A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da taron tunawa da babban jagoran juyin juya hali, Hazrat Imam Khumaini (R.A) a da yammacin ranar Laraba, tare da halartar jami'ai daga lungu da sako na mutane a harami mai tsarki na Hazrat Fatima Ma'asuma (S.A), ƙarƙashin kulawar ofishin Jagoran Juyin Juya Hali.
A yayin wannan taro, Ayatullah Muhsin Araki ya yi nuni da abun da ya faru a Ghadir Khum, inda ya bayyana cewa sako mai girma na Ghadir ba kawai labari ne na tarihi ba; a'a, a cikin wadannan gajerun kalmomi na Manzon Allah (S.A.W.W) da yake cewa: *"Duk wanda na kasance shugabansa, to wannan Ali shugabansa ne..."*, an bayyana wani babban bangare na gaskiyar addini, asalin al'ummar musulmi, da kuma makomar 'yan adam.
Bayyanannen Asalin Al'ummar Musulmi a Makarantar Ahlul Bait (A.S)
Mamban majalisar malaman Hauzar Qom ya kara da cewa: "A hangen makarantar Ahlul Bait (A.S), al'ummar musulmi tana da asali bayyananne kuma ƙaddararre, kuma tafiyar tarihin dan adam tana tafiya ne zuwa ga tabbatar da al'ummar da ta ginu a kan adalci, bautar Allah, da kuma shugabancin mutanen ƙwarai."
Ya ci gaba da cewa, a mahangar tunanin Shi'a, farko, tsakiya, da ƙarshen tafiyar al'umma da kuma rawar da shugabanni na Allah ke takawa suna da bayani filla-filla da ke da jituwa, kuma wannan fahimta tana ɗaya daga cikin mafi muhimmancin jarin ilimi na makarantar Shi'anci."
Koyarwa irin su "Ali yana tare da gaskiya, gaskiya kuma tana tare da Ali" da kuma alaƙa ta jini da ba ta rabuwa tsakanin Alkur'ani da Wilayah, suna cikin zurfafan koyarwar Musulunci da ke tsara rayuwar mutum ɗaya da ta zamantakewa ta musulmi.
Yabon Juriyar Al'ummar Iran a Gaban Girman Kan Duniya
Ayatullah Araki ya yaba da tsayin dakan al'ummar Iran a gaban barazanar ƙasashen duniya, inda ya ce: "Gwagwarmayar al'ummar Iran a gaban matsin lamba da barazanar manyan ƙasashen duniya abin yabo ne. A yau da yawa daga cikin mutanen duniya suna tambayar cewa wane abu ne ya sanya al'ummar Iran tsayuwa a gaban manyan ƙasashen girman kai na duniya, kuma ta kiyaye haɗin kai da sabatinta ko da a cikin mafi tsananin yanayi?"
Shahadar Shugabanni Tana Kara Haɗin Kan Kasa da Fadada Al'adar Gwagwarmaya
Mamban majalisar tantance maslahar tsarin mulki ya bayyana cewa: "Al'ummar Iran a lokuta daban-daban na tarihi ta nuna cewa shahadar shugabanni, fitattu, da manyan mutane ba wai kawai ba ta kawo rauni ko rushewar nufin kasa ba ne, a'a, tana zama silar karfafa gwiwar tsayuwa, danƙon zumuncin al'umma, da kara karsashin ƙasa a gaban barazana da ƙalubale."
Ya bayyana cewa wannan siffa ta samo asali ne daga al'adar Wilaya da koyarwar makarantar Ashura. Tarihin Musulunci yana dauke da bayyanannun misalai na wannan gaskiya, wanda mafi fice a ciki shi ne yunƙurin Hazrat Sayyidush Shuhada (A.S) wanda duk da dukkan tsanani, masifu, da matsin lamba da aka yi wa gidan Manzon Allah (S.A.W.W) da sahabbansa, bai tsaya ba, sai ma ya kai ga kafawa da faɗaɗar wani yunkuri mai ɗorewa kuma mai tasiri a tarihin Musulunci."
Tsayuwar Tarihi Ta Al'ummar Shi'a a Gaban Zalunci
Mamban hukumar shugabancin majalisar kwararru (Khobregan) ya yi nuni da asalin tarihin Shi'anci, inda ya ce: "Al'ummar Shi'a a tsawon ɗaruruwan shekaru ta tsaya a gaban kowane nau'in matsin lamba, zalunci, da gwamnatocin kama-karya. Wannan juriya ta tarihi ba ta takaitu ga wannan zamani kaɗai ba; tana da tushe a cikin zurfafan aƙidoji na addini da al'adu na 'yan Shi'a. Wannan gado mai daraja an kiyaye shi ne tun daga zamanin Amirul Muminina Hazrat Ali (A.S), sannan bayan sa Imam Hasan Al-Mujtaba (A.S) ya taka rawar gani wajen kare shi. Sai dai kuma, abun da ya faru a Ashura da juyin juya halin Imam Husain (A.S) ya zama gaɓar canji a tarihin Musulunci da Shi'anci, wanda ya sanya wannan tunani da aƙida ya koma zuwa ga al'umma mai faɗi, mai karsashi, mai juriya da tasiri a fagen tarihi."
Ayatollah Araki ya jaddada buƙatar gudanar da bincike na ilimi kan dalilan ɗorewar al'ummar Shi'a, inda ya bayyana cewa sirrin iko da ɗorewar Shi'a yana cikin dankon alaka mai zurfi da tushen Wilaya, wanda Manzon Allah (S.A.W.W) ya zana a Ghadir Khum.
Imam Khumaini Ya Rayar da Alaƙar Al'umma Da Wilaya da Al'adar Intizar
Ayatullah Araki ya bayyana rawar da Imam Khomeini ya taka wajen rayar da karfin Wilayh da na zamantakewa, inda ya ce: "Imam Khumaini ya sami damar mayar da alakar al'umma da Wilaya da al'adar Intizar (jiran bayyanar Imam Mahdi) daga wani ƙarfi ɓoyayye zuwa ga zama wani babban ƙarfi na zamantakewa mai tasiri a aikace. Wannan alaƙa ta samar da fagen da koyarwar addini da ta Wilaya za su taka rawa a aikace a cikin rayuwar zamantakewa da ta siyasar mutane."
Ya jaddada cewa wannan tafarki ya ci gaba da ɗorewa har bayan rasuwar Imam Khumaini karkashin shiriya ta Shahidin jagoran juyin juya hali, wanda hakan ya zurfafa alaƙar al'umma da dabi'u na Ubangiji da koyarwar Wilaya. Sabati da juriyar al'umma a gaban matsin lamba da barazana na ciki da na waje, sun ginu ne a kan wannan danƙon alaƙa mai karfi da kuma shiriyar Wilaya.
Juyin Juya Halin Musulunci; Gaɓar Farfaɗo Da Mutuncin Ƙasa
Mamban majalisar tantance maslahar tsarin mulki ya yi nuni da lokacin kafin samun nasarar juyin juya halin Musulunci, inda ya ce: "Al'ummar Iran kafin juyin juya hali tana da asali mai girma da na wayewar kai, amma a lokuta daban-daban na tarihi ta fuskanci ƙanƙanci, mika wuya ga ƙasashen waje, da kuma asarar ɓangarori na karfin ƙasa. Wannan lokaci ya haifar da buƙatar al'umma ta neman farfaɗo da mutunci, dogaro da kai, da kuma 'yancin ƙasa."
Juyin Juya Halin Musulunci ya sami damar samar da fagen dawo da mutuncin ƙasa, dogaro da kai, bunkasar ilimi, da kuma 'yancin ƙasar. A yau, al'ummar Iran tana tafiya ne a kan tafarkin kare mutuncinta da 'yancinta ta hanyar yin koyi da al'adar Ashura da rayuwar Ahlul Bait (A.S).
A ƙarshe ya bayyana cewa ana iya ganin wannan ƙarfin ƙasa da sadaukarwa wajen kare tsarin Musulunci a cikin take da fitowar al'umma a tituna wanda yake nuna alamar ɗamfarar al'umma da tsarin na juyin juya halin Musulunci.
Ra'ayinka