A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Ja'afar Morouji Tabasi, a cikin wani rubutu mai taken "Lu'u-lu'un Ilimi a Cikin Huɗubar Ghadir", ya kawo kamar haka:
Goma sha takwas ga watan Zul-Hijjah ita ce ranar da fiyayyen halitta (S.A.W.A) ya naɗa Shugaban Masu Tsoron Allah, Amirul Muminina Ali (A.S) a matsayin jagora. A wannan rana mai cike da kaddara wacce ta shafi makomar al'ummar musulmi, Manzon Allah (S.A.W.A) a cikin tsananin zafin rana da sahara marar ruwa da ciyawa, ya gabatar da bayanai masu matukar muhimmanci game da fifikon Amirul Muminina (A.S).
Zafin ranar ya kai matsayin da marigayi Sheikh Mufid (ya rasu a shekara ta 413 bayan hijira) a cikin littafinsa Al-Irshad (Juz'i na 1, shafi na 175) ya bayyana cewa: "Mafi yawan mutane saboda tsananin zafi sun riƙa nade mayafansu a ƙafafunsu." Sibt ibn al-Jauzi, malami ɗan mazhabar Hanafiyya (ya rasu a shekara ka 685 bayan hijira) a cikin littafinsa Tazkiratul Khawas (shafi na 37) ya ambaci cewa adadin mutanen da suka halarci wajen sun kai dubu 120 (120,000). Haka nan, Ibn Asakir al-Dimashƙi, malami ɗan mazhabar Shafi'iyya (ya rasu a shekara ta 571 bayan hijira) a cikin littafinsa Tarikh Dimashƙ (Juz'i na 45, shafi na 187) yayin da yake siffanta jawabin Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce: "Ya tsaya ya faɗi abin da Allah ya so ya faɗa"; wannan magana tana nuna cewa Annabi bai yi takaitaccen jawabi ba a cikin wannan zafi, a'a, ya bayyana bayanai masu yawa ne ga wannan taron jama'a.
A cikin wannan gajeren rubutu, muna son fito da lu'u-lu'an ilimi da ma'arifa daga wannan huɗuba ta tarihi ta Manzon Allah (S.A.W.A). Marigayi Ibn Jabr a cikin littafinsa Nahjul Iman, ya kawo sassan huɗubar inda kalmar "Ma'ashiran Nas" ta zo kusan sau 70, ga wasu daga cikin sassan kamar haka:
1. Yaku mutane (Ayyuhan Nas): Wannan shi ne waje na karshe da zan tsaya, don haka ku saurara, ku yi biyayya, kuma ku amshi umarnin Ubangijinku; domin Allah shi ne Maulanku (Shugabanku) kuma Ali shi ne Imaminku.
2. Yaku taron mutane (Ma'ashiran Nas): Ku fifita Ali, domin babu wani ilimi face Allah ya ba ni shi, kuma duk abun da aka koya mini, lallai na koya wa Ali; shi ne mutumin da zai bayyana muku ilimi a bayana.
3. Ma'ashiran Nas: Ku fifita Ali domin Allah ne ya fifita shi, kuma ku amshe shi (a matsayin jagora) domin Allah ne ya naɗa shi.
4. Ma'ashiran Nas: Ali limami ne (Imam) daga bangaren Allah.
5. Ma'ashiran Nas: Ku fifita Ali domin shi ne mafi alherin mutane a bayana a cikin maza da mata.
6. Ma'ashiran Nas: Lallai Ali da tsarkakan mutane daga cikin 'ya'yana duka suna daga tsatson Ali; su ne nauyi mafi kankanta (Thaqalul Asghar) kuma Alƙur'ani shi ne nauyi mafi girma (Thaqalul Akbar). Wannan jawabi yana nuni ne ga ingantaccen hadisin nan na Thaqalain wanda ya zo a cikin manyan littattafan Ahlus Sunnah.
7. Ku sani kuma ku fahimta cewa lallai na cika aikina, kuma na isar da sakon da ya zama dole in isar muku, na kuma jiyar da kunnuwanku kuma na bayyana muku. Ku sani... ku sani cewa babu wani wanin ɗan'uwana wannan (Ali) da yake Amirul Muminina (Shugaban muminai), kuma yin mulki a kan mutane a bayana bai halatta ga kowa ba face Ali.
8. Ma'ashiran Nas: Wannan Ali ɗan'uwana ne kuma magajina a kan duk wanda ya yi imani da ni, kuma Ali shi ne mai fassara littafin Ubangiji.
9. Ma'ashiran Nas: Lallai Allah ya cika muku addininku ta hanyar shugabancin (Imamancin) Ali. Wannan yana nuni ne ga ayar nan ta Alƙur'ani da ke cewa: "A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni'amata..."
10. Ma'ashiran Nas: Shi (Ali) yana sauke nauyin addinin Allah, yana kare Manzon Allah, kuma shi tsarkakakken mutum ne, mai shiryarwa kuma shiryatacce; Annabinsa shi ne mafi alherin Annabawa, shi kuma shi ne mafi alherin wasiyyi.
11. Ma'ashiran Nas: Zuriyar kowane Annabi tana gaba ne daga tsatson sa, amma tawa zuriyar tana daga tsatson Amirul Muminina Ali bin Abi Talib.
12. Ma'ashiran Nas: Wani haske na Ubangiji yana cikina, sannan yana cikin Ali, sannan yana cikin zuriya tasa har zuwa bayyanar Al-Mahdi wanda zai karbo hakkin Allah da hakkinmu.
13. Ma'ashiran Nas: Ni ne hanyar Allah madaidaciya (Siraɗal Mustaƙim) wacce Allah ya umarce ku da ku bi ta, kuma a bayana Ali ne, sannan bayan Ali, Imaman shiriya daga tsatsonsa za su shiryar da ku zuwa ga gaskiya da adalci.
14. Ma'ashiran Nas: Lallai ni mai gargadi ne, Ali kuma mai bushara ne. Ni mai gargadi ne, Ali kuma mai shiryarwa ne. Ni Annabi ne, Ali kuma wasiyyina ne.
15. Ma'ashiran Nas: Ni Manzon Allah ne, Ali kuma Imami ne, kuma Imamai a bayansa 'ya'yansa ne... kuma Al-Mahdi (Mai jiran gado) wanda zai yi nasara a kan dukkan addinai yana daga cikinmu. Lallai shi ne mai daukar fansa a kan azzalumai, mai bude katangun yaki kuma mai ruguza su... Shi ne hujjar Allah mai wanzuwa, babu wata hujja a bayansa, kuma gaskiya ba ta rabuwa da shi... Ku sani shi ne waliyyin Allah a bayan kasa.
16. Ma'ashiran Nas: Alƙur'ani yana cikinku, kuma Ali da Imamai a bayansa za su kasance cikinku... matukar dai kuna riko da su, ba za ku taba bata ba.
17. Ma'ashiran Nas: Falalolin Amirul Muminina Ali bin Abi Talib suna wajen Allah, kuma Allah ya saukar da su a cikin Alƙur'ani; adadinsu ya yi yawa da ba za a iya kididdige su a zama guda ba.
18. Ma'ashiran Nas: Duk wanda ya yi biyayya ga Allah da Manzonsa da kuma Ali da sauran Imamai da na ambata, to lallai ya rabauta da babban rabo.
Lu'u-lu'an Ma'arifa (Gudunmawar Ilimi)
A cikin wadannan sassa 18 na huɗubar Ghadir, za a iya fito da manyan rukunai kamar haka:
- Nuni ga Wilaya, Imamanci, da kuma halifancin Ali (A.S).
- Nuni ga fifiko da ilimin Amirul Muminina (A.S) a kan daukacin wadanda suka halarci wajen.
- Duk wani ilimi da Allah ya koya wa Annabi, ya mika shi ga Amirul Muminina.
- 'Ya'ya da zuriyar Manzon Allah (S.A.W.A) suna asali ne daga tsatson Ali (A.S).
- Nuni ga ingantaccen hadisin nan na Thaqalain.
- Kafa hujja da Annabi ya yi wa daukacin mutane.
- Cikar addinin Allah ta hanyar wilaya da Imamancin Ali (A.S).
- Nuni ga Imamancin Imam Zaman (A.S) da muhimmiyar magana kan Mahdawiyya.
- Imam Zaman shi ne mai taimakon addinin Allah, magajin dukkan ilimi, kuma waliyyin Allah a bayan kasa.
- Tsira da rabo na 'yan adam yana boye ne a cikin biyayya ga Ali (A.S).
Mutanen Farko Da Suka Yi Wa Ali (A.S) Mubaya'a
Marigayi Ibn Jabr bayan kammala kawo kalaman Manzon Allah (S.A.W.A) da huɗubar Ghadir, ya ce: "Mutanen farko da suka damƙi hannun Manzon Allah (S.A.W.A) suka kuma taya Ali (A.S) murna sune: Abubakar, Umar, Usman, Dalha, Zubair, da sauran sahabai na Muhajirun da Ansar."
Tambayar da ke zuwa a zukatan mutane a yau ita ce: Shin wadanda suka yi wannan mubaya'a sun tsaya a kanta ko kuwa sun karya ta?
Hafiz al-Zahabi (ya rasu a shekara ta 748 bayan hijira) a cikin littafinsa Siyar A'alam al-Nubala (Juz'i na 19, shafi na 328) ya fito da magana daga littafin Al-Ghazali mai suna Sirr al-Alamin inda ya kawo cewa Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce a ranar Ghadir: "Wanda na kasance shugabansa (Maulansa), to Ali shugabansa ne." Sai Umar ya ce wa Ali: "Bakhin, bakhin (madalla, madalla) gareka ya Ali, ka wayi gari shugabana kuma shugaban kowane mai imani namiji da mace."
Zahabi ya ci gaba da cewa: Al-Ghazali ya bayyana cewa wannan kalami na Umar yana nuna yarda da mika wuya ne ga wilayar Ali; sai dai son mulki, sarauta, da neman shugabanci ya sanya son zuciya ya yi tasiri a kansu, har ta kai ga sun juyo da baya ga gaskiya, suka sayi duniya da ainihin gaskiya a kan farashi kalilan, kuma lallai sun yi mummunan fatauci. A bayyane yake cewa wannan kalami na Al-Ghazali (ya rasu a shekara ta 505 bayan hijira) nassi ne da ke nuna karya waccan mubaya'a.
Ra'ayinka