Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Dangantakar da ke tsakanin hankali da imani na daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a falsafar addini da ilimin tauhidi. Wasu ra’ayoyi suna ɗaukar imani a matsayin wanda ya fi hankali, har ma suna fassara su a matsayin abubuwa biyu masu saɓani da juna. A al’adar Kiristanci, ana kiran wannan ra’ayi da “Imaniyya” (Fideism), kuma ya bayyana ta hanyoyi daban-daban.
Tambaya: Menene Imaniyya, kuma me ya sa ta yaɗu a Kiristanci amma Musulmi ba sa karɓarta?
Imaniyya ta yaɗu a cikin al’adar Kiristanci, kuma ta bayyana da siffofi daban-daban; tun daga Imaniyya mai tsanani, wadda take kallon hankali a matsayin wanda yake karo da imani, zuwa Imaniyya matsakaiciya ta Augustine, wadda take ɗaukar imani a matsayin sharadin fara fahimta.
Ana iya danganta tushen wannan tunani da tsarin ilimin tauhidin Kiristanci da wasu koyarwarsa, kamar “Trinity” (Uku-cikin-ɗaya), “Incarnation” (Allah ya ɗauki siffar mutum), da “Original Sin” (asalin zunubi), waɗanda ba su yi daidai da fahimtar hankali ba.
A gefe guda kuma, a al’adar Musulunci, hankali yana daga cikin ingantattun hanyoyin samun ilimin addini, kuma ba a karɓar imani a kan tushen addini ba tare da yin hukunci da hankali ba.
Saboda haka, bisa fahimtar Musulmi, Imaniyya a wannan ma’anar ba abin karɓa ba ce ko kaɗan.
Madogara: Cibiyar Amsa Tambayoyin Addini ta Ƙasar Iran
Ra'ayinka