Lahadi 16 Agusta 2026 - 21:56
Sharhin Hadisi Game da Hirar Ƙarshe Tsakanin Manzon Allah (S) da Sayyida Fatimatuz Zahra (SA)

Hauza/ Tarihin rayuwar Manzon Allah (S) da yadda yake mu'amala da Sayyida Fatima Az-Zahra (SA), yana daga cikin kyawawan misalan girmama matsayin mace da iyali a Musulunci. Shahidin Jagora Juyin Juya Halin Musulunci, Imam Sayyid Ali Khamenei (Allah Ya jiƙansa), ya yi bayani kan fannoni daban-daban na wannan kyakkyawar alaƙa, yana dogaro da wata ruwaya daga A’isha.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shahid Ayatullah Imam Khamenei (Q), a farkon zaman karatun Bahsul Kharij na Fiƙihu, ya yi bayani da sharhin wani hadisi da ya shafi hirar ƙarshe tsakanin Manzon Allah (S) da Sayyida Fatima Zahra (S). Ga rubutun bayanin:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da iyalansa tsarkaka, kuma tsinuwar Allah ta tabbata ga maƙiyansu baki ɗaya.

عَن عائِشَةَ بِنتِ طَلحَةَ عَن عائِشَةَ قالَت ما رَأَیتُ مِنَ النّاسِ اَحَداً اَشبَهَ کَلاماً وَ حَدیثاً بِرَسولِ اللهِ (صَلَّی اللهُ عَلَیهِ وَ آلِه) مِن فاطِمَةَ. کانَت اِذا دَخَلَت عَلَیهِ رَحَّبَ بِها وَ قَبَّل یَدَیها وَ اَجلَسَها فی مَجلِسِهِ فَاِذا دَخَلَ عَلَیها قامَت اِلَیهِ فَرَحَّبَت بِهِ وَ قَبَّلَت یَدَیهِ وَ دَخَلَت عَلَیهِ فی مَرَضِهِ فَسارَّها فَبَکَت ثُمَّ سارَّها فَضَحِکَت. فَقُلتُ کُنتُ اَریٰ لِهٰذِهِ فَضلاً عَلَی النِّساءِ فَاِذا هِیَ امرَأَةٌ مِنَ النِّساءِ فَبَینَما هِیَ تَبکیٰ اِذ ضَحِکَت. فَسَأَلتُها فَقالَت اِنّی اِذَن لَبَذِرَةٌ. فَلَمّا تُوَفِّیَ رَسولُ اللهِ (صَلَّی اللهُ عَلَیهِ وَ آلِه) سَأَلتُها فَقالَت اِنَّهُ اَخبَرَنی اَنَّهُ یَموتُ فَبَکَیتُ ثُمَّ اَخبَرَنی اَنّی اَوَّلُ اَهلِهِ لُحوقاً بِهِ فَضَحِکتُ.(۱)

Daga A’isha ’yar Ɗalha, daga A’isha, ta ce: “Ban taɓa ganin wani daga cikin mutane da ya fi kama da Manzon Allah (S.A.W.A) wajen magana da zance kamar Fāɗima ba. Idan ta shiga wurinsa, yana maraba da ita, yana sumbatar hannayenta, sannan ya zaunar da ita a wurin zamansa. Idan kuma ya shiga wurinta, sai ta tashi ta tarye shi, ta yi masa maraba, sannan ta sumbaci hannayensa. A lokacin da ta je wurinsa yayin rashin lafiyarsa, sai ya yi mata magana a ɓoye, ta yi kuka. Daga nan sai ya sake yi mata magana a ɓoye, sai ta yi murmushi ta yi dariya. Sai na ce: ‘Na kasance ina ganin cewa wannan matar tana da fifiko a kan sauran mata, amma yanzu na ga cewa ita ma mace ce daga cikin mata; domin a lokacin da take kuka, sai ga ta ta yi dariya.’

Sai na tambaye ta, sai ta ce: ‘Ta ya zan tona asirin abin da aka faɗa min.’ Bayan Manzon Allah (S.A.W.A) ya rasu, sai na sake tambayarta. Ta ce: ‘Ya sanar da ni cewa zai rasu, sai na yi kuka. Daga nan kuma ya sanar da ni cewa ni ce mutum ta farko daga cikin iyalansa da za ta bi shi, sai na yi dariya.’”

Bayanin Hadisin

A’isha ’yar Ɗalha, wadda take daga cikin fitattun matan Kuraishawa, ta ruwaito daga matar Manzon Allah (S), wato A’isha ’yar Abubakar, cewa ta ce: “Ban taɓa ganin wani mutum da ya yi kama da Manzon Allah (S) wajen magana da zance kamar Fatima ba.”

Wannan ruwaya tana magana ne kan kamanceceniya wajen magana da zance. Akwai kuma wata ruwaya da na taɓa gani, ita ma daga A’isha, wadda ta yi bayani cewa Sayyida Fatima (SA) ita ce mafi kama da Manzon Allah (S) wajen tafiya, kallo da sauran irin waɗannan halaye.

کانَت اِذا دَخَلَت عَلَیهِ رَحَّبَ بِها

Wato, idan Sayyida Fatima (SA) ta shiga gidan Manzon Allah (S), sai ya yi maraba da ita, ya nuna mata farin ciki da girmamawa.

وَ قَبَّل یَدَیها

Manzon Allah (S) ya kasance yana sumbatar hannayen Fatima Zahra (SA).

وَ اَجلَسَها فی مَجلِسِه

Sannan ya zaunar da ita a wurin zamansa.

Wannan yana nuna irin girma da darajar da Manzon Allah (S) yake ba wannan ’yar tasa, wadda take daga cikin manyan matan da suka taɓa rayuwa a tarihin bil’adama.

فَاِذا دَخَلَ عَلَیها قامَت اِلَیهِ فَرَحَّبَت بِهِ وَ قَبَّلَت یَدَیه

Idan Manzon Allah (S) ya shiga gidanta, ita ma sai ta tashi ta tarye shi, ta yi masa maraba, sannan ta sumbaci hannayensa.

وَ دَخَلَت عَلَیهِ فی مَرَضِه

A lokacin da Manzon Allah (S) yake fama da rashin lafiya, wato a lokacin rashin lafiyarsa ta ƙarshe, Fatima (SA) ta shiga wurinsa.

فَسارَّها فَبَکَت

Sai Manzon Allah (S) ya yi mata magana a hankali, a ɓoye, kusa da kunnenta. Sai Fatima (SA) ta yi kuka.

ثُمَّ سارَّها فَضَحِکَت

Daga nan sai ya sake yi mata magana a ɓoye, sai Fatima (SA) ta yi murmushi kuma ta yi dariya.

Sai A’isha ta ce:

فَقُلتُ کُنتُ اَریٰ لِهٰذِهِ فَضلاً عَلَی النِّساء فَاِذا هِیَ امرَأَةٌ مِنَ النِّساء فَبَینَما هِیَ تَبکیٰ اِذ ضَحِکَت

“Sai na yi tunani a raina cewa me ya sa haka yake faruwa? Ni dai na kasance ina ganin wannan baiwar Allah tana da fifiko a kan sauran mata. Amma yanzu sai na ga cewa ita ma mace ce kamar sauran mata; domin sau ɗaya tana kuka, sannan kuma ga ta tana dariya.”

فَسَأَلتُها فَقالَت اِنّی اِذَن لَبَذِرَة

Sai na je na tambaye ta abin da ya faru. Sai ta ce: “Ba zan iya gaya miki ba; domin idan na gaya miki, zan zama mai tona asiri.”

Ma’ana, Sayyida Fatima (SA) ba ta bayyana wa A’isha abin da Manzon Allah (S) ya faɗa mata ba, saboda amana da kiyaye sirrin mahaifinta.

فَلَمّا تُوَفِّیَ رَسولُ اللهِ (صَلَّی اللهُ عَلَیهِ وَ آلِه) سَأَلتُها

Bayan Manzon Allah (S) ya yi wafati, sai na sake tambayar ta.

A wannan lokacin abin da ya hana ta bayyana sirrin ya riga ya gushe, domin Manzon Allah (S) ya riga ya koma ga Allah, saboda haka ba ta ganin wani abu da zai hana ta bayyana abin da aka faɗa mata.

فَقالَت اِنَّهُ اَخبَرَنی اَنَّهُ یَموتُ فَبَکَیتُ

Sai ta ce: “Manzon Allah (S) ya sanar da ni cewa zai rasu. Wannan ne ya sa na yi kuka.”

ثُمَّ اَخبَرَنی اَنّی اَوَّلُ اَهلِهِ لُحوقاً بِهِ فَضَحِکتُ

“Daga nan kuma ya sanar da ni cewa ni ce farkon wanda daga cikin iyalansa zai bi shi, ya shiga tare da shi. Wannan ne ya sa na yi farin ciki har na yi dariya.”

Ƙarshen Bayani

Wannan hadisi yana nuna irin kusanci, soyayya, girmamawa da amana da ke tsakanin Manzon Allah (S) da ’yarsa Sayyida Fatima Zahra (SA). Haka kuma yana bayyana irin matsayinta na musamman a wurin Manzon Allah (S), har ya kasance yana nuna mata girmamawa a fili, yana maraba da ita, yana sumbatar hannunta kuma yana zaunar da ita a wurin zamansa.

Manazarta:

1. Amali, Tusi, Majlisi na 14, shafi na 400.

2. A’isha ’yar Abubakar.

3. Ana nufin kwanakin shahadar Sayyida Fatima Zahra (Salamullahi Alaiha).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha