Talata 25 Agusta 2026 - 15:35
An Jaddada Muhimmancin Koyi da Ɗabi’un Annabi (S.A.W.A) Wajen Gina Al’umma ta Gari

Hauza/ Malamin Hauzar Ilimi ta Qum, Hujjatul Islam wal Muslimin Abdulhamid Mardani, ya bayyana cewa bin ɗabi’u da Sirar Annabi Muhammad (SAWA) na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen gyara rayuwar mutum da gina al’umma mai kyawawan halaye.

Hujjatul Islam Mardani ya bayyana hakan ne a wata hira da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, inda ya yi bayani kan muhimmancin ɗabi’a (akhlaƙ) a cikin rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W.A), yana mai cewa Alƙur’ani Mai Girma ya bayyana Manzon Allah (S.A.W.A) da cewa: “Kuma lallai kana kan ɗabi’a mai girma.”
Ya ce wannan aya tana nuna babban matsayi da kyawawan ɗabi’u suke da shi a rayuwar Annabi (S.A.W.A), domin ɗabi’a mai girma ta kasance cikin halayensa da ayyukansa. Saboda haka, duk wanda yake son fahimtar ainihin ɗabi’ar Musulunci ya kamata ya yi nazari kan Sirar Manzon Allah (S.A.W.A).
Malamin ya jaddada cewa Annabi Muhammad (S.A.W.A) ba malamin ɗabi’a kawai ba ne, a’a, rayuwarsa ita ce cikakken misali na kyawawan ɗabi’un Musulunci. Ya ce ya kamata a koyi yadda Annabi (S.A.W.A) yake magana, yadda yake mu’amala da mutane, da yadda yake fuskantar matsaloli da yanayi daban-daban.
Ya kuma yi kira ga Musulmi da su koma ga Sunnah da Sirar Annabi (S.A.W.A), musamman a wannan zamani da mutane ke fuskantar ma’aunai da ra’ayoyi daban-daban game da ɗabi’a. A cewarsa, bai kamata mutum ya ɗauki abin da ya gada daga muhallinsa a matsayin ma’aunin ɗabi’a na ƙarshe ba, sai dai ya koma ga koyarwar Manzon Allah (S.A.W.A).
HujjatulIslam Mardani ya bayyana cewa sanin Sirar Annabi (S.A.W.A) bai kamata ya tsaya ga karatu da samun bayanai kawai ba, domin manufar sanin Sira ita ce a mayar da koyarwarta zuwa aikace-aikace a rayuwar yau da kullum.
Ya ce ya kamata Musulmi su yi nazari kan yadda Annabi (S.A.W.A) yake mu’amala da iyalansa, abokansa, maƙwabtansa da sauran jama’a, da kuma yadda yake gudanar da harkokin kasuwanci da kiyaye haƙƙin mutane. A cewarsa, waɗannan halaye ne suke samar da cikakkiyar Sirar Annabi wadda za ta iya zama abin koyi ga al’umma.
Hujjatul Islam Mardani ya kuma bayyana cewa duniya a yau tana matuƙar buƙatar ɗabi’a da ruhaniya, musamman saboda matsalolin akhlaƙ da zamantakewa da ake fuskanta. Ya ce ɗabi’ar Annabi Muhammad (S.A.W.A) na iya zama muhimmiyar hanya wajen sake gina ɗabi’ar mutum da ta al’umma.
Ya ƙara da cewa ɗabi’ar Annabi (S.A.W.A) ta ƙunshi bautar Allah, tauhidi, soyayya, adalci, yafiya, mutuncin ɗan Adam da kiyaye haƙƙin wasu. Saboda haka, duk yadda mutum ya kusanci ɗabi’ar Manzon Allah (S.A.W.A), haka zai ƙara kusantar Allah Maɗaukakin Sarki da samun farin ciki na gaskiya.
A ƙarshe, Hujjatul Islam wal Muslimin Abdulhamid Mardani ya yi addu’ar Allah Ya ba Musulmi ikon yin koyi da Annabi Muhammad (S.A.W.A) a dukkan ɓangarorin rayuwa, yana mai jaddada cewa sanin Sirar Annabi mataki ne na farko, amma aiwatar da koyarwarsa shi ne ainihin hanyar kaiwa ga kololuwar kyawawan ɗabi’u da gina al’umma ta gari.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha