Laraba 11 Nuwamba 2026 - 22:05
Cibiyar Imam Khumaini (RA) Ta Wallafa Littattafai Fiye da 2,000, Tana Kuma Yaɗa Ilimin Zamantakewa Bisa Koyarwar Musulunci a Duniya

Hauza/ Shugaban Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (RA), Ayatullah Mahmud Rajabi, ya bayyana cewa cibiyar ta wallafa littattafai fiye da 2,000, tare da gudanar da ayyukan bincike da yaɗa ilimin zamantakewa bisa koyarwar Musulunci a matakin ƙasa da ƙasa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Rajabi ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da Ministan Ilimi, Bincike da Fasaha na Iran, inda ya gabatar da rahoto kan ayyukan ilimi, bincike da al’adu da cibiyar ke gudanarwa.

Ya ce ilimin zamantakewa bisa koyarwar Musulunci yana taka muhimmiyar rawa wajen gina al’adu, samar da kyakkyawar fahimtar kai da kuma tsara tafarkin ci gaban al’umma. Saboda haka, cibiyar ta mayar da hankali wajen horar da malamai da masu bincike da kuma samar da sabbin ra’ayoyi da ilimi bisa koyarwar Musulunci.

Ya kuma bayyana cewa an fassara wasu daga cikin fitattun ayyukan marigayi Allama Misbah Yazdi (RA) zuwa harsuna 14 na duniya. Ya zuwa yanzu, an wallafa juzu’ai 84 na zaɓaɓɓun ayyukansa. Haka kuma, an samar da littattafan sauti kusan 40, tare da ɗora karatuttukan darussa 1,400 a intanet da kuma wallafa amsoshinsa ga tambayoyi 15,000 da aka yi masa.

Ayatullah Rajabi ya ƙara da cewa an wallafa shirin koyar da Ɗarhe Wilayat, wanda ya ƙunshi muhimman koyarwar Musulunci, a cikin littattafai daban-daban domin ɗaliban jami’o’i, malamai, ɗaliban Hauza da yara. An kuma fassara shi zuwa harsuna biyar na duniya, inda mutane fiye da 100,000 daga sassa daban-daban na al’umma suka amfana da koyarwar shirin.

Dangane da ayyukan ƙasa da ƙasa, ya bayyana cewa waɗanda suka kammala karatu a cibiyar suna koyarwa da gudanar da ayyukan bincike da wa’azi a jami’o’in ƙasashen waje. Haka kuma, cibiyar ta gudanar da tura malamai da masu koyarwa zuwa jami’o’i da cibiyoyi daban-daban kusan sau 15,000.

Shugaban cibiyar ya kuma bayyana cewa ɗakin karatunta da ke birnin Qum yana da littattafai 256,000 a harsunan Farisanci, Larabci da Turanci, tare da takardun bincike da kammala karatu guda 2,800. Ya ƙara da cewa cibiyar tana da shirye-shiryen kafa shafukan intanet guda 69 da manhajoji 85, tare da amfani da fasahar basirar ɗan’adam wajen gudanar da bincike.

A nasa ɓangaren, Ministan Ilimi, Bincike da Fasaha na Iran, Dakta Husain Simayi Sarraf, ya yaba da matsayin ilimi na marigayi Allama Misbah Yazdi (RA), tare da jaddada muhimmancin ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa tsakanin makarantun ilimin addini (Hauza) da jami’o’i.

Ya kuma bayyana cewa an kafa sabuwar majalisar kula da ilimin zamantakewa a ma’aikatar, inda ya buƙaci Cibiyar Imam Khumaini (RA) ta taka muhimmiyar rawa a cikinta. Ya ce hakan zai taimaka wajen faɗaɗa haɗin gwiwar bincike da ilimi, da kuma sanar da matasa da al’ummar duniya game da tunani da koyarwar Musulunci.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha