin rufewa sai kuma Hujjatul Islam Sheikh Muhammad Sani Malafa ya rufe da addu'a.

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Daliban Harkar Musulunci Mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Iran Sun Gudanar da Muzaharar Qudus a Birnin Qom

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha