A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, jerin darussan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al'umma Mai Manufa”, ana gabatar da su ne domin yaɗa koyarwa da ma’arifar da ta shafi Imamuz Zaman (AJ) ga ku masoya masu daraja.
Bayan duniya ta shafe wani dogon lokaci karkashin mulkin zalunci da danniya, duniya – da bayyana (zuhur) na ƙarshen hujjar Ubangiji – za ta juya zuwa mulkin salihan mutane; mulki zai koma hannun shugabanni nagari da mutane na ƙwarai, kuma wannan alkawari ne tabbatacce daga Allah.
Wannan mulkin nagartattu wanda zai fara ne da shugabancin Imam Mahdi (AS), zai ci gaba har zuwa ƙarshen duniya, kuma lokacin zalunci da azzalumai ba zai sake dawowa ba.
Ubangiji Maɗaukaki yana yi wa Annabi Musulunci (sallallahu alaihi wa alihi) bushara da mulkin ƙarshe na jagora ma’asumi, sannan a ƙarshe yana cewa:
«لَأُدِیمَنَّ مُلْکَهُ وَ لَأُدَاوِلَنَّ الْأَیَّامَ بَیْنَ أَوْلِیَائِی إِلَی یَوْمِ الْقِیَامَةِ.»
“(Bayan Mahdi (AS) ya hau mulki) zai tabbatar dawwamammen mulkinsa, kuma zan riƙa juyar da ranaku (da mulkin kasa) a hannun waliyyaina da masoyana har zuwa ranar ƙiyama.” (Kamal ad-Din, j. 1, sh. 256)
Saboda haka, tsarin adalcin da Imam Mahdi (AS) zai kafa, daula ce da bayan ta ba za a samu wata daula ta wani ba, kuma a zahiri sabon tarihi ne na rayuwar ɗan Adam zai fara, wanda gaba ɗayansa zai gudana ne a ƙarƙashin mulkin Allah.
Imam Baƙir (AS) yana cewa:
«دَوْلَتُنَا آخِرُ الدُّوَلِ وَ لَنْ یَبْقَ أَهْلُ بَیْتٍ لَهُمْ دَوْلَةٌ إِلَّا مُلِّکُوا قَبْلَنَا لِئَلَّا یَقُولُوا إِذَا رَأَوْا سِیرَتَنَا إِذَا مُلِّکْنَا سِرْنَا مِثْلَ سِیرَةِ هَؤُلَاءِ»
“Daularmu ita ce ƙarshe daga cikin dukkan dauloli, kuma babu wata daula ta dangin wani gida da zai rage, face kafin mulkinmu su ma sun taɓa mulki, domin kar idan suka ga salon mulkinmu su ce: ‘Da mu ma mun samu mulki, da mun yi kamar yadda waɗannan suka yi.'” (Al-Ghayba, Shaikh Tusi, sh. 473)
Saboda haka, tsawon dorewar tsarin Allah bayan zuhur ya bambanta da tsawon lokacin da mutum ɗaya – Imam Mahdi (AS) da kansa zai zauna yana mulki; domin bisa ruwayoyi, zai yi mulki ne na sauran shekarun rayuwarsa, sannan a ƙarshe zai bar wannan duniya.
Babu shakka cewa tsawon lokacin mulkinsa dole ne ya zama haka da zai ba da damar sauyin duniya baki ɗaya da kafuwar adalci a dukkan yankunan duniya. Amma ko wannan manufa za a iya cimma ta cikin shekaru nawa? Ba abin tsammani da zato ba ne; dole ne a koma ga ruwayoyin Imamai Ma’asumai (AS).
To amma, idan aka yi la’akari da ƙwarewa da ƙarfafa ruhaniya na wannan jagora na Allah, da taufiki da taimakon gaibi da yake tare da shi, da abokan tafiya da sahabbansa nagari, da kuma shirye‑shiryen duniya gaba ɗaya na karɓar mulkin ƙimomi da kyawawa a lokacin zuhur, yana yiwuwa aikinsa na Mahdi al-Maw’ud (AS) ya kammala cikin wani lokaci mai ɗan takaitaccen tsawo.
Ruwayoyin da suka ambaci tsawon lokacin mulkin Imam Mahdi (AJ) sun zo da siffofi daban-daban. Wasu sun ambaci cewa zai yi mulki shekara 5, wasu sun ce shekara 7, wasu kuma 8, 9 ko 10. Wasu ruwayoyin sun ambaci shekara 19 da wasu watanni, wasu shekara 40, har ma wasu sun ambaci shekara 309.
Samun hakikanin adadin tsawon mulkin daga cikin waɗannan ruwayoyin abu ne mai wuya, amma wasu daga cikin malaman Shi’a sun yi la’akari da yawan ruwayoyi da shaharar ruwayoyin shekara 7, suka zaɓi wannan ra’ayi. Wasu kuma, bisa wasu ruwayoyi, suka ce: tsawon mulkin Imam Mahdi (AS) shekara 7 ne, amma kowace shekara daga cikin shekarun mulkinsa ta yi daidai da shekaru 10 daga cikin shekarunmu.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba…
An ɗauko daga littafin “Negine Afarinesh” (Zoben Halitta), tare da ɗan ƙaramin gyara.
Ra'ayinka