Lahadi 19 Yuli 2026 - 13:26
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Nuna Godiyarsa Ga Al'ummar Iraki Kan Gagarumar Jana'izar Imam Shahid 

Hauza / Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fitar da saƙo inda ya nuna godiyarsa ga al'ummar Iraki bisa gagarumar jana'izar Imam Mujahidi Shahidi.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wani saƙo, ya girmama manyan Maraji'ai, fitattun malamai, shugabannin ƙabilu, matasa masu kishin addini da kuma daukacin al'ummar Iraki saboda rawar da suka taka wajen ƙirƙirar gagarumar jana'izar Shahidin jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Haramai Masu Tsarki. Ya bayyana wannan jana'iza ta miliyoyin jama'a, wadda ba ta da tamka, mai ɗauke da tutar gwagwarmaya, a matsayin cikakkiyar alamar haɗin kai, 'yan'uwantaka da jituwa tsakanin al'ummomin Iraki da Iran. Ya kuma jaddada cewa: Halartar miliyoyin jama'a a Iran da kuma Iraki domin jana'iza da rakiyar Imam Mujahidi Shahidi (Allah Ya ɗaukaka matsayinsa), ta buɗe sabon babi na farkawa da taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsare-tsaren da azzaluman masu girman kai suka tsara tun farko.

Ga fassarar cikakken saƙon na Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Zuƙatanmu suna miƙa gaisuwa, girmamawa da godiya mai yawa ga manyan Maraji'ai, malamai masu daraja, malamai da furofesoshi na cibiyoyin ilimin addini da jami'o'i, masana da fitattun masu tunani, shugabanni da manyan ƙabilu, shugabannin kabilu da al'ummomi, da kuma al'umma masu karamci, ƙauna, da matasa masu kishin addini da mutunci na ƙasar Iraki da ake zalunta.

Al'ummar Iraki masu imani, waɗanda Allah Ya musu ni'ima da kasancewa maƙwabta kuma masu masaukin Ahlulbaiti (SAWA) a Haramai Masu Tsarki, tare da kyakkyawan tarihinsu na al'adu, da cin moriyar hasken jagoranci daga tsohuwar Hauzar Najaf mai albarka, da kuma irin gwagwarmayar da suka yi a fagen gwagwarmayar adawa, sun ƙirƙiri babbar gagarumin al'amari mai cike da ma'ana da baƙin ciki da raɗaɗi wajen tarbar babban jagora shahidi (Allah Ya ɗaukaka matsayinsa), kamar yadda al'ummar Iran suka yi.

Iraki, tun daga ranar da ƙafafun Maulanmu Amirul Muminina (A.S) suka taka ƙasarta, ta zama ƙasa mai albarka. Ba da daɗewa ba mutanenta suka sanya abin wuya na soyayya da wilayar wannan Imami da zuriyarsa tsarkaka (A.S) cikin cikakken alfahari. Zamanin mulkin azzalumai da sarakuna masu zalunci bai taɓa iya cire lu'ulu'in wilaya da ƙaunar Ahlulbaiti daga zukatan wannan al'umma ba. Saboda haka ne bayan rugujewar gwamnatin Ba'ath aka ga babbar tafiyar Arba'in, wadda saboda ta fito daga zurfin zukatan al'umma masu imani, take ci gaba da faɗaɗa kowace rana. Kuma saboda wannan ne, lokacin da mutanen nan suka ga ɗan Amirul Muminina da Sayyidush Shuhada mazalumi kuma shahidi (A.S), bayan shekaru masu yawa na rabuwa a zahiri da Haramai Masu Tsarki, wannan karon yana zagaya haramai da wani jiki mai kama da na Husaini da mahaifiyarsa da ɗan'uwansa, suka tarbe shi da dukkan zuciyoyinsu tare da girmama zuwansa.

A wani ɓangaren kuma, wannan jana'iza ta miliyoyin jama'a, wadda ba ta da tamka, ta jagoran tutar gwagwarmaya, ta nuna cikakkiyar alamar haɗin kai, 'yan'uwantaka da jituwa tsakanin al'ummomin Iraki da Iran. Babu shakka shugabannin girman kai na duniya sun kalli hotunan wannan gagarumin taro a Iraki da zukata masu cike da tsoro, kuma sun ga yadda manyan kuɗaɗen da suka kashe domin lalata dangantakar al'ummomin biyu suka zama a banza kuma ba su yi wani tasiri ba. Wannan halartar ta miliyoyin jama'a a Iran da kuma Iraki domin jana'iza da rakiyar Imam Mujahidi Shahidi (Allah Ya ɗaukaka matsayinsa), ta buɗe sabon babi na farkawa da taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsare-tsaren da azzaluman masu girman kai suka ƙirƙira tun farko. Yanzu Babban Shaidan, wato Amurka mai aikata laifuffuka, ta fahimci cewa ci gaba da kasancewarta cikin sauƙi tana mulkin wannan yanki mafarki ne marar tushe.

Ba da daɗewa ba, ƙirjin al'umma mai karamci ta Iraki, da ƙabilu da al'ummomi masu jinin ƙauna, za su sake buɗewa domin maraba da masu ziyartar Arba'in, ciki har da tarin waɗanda za su yi ziyarar a madadin Shahidin Iran. Wannan zai haɗu da tunanin wannan gagarumar jana'iza da kuma wannan babban mutum wanda watakila ya shafe shekaru yana fatan samun damar ziyartar Haramai Masu Tsarki. Hakan zai bayyana wa duniya gaskiyar taken nan mai cike da ma'ana cewa: "Hubbul Husain Yajma'una" (Ƙaunar Husaini ta haɗa mu).

Kuma in sha Allah, addu'ar Maigidanmu (Allah Ya gaggauta bayyanarsa mai albarka) za ta kasance sanadin tsaro, albarka da ci gaban al'ummar Iraki, da falalarsa da karamcinsa.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i 

2 Safarul Muzaffar 1448

26 Tir 1405 (17 Yuli 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha