Alhamis 18 Yuni 2026 - 22:23
Cikakken Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Game Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Tsakanin Shugabannin Iran Da Amurka

Hauza/ Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, a cikin wani saƙo da ya aike wa al’ummar Iran, ya yi ishara da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin shugabannin Iran da Amurka.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza,  Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, a cikin wani saƙo da ya aike wa al’ummar Iran, ya yi ishara da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin shugabannin Iran da Amurka. Ga cikakkiyar fassarar matanin saƙon kamar haka:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai

Al’ummar Iran masu kishin ƙasa da aminci

Kamar yadda kuka samu labari, an rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin shugabannin Iran da Amurka. A hanyar kaiwa ga wannan mataki, jami’an gwamnati, bisa kyakkyawar niyya da tausayi, sun yi ƙoƙari sosai, kuma hakika shugaban ƙasar Amurka ne ya yi amfani da kowane irin ƙarfi da matsin lamba saboda halin ƙunci da ya tsinci kansa a ciki.

Ni a mahangata ta asali ina da wani ra'ayi daban, amma saboda alƙawarin da shugaban ƙasa mai daraja, a matsayinsa na shugaban Majalisar Koli ta Tsaro ta Ƙasa, ya yi mini a madadin kansa da sauran mambobin majalisar, dangane da kare haƙƙin al’ummar Iran da kuma rundunonin Gwagwarmaya, kuma ya tabbatar da karɓar nauyin hakan, shi ne ya sa na bayar da izini. Ya kuma tabbatar da cewa idan ɓangaren Amurka ya nemi yin ƙarin buƙata, ba za su amince da hakan ba.

Daga wannan lokacin, mu, wato ku al’ummar nan mai girma da wannan bawan Allah mai ƙasƙanci, za mu kasance muna jiran ganin cikar sharuddan da aka ambata. Amma abin da yake a bayyane yake shi ne, tattaunawar fuska da fuska da za a yi a nan gaba, ba ta nufin amincewa da ra’ayin maƙiya. Muna fatan addu’ar shugabanmu (Imam Mahdi - Allah ya gaggauta bayyanarsa) ta kawo nasarori da buɗi ga al’ummar Iran mai daraja.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh

Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei

28 Khordad 1405 (18 ga Yuni 2028)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha