A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a tsawon waɗannan kwanaki, ta gudanar da karatun Alkur'ani Mai Tsarki tare da addu'o'in neman karin taimakon Allah (T) ga rundunar Allah domin yin nasara a kan maƙiya tare da neman samun sa'ada ga ruhin shuhada.
Haka nan kuma an gudanar da jawabai a tsawon kwanakin akan darussan da muminai zasu dauka daga wannan waki'ar, da ma wasu bayanai masu muhimmanci da suka shafi waki'ar wanda Hujjatul Islam wal-Muslimin Abdullahi Ahmad Fudiyya ya gabatar.
A ranar rufewar, Cibiyar ta Albasira Qom Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta gudanar da Muzaharar cika kwana bakwai, wanda ta karade dukkan unguwar ɗalibai ta Shahrek Mahdiye. Masu Muzaharar suna tafe ɗauke da tutar jamhuriyar Musulunci ta Iran, hotunan Shaheed Sayyid Ali Khamenei, Imam Khumaini (Q) da Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) suna rera taken goyon baya ga Jamhuriyyar Musulunci tare da neman daukar fansar jinin shahidai da kuma jaddada alkawarin tabbata a kan tafarkin Shaheed Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei.







Ra'ayinka