A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Dokta Abbasi, shugaban Jami'ar kasa da kasa ta Al-Mustafa (SAWA) ya tura wasikar martani kan takardar da Jami'ar Al-Azhar ta fitar dangane da abin da yake faruwa a yankin gabas ta tsakiya.
Rubutun da zai zo a ƙasa fassarar cikakkiyar wasikar ne:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai
Mai girma Dr. Ahmad Muhammad Ahmad Al‑Tayyib
Babban Limami kuma Sheikh na Jami’ar Al‑Azhar
Assalamu alaikum,
Ina so in bayyana mamakina da kuma baƙin cikina game da bayanin da Majalisar Fatwa ta Al‑Azhar ta fitar a kwanakin baya, a daidai lokacin da Amurka da muguwar kawarta a yankin – wato gwamnatin mamayar sahyoniya – suke kai farmaki na zalunci.
A cikin wannan bayani, an jaddada muhimmancin kiyaye jinin Musulmi da bin dokokin ƙasa da ƙasa, amma kuma an yi Allah‑wadai da duk wani matakin soji da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ɗauka a kan wuraren Amurka da gwamnatin sahyoniya a yankin, tare da bayyana waɗannan hare‑haren a matsayin abin da ke haddasa rashin zaman lafiya a yankin.
Ina so in gabatar da wasu bayanai a wannan lamari:
1. Kai, mai girma, ka san cewa Amurka da Isra’ila a tsakiyar tattaunawa sun kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin watan Ramadan mai alfarma, da nufin rusa da kuma rarraba ƙasar. A wannan harin an kashe babban shugaba kuma jagoran juyin juya halin Musulunci, tare da wasu manyan kwamandojin soji da kuma wasu daga cikin talakawan Iran marasa laifi.
Shin a ganinka da kuma na Majalisar Fatwa ta Al‑Azhar, jama’ar Iran da sojojinta suna da wata hanya daban face yin tsayin daka (muƙawama)? Me ya sa ba ku ga ya dace ku yi Allah‑wadai da wannan farmaki a fili kan ƙasar Musulmi daga sahyoniyawan Yahudawa ba? Shin ba Manzon Allah (SAWA) ya ce ba:
“Duk wanda ya ji Musulmi yana kiran ‘Ya ku Musulmi ku taimake ni’ amma bai amsa ba, to ba Musulmi ba ne.”
A irin wannan hali na gaggawa da mutanen Iran suka shiga, wane uzuri ne wannan shiru yake da shi?
2. A cikin bayanin Majalisar Fatwa ta Al‑Azhar, an yi Allah‑wadai da harin Iran kan sansanonin Amurka a wasu ƙasashen yankin.
Abin mamaki ne! Amurka ta yi amfani da kayan aikinta da ke cikin waɗannan ƙasashe wajen kai hari kan wata ƙasa Musulma, kuma sojojinmu sun mayar da martani ta hanyar kai hari kan waɗannan sansanonin da jiragen Amurka suka tashi daga cikinsu.
Amma abin mamaki, Majalisar Fatwa ta Al‑Azhar ta yi shiru game da harin wanda ya fara kai hari, amma ta yi Allah‑wadai da haƙƙinmu na doka da na ƙasa da ƙasa wajen kare kai da hukunta mai zalunci. Shin Allah Madaukaki bai ce a cikin Alƙur’ani ba:
“Duk wanda ya kai muku hari, ku ma ku kai masa hari da misalin abin da ya kai muku.” (Al‑Baqarah: 194)
Ba ku ganin wannan matsayi mai nuna bambanci zai jefa masu sauraronku cikin ruɗani ba?
3. An ce a cikin bayanin Majalisar Fatwa ta Al‑Azhar an yi Allah‑wadai da harin Iran kan sansanonin Amurka a ƙasashen yankin.
Dr. Al‑Tayyib! Me ya sa Majalisar Fatwa ta jami’arku ba ta yi gargadi ga waɗannan ƙasashen maƙwabta ba cewa bai kamata su ba wa Amurka – wadda take kafira mai yaƙar Musulmi – damar amfani da ƙasarsu wajen kai hari kan wata ƙasa Musulma ba?
Shin Allah Madaukaki bai ce ba:
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Kada ku riƙi Yahudawa da Kiristoci a matsayin majiɓinta...” (Al‑Ma’idah: 51)
Kuma a wata aya:
“Kar muminai su riƙi kafirai a matsayin majiɓinta maimakon muminai...” (Ali‑Imran: 28)
Shin ba da damar amfani da ƙasa da sararin samaniyar ƙasar Musulmi ga kafiri mai yaƙi ba ya nuna karya waɗannan umarnin Allah na Alƙur’ani a fili?
4. Mai girma shugaban Al‑Azhar! Mu yi tunani kaɗan game da makomar duniyar Musulmi da al’ummar Musulmi. Shin Isra’ila da Amurka maƙiyan Iran kaɗai ne? Shin laifin Iran ba shi ne kawai goyon bayan da take bai wa mutanen Gaza wadanda ake zalunta ba?
Ina kira gare ku da gargadi na ɗan uwa cewa yin shiru a kan wannan bala’i zai yi babbar illa ga makomar al’ummar Musulmi.
Dr. Al‑Tayyib! Mu haɗa hannu mu taru a ƙarƙashin tutar Alƙur’ani, mu tsaya kan adalcin Alƙur’ani mu yi magana kuma mu ɗauki mataki a kan mugayen yan sahyoniyawa da sahyoniyanci. Bayan alhakin da za mu fuskanta a ranar alƙiyama game da maganganunmu da shiru na yau, al’ummomin da za su zo nan gaba za su yi hukunci kan abin da muka faɗa da abin da muka aikata a yau.
Wassalamu ala manittaba’al‑huda.
Ali Abbasi
Shugaban Jami’ar Ƙasa da Ƙasa ta Al‑Mustafa
29 ga Ramadan 1447 Hijri.
19 ga Maris 2026
Ra'ayinka