Lahadi 16 Agusta 2026 - 23:05
Ci Gaba da Tsaurara Danniya a Bahrain; An Kama ’Yan Shi’a Saboda Gudanar da Makokin Imam Rida (AS)

Hauza/ Jami’an tsaron Bahrain sun kama ’yan Shi’a da dama a cikin makonnin da suka gabata, ciki har da wasu malamai, madihai da masu gabatar da jawabai, saboda gudanar da tarukan addini da zaman makokin Imam Rida (AS).

A cewar Sashen Fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, jami’an tsaron Bahrain sun ci gaba da kama ’yan Shi’ar ƙasar da dama a cikin makonnin da suka gabata. Daga cikin waɗanda aka kama akwai wasu malamai, masu waƙoƙin addini da masu wa’azi, sakamakon gudanar da tarukan addini.

Majiyoyin jama'a sun bayyana cewa an kama mai gabatar da wa’azin Imam Husaini kuma malamin makarantar Hauza, Sheikh Ja’afar al-Sitri al-Amjadi, bayan an kira shi domin yi masa tambayoyin tsaro. An shirya zai gurfana a gaban ofishin masu gabatar da ƙara a ranar Talata,11 ga Agusta 2026.

Kame-kamen sun ci gaba ta hanyar kiran mutane zuwa ofisoshin tsaro domin yi musu tambayoyi, inda waɗanda abin ya shafa suka haɗa da: Saeed Akbar al-Mulla, Ali al-Qassab, Ali Saeed, Hussain al-Arab, Hussain Abdulilah, Muhammad Amin, Sayyid Hashim Ibrahim, Hamza Saeed Zuhair, Ahmad Yasin Zuhair, Sayyid Abbas Sayyid Tahir da Rida Hussam.

Majiyoyin sun ƙara da cewa, bayan kiran mutane domin yi musu tambayoyin tsaro, hukumomi sun kama wasu ’yan ƙasa daga garin Samahij saboda halartar taron makoki a daren shahadar Imam Ali bn Musa ar-Rida (AS). Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdullah Sabt, Abbas Abdullah, Hussain Shamsan da Ali Makki.

Haka kuma, an kama ɗan ƙasa Sayyid Ali Sayyid Mazin yayin da yake wucewa ta mashigar King Fahd Causeway, sannan aka kama Hassan Yusuf al-Asfour yayin da yake tafiya ta Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Bahrain.

A wannan lokaci, hukumomi sun kuma kai hari kan wasu daga cikin masu kula da Hussainiyyoyi. Daga cikinsu akwai kama ’yan ƙasa biyu, Muhammad Hassan Jasim al-Nakkal da Sayyid Abdullah Hashim al-Khurjani, daga Ƙungiyar Sitra al-Kharija, da kuma Ahmad Abdulnabi Zayir, wanda yake daga cikin masu kula da Hussainiyyar Ansar al-Adala a garin Diraz.

Wasu jami’an tsaro da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Bahrain sun kuma kai samame a wasu yankuna, lamarin da ya haifar da kama ’yan ƙasa da suka haɗa da Yunus Ahmad Hammad, Abdullah Fadil al-Daqqaq, Hassan Abdulamir da Isa Abbas.

A lokaci guda, kame-kamen da aka yi ta hanyar kiran mutane domin yi musu tambayoyin tsaro sun shafi Hassan Ali al-Tajir, Muhammad Abdulwahab Habib, Sayyid Salih Nizar al-Alawi, Yusuf Muhsin al-Mughni, Zuhair Ja’afar Abu Ruwais, Hussain Abdullah Juma’a, Nasrullah Mansur (matashi) da Ja’afar al-Zaki.

Kame-kamen ’Yan Shi’a a Bahrain

Jami’an tsaron Bahrain sun kama ɗaruruwan ’yan ƙasar tun bayan fara hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, ciki har da mata, yara da malaman addini.

Rahoton ya bayyana cewa an yi amfani da munanan hanyoyin azabtarwa da matsin lamba kan waɗanda aka kama. Rahoton ya ce sabon misali shi ne rasuwar ɗan Shi’ar ƙasar Sayyid Muhammad Muhsin al-Musawi saboda azabtarwa.

Wannan lamari ya faru ne bayan wasu hare-haren tunzura rikicin ƙungiyoyin addini a kafafen sada zumunta, da kuma kiraye-kirayen ƙasar da wasu suka yi na a zartar da hukuncin kisa bisa matsayinsu na siyasa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha