Alhamis 11 Disamba 2025 - 20:51
Wajibcin Samar da Sabbin Hanyoyin Tabligin Addini Da Suka Dace da Sauye-sauyen Zamantakewa / Tabligin Addini Yana Buƙatar Fasaha da Kirkire-kirkire.

Hauza/Hujjatul Islam Ahmad Wa'iziy, yayin bayyana matsayi iri-iri na cibiyoyin ilmi (Hauza), ya yi bayani cewa: Cibiyoyin ilimin addini (Hauza) su ne cibiyoyin ilimi, tsarkakewa, koyarwa, bincike da nazari; amma sakamako na asali da aikin ƙarshe na cibiyoyin ilimin addini, shi ne kafawa tare da kaddamar da addini a cikin al'umma da kuma yada sakon Allah.

A cikin rahoton da Ofishin Yada Labaran Hauza ya fitar, Hujjatul Islam Ahmed Wa'iziy, Shugaban Ofishin Tabligin Addinin Musulunci na Cibiyar Ilimin Addini ta Qum a wajen taron rufe bikin "Jannat" wanda aka gudanar a yau a dakin taro na Ghadeer Qum, yana mai nuni ga sakamakon albarkar juyin juya halin Musulunci, ya ce: "Ayyukan jihadi, ƙungiyoyi masu gina al'umma, da ci gaban cibiyoyin ilimin addini, duk sun samo asali ne daga albarkacin kasancewar Imam Khomeini, muna fatan Allah Ya ƙara daga darajarsa da ta shahidai."

Ya kuma kira bikin "Jannat" a matsayin misali na haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da cibiyoyi masu alaƙa da Hauza, kuma ya ce: "Muna fatan wannan tsari zai haifar da ƙarin hulɗa da faɗaɗa tasiri da albarka a nan gaba."

Me Yasa Yada Addini (Tablig) Yake Buƙatar Sabbin Kirkirori?

Shugaban Ofishin Tabligin Addinin Islama a ci gaba da jawabinsa, ya bada amsar wata tambaya mai mahimmanci, ya ce: "A yau dole ne mu ba da amsa don me a cikin wannan aiki mai mahimmanci na yada addini, muke buƙatar sabbin hanyoyi, fasaha, da kirkire-kirkire?."

Hujjatul Islam Ahmad Wa'iziy, da yake bayyana matsayi iri-iri na cibiyoyin ilimi (Hauza), ya yi bayyana cewa: "Cibiyoyin ilimin addini (Hauza) su ne cibiyoyin ilimi, tsarkakewa, koyarwa, bincike da nazari; amma sakamako na asali da aikin ƙarshe na cibiyoyin ilimin addini, shi ne kafawa da kaddamar da addini a cikin al'umma da kuma isar da sakon Allah. Duk ayyukan ilimi, bincike, da tsarkakewa, ana gabatarwa ne don cimma wannan babbar manufa, wato yada ilimin Alkur'ani da na 'Ya'yan Gidan Annabi (AS)."

Canza Al'umma Daga ta Gargajiya Zuwa ta Zamani

Hujjatul Islam Ahmed Wa'azi, yana mai nuni ga canje-canje masu zurfi na zamantakewa, ya bayyana cewa: "Al'ummar mu ta yau ta fita daga yanayin gargajiya. A cikin al'ummar gargajiya, imani da riƙon addini ana ɗaukarsa a matsayin wani abu na halitta na yau da kullum, kuma nisa da addini, sabon abu ne ba abu ne da aka saba da shi yau da kullum ba. A irin wannan al'umma, bin ka'idojin manyan al'adu yana da sauƙi, amma tare da shigar al'ummomin Musulmi cikin igiyar zamani (modernity), yanayi ya canza kuma an shigar da abubuwa na musamman cikin imani, addini, ɗabi'a, da alaƙar zamantakewa da suka dogara da tsarin addini."

Shugaban Ofishin Tablig na Hauzar Qum ya jaddada cewa: "Waɗannan canje-canje suna buƙatar cewa hanyoyin yada addini su ma su samu canji, ta hanyar amfani da fasaha da kirkire-kirkire, a daidaita su da buƙatu da yanayin al'ummar wannan zamani."

Munanan Barna Sakamakon Zamani (modernity)

Hujjatul Islam Ahmed Wa'iziy, yana mai nuni ga binciken wani masanin tunani daga yammacin duniya game da makomar zamani (modernity), ya jaddada cewa: "Ko da yake zamani (modernity) a cikin tarihi da al'adun yammacin duniya ya fara ne a ƙarni na 17, 18 da 19 ya ƙare a wadannan ƙarnukan, sannan kuma zamanin bayansa (post-modern) ya fara, amma 'tushen nazariyyarsa, buri, da sakamakon ɓarnansa' har yanzu yana ci gaba da yin mummunan tasiri a kan ɗabi'a, ruhi, riƙon addini, da asalin ɗan adam a wasu al'ummomi. Duk da faɗuwar tarihi na zamani (modernity) a yammacin duniya, duk inda ya je, yana kai wannan mummunan sakamako da ɓarnar ta sa."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha