A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an buga sabon fitowar mujallar "Payam" da nufin bayyana tunanin Alƙur'ani na Shahidin Jagora, da kuma sanar da malamai, masana da manyan mutanen wannan ƙasa game da ra'ayoyinsa, tare da haɗin gwiwar gidan al'adun Iran.
Tunanin Alƙur'ani na Shahidin Jagora yana tasiri a cibiyoyin ilimi na Pakistan
Wannan fitowa ta musamman, wacce aka ɗauka a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa dangantakar tunani da addini tsakanin kasashen makwabta Iran da Pakistan, Cibiyar Al'adu da Bincike ta "Al-Basirah" ta Pakistan ce ta buga kuma aka rarrabawa masana.
Ginin tunanin Alƙur'ani na Shahidin Jagora Imam Khamene'i yana dogara ne akan hangen nesa mai ƙarfi, mai warware matsaloli kuma mai amfani ga Littafin Allah; hangen nesa wanda yake ɗaukan Alƙur'ani mai girma ba kawai littafin ibada na mutum ba, har ma da magani mai warkarwa da shiri cikakke don tsara al'ummar zamani, kafa adalci, da samun 'yanci ga al'ummar Musulunci.
A cikin wannan makarantar tunani, yin tadabbur akai-akai a cikin ayoyin Allah shine mabuɗin farkawa ta Musulunci, muƙawama ga tsarin mulkin mallaka na duniya, da ƙarfafa haɗin kai da 'yan uwantaka tsakanin mazhabobin Musulunci daban-daban; makarantar da take ƙoƙarin fitar da sababbin amsoshi daga cikin wahayi da kuma ba da mafita a aikace ga ƙalubalen siyasa, zamantakewa da tunani na duniyar Musulunci.
A cikin wannan fitowa ta musamman, manyan marubuta, masu fassara da masu bincike sun yi ƙoƙari su keɓanta fannoni daban-daban na zurfin kallon Alƙur'ani na Shahidin Jagora Ayatullah al-Uzma Khamene'i a cikin rubuce-rubuce masu inganci, masu sauki kuma masu dacewa da bukatun tunani na yankin, domin malaman jami'o'i da ma'abota ilimi na Pakistan su sami zurfin fahimta game da manufofi da tushen tunanin Musulunci.
Ra'ayinka