Talata 27 Oktoba 2026 - 23:54
An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS) na Kwana Uku a Kano, Nijeriya

Hauza/ An gudanar da zaman juyayin shahadar Sayyida Fatima Zahra (AS) na tsawon kwanaki uku, tare da halartar ɗimbin mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a cibiyoyin addini da ke birnin Kano, Nijeriya.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Nijeriya, an gudanar da zaman juyayin a ne Husainiyyar Imam Ridha (AS), domin tunawa da matsayin Sayyida Fatima Zahra (AS) da kuma bayyana soyayya da biyayya ga Iyalan Manzon Allah (SAWA).

A ranar farko na zaman, Mallam Musa Jakara me ya gabatar da jawabin. Malamin ya kawo bayanin mazalumiyar Sayyida Fatima Zahra (AS) da irin cin zalin da aka yi wa wannan tsoka ta Manzon Rahama (SAWA).

A rana ta biyu kuwa Malam Ali Kofar Waika ne ya gabatar da jawabai kan matsayin Sayyida Fatima Zahra (AS), abubuwan da suka faru bayan wafatin Manzon Allah (SAWA), da kuma batun Gonar Fadak. Ya kuma yi tsokaci kan muhimman fannoni na tarihi da aƙida da suka shafi waɗannan batutuwa, tare da jaddada matsayinta na ruhi da kuma batun cetonta a ranar Alƙiyama.

A rana ta uku kuwa, Dr. Ahmad Tijjani ya gabatar da jawabi kan matsayin Sayyida Fatima Zahra (AS), inda ya nakalto wani Hadisi Qudsi domin jaddada matsayinta a aƙidar mabiya Mazhabar Shi’a.

Daga cikin shirye-shiryen zaman an gudanar da muzaharar juyayi daga Unguwar Gwammaja zuwa Husainiyyar Imam Ridha (AS), waƙoƙin juyayi, Latmiyya da kuma karanta Ziyarar Sayyida Fatima Zahra (AS).

An kammala zaman da karanta Addu’ar Faraj da addu’ar neman gaggauta bayyanar Imam Mahdi (AF), tare da yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Jamhuriyar Musulunci da ƙungiyoyin gwagwarmaya addu’ar samun lafiya da nasara.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha