Talata 13 Oktoba 2026 - 19:38
A Yi Amfani da Ranakun Makokin Sayyida Zahra (SA) Wajen Ƙarfafa Fadaƙarwa da Haɗin Kan Al’umma

Hauza/ Ayatullah Alireza A‘arafi ya jaddada wa masu wa’azi a lokacin makokin Shahadar Sayyida Fatimatuz Zahra (SA) muhimmancin amfani da dukkan damammakin wa’azi da fayyace gaskiya, musamman a waɗannan ranaku, domin ƙarfafa fitowar al’ummar da aka tasa zuwa tituna, tare da shirya fuskantar ƙalubalen tarbiyya, al’adu da zamantakewa cikin hikima.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, Ayatullah A‘arafi, shugaban makarantun Hauza na ƙasar Iran, ya fitar da saƙo na musamman dangane da ranakun makokin shahadar Sayyida Fatimatuz Zahra (SA), inda ya bayyana muhimmancin gudanar da ayyukan wa’azi, ƙarfafa al’umma da kuma shirya ta don fuskantar ƙalubalen da ke gabanta.

Ga fassarar cikakken saƙon nasa:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

اللّهُمَّ صَلِّ عَلَی الصِّدّیقَةِ الطاهرةَ فاطِمَةَ الزَّکِیَّةِ وَکُنِ الثّائِرَ اَللّهُمَّ بِدَمِها و دم اَوْلادِها و دماء شهدائنا

Ya Allah! Ka yi salati ga Siddiƙatu Ɗahiratu, Faɗimatu Zakiyya, kuma Ka ɗauki fansa, Ya Allah, na jininta da jinin ’ya’yanta da kuma jinin shahidanmu.

Ina miƙa ta’aziyyata ga daukacin al’ummar Iran mai daraja, makarantun Hauza, manyan maraji'ai, malaman addini masu wayewar kai da masu wa’azi masu kishin farkar da al’umma, bisa zagayowar ranakun shahadar Sayyida Fatimatuz Zahra (SA).

Haka kuma, ina sanar da dakatar da karatun matakan ilimi na gaba da na ƙwarewa a makarantun Hauza, da cibiyoyi da sassan ƙwarewa na Hauza a birnin Qum, daga ranar 13 ga watan Jimada al-Ula har zuwa ƙarshen mako, wato daga 2 zuwa 7 ga watan Aban(24-27 ga Oktoba), bisa daidaitawa da manyan maraji’ai, Babbar Majalisar Hauza da sauran cibiyoyin Hauza, domin bai wa ɗalibai da malaman Hauza damar fita aikin wa’azi na jihadi da na sa-kai.

Za a kuma bar wa jami’an da abin ya shafa, bisa haɗin gwiwa da mataimakin shugaban da ya dace, tsara batutuwan da suka shafi shirye-shiryen wa’azi da hutun da ya shafi larduna da matakin farko na karatun Hauza.

Ina amfani da wannan dama ta ranakun tablig na Fatimiyya (SA) wajen tunatar da wasu muhimman batutuwa:

1. Muhimmancin bayyana matsayi da kyawawan halayen Sayyida Fatimatuz Zahra (SA)

Matsayi da darajar shugabar matan talikai sun bayyana a cikin Alƙur’ani, ruwayoyi, tarihi da sauran ilimomin Musulunci. Haka kuma, babbar taskar ilimi da ta bari tana bayyana irin matsayi da darajarta mai girma, wadda ta wuce tunanin ɗan Adam.

Fahimtar zurfin matsayinta ba ta yiwuwa ga kowa sai Ma’asumai (AS), domin matsayinta ya wuce yadda za a iya riskarsa ko bayyana shi gaba ɗaya. Sai dai, kamar yadda ake cewa, idan ba za a iya ɗibar dukkan ruwan teku ba, to a ɗebi gwargwadon ƙishirwa.

Babu shakka, ya zama wajibi a yi koyi da rayuwarta mai haske, domin ita ce bayyanar hasken Allah, hanyar isar da falalarsa, abin koyi ga Imamai Ma’asumai (AS) da dukkan mata da maza a duniya. Ita wata fitacciyar mace ce da ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sadaukar da komai domin kare matsayin Wilaya.

Saboda haka, bayyana matsayinta, girmanta, zaluncin da aka yi mata, da kuma maganganunta da kyawawan halayenta, musamman a ranakun Fatimiyya, na daga cikin nauyin da ke kan malaman Hauza, masu wa’azi da malaman addini.

A saboda haka, ya dace cibiyoyin wa’azin addini, daukacin malamai, masu wa’azi, masu gabatar da huɗubobi da sauran ƙwararru a fannin ilimin Hauza su yi amfani da wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin duniya wajen gudanar da aikinsu na kare addini da bayyana gaskiya.

Wajibi ne su yi haka tare da gudanar da sauran ayyukansu na ilimi da gudanarwa, bisa ga wannan aya mai albarka:

:«أَنْ تَقُومُوا لِلّهِ مَثْنی وَ فُرادی»

“Ku tashi domin Allah, bibbiyu da ɗaiɗaiku.”

Ta hanyar kafa ƙungiyoyin wa’azi, raya masallatai da tarukan makokin Fatimiyya, tare da mayar da hankali kan ƙarfafa fitowar al’ummar da aka tasa zuwa tituna, ya kamata su ba da kulawa ta musamman wajen bayyana matsayinta na ilimi, ibada, zamantakewa da siyasa.

Haka kuma, ya kamata a gudanar da wani sabon yunƙuri na jihadin fayyace gaskiya (Jihadut-Tabyin ) a faɗin ƙasar.

2. Warware matsalolin al’umma da ƙarfafa hidima ga jama’a

A bayyane yake cewa samun nasara a fagen wa’azi da tarbiyyar addini da juyin juya halin Musulunci yana da alaƙa da warware matsalolin al’umma, ƙoƙarin rage wahalhalu da raɗaɗin da suke fuskanta, da kuma taimaka wa jami’an gwamnati.

Haka kuma, hakan yana buƙatar yin kira ga jami’ai cikin adalci da ƙarfin hali, tare da kiyaye haɗin kai da haɗin kan al’umma bisa jagorancin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i (Allah Ya kiyaye shi).

Saboda haka, kafa ƙungiyoyi da za su ci gaba da yi wa al’umma da matasa hidima abu ne mai muhimmanci.

Haka kuma, wajibi ne jami’an ƙasar a matakai daban-daban su inganta ayyukansu wajen warware matsaloli da samar da ci gaba, tare da rage matsalolin al’umma, musamman matsalolin tattalin arziki.

Al’ummar Iran mai gwagwarmaya da jami’an ƙasar za su iya taimaka wa ƙasar ta tsallake wannan mataki mai muhimmanci ta hanyar dogaro da al’adun gwagwarmaya da tattalin arzikin juriya.

3. Ƙarfafa ruhin gwagwarmaya, haɗin kai da al’adar jihadi da shahada

Jarumtaka da ƙarfin hali, juriya da tsayin daka, faɗakarwa da dagewa, haɗin kai mai tsarki da haɗin kan zamantakewa, bin Musulunci da jagoranci, a taƙaice, al’adar jihadi da shahada, duk manyan kadarori ne da al’ummar Iran mai daraja da kuma rundunar gwagwarmaya suke da su.

Waɗannan su ne ginshiƙan da za su taimaka wajen tsallake manyan haɗurra, da kuma tafiya zuwa ga gina sabuwar wayewar Musulunci, domin ɗaukaka Iran mai daraja, ƙarfi da ci gaba, da kuma samun nasarar al’ummar Musulunci, al’ummar Iran da dakarunta masu daraja a kan masu girman kai, masu mamaye duniya da kuma Amurka da Isra’ila masu ƙarya alkawari.

Ya kamata a yi amfani da dukkan damammakin fayyace gaskiya, wa’azi, koyarwa da tarbiyya, musamman a ranakun Fatimiyya, domin ƙarfafa wannan al’ada da tabbatar da wannan tunani.

Haka kuma, wajibi ne a ƙara shiri domin fuskantar dukkan ƙalubale da matakai masu wuya da ke tafe cikin hikima da basira.

4. Fayyace rayuwar Sayyida Fatimatuz Zahra (SA) wajen fuskantar ƙalubalen al’adu da zamantakewa

A halin da ake ciki, yayin fuskantar ƙalubalen al’adu, ginshiƙan iyali da al’umma mai lafiya da ci gaba, tare da ƙimomin hijabi da kamun kai, suna fuskantar manyan ƙalubale.

Saboda haka, bayyana salon rayuwa na wayewa, imani da kamun kai na shugabar matan duniya, Sayyida Fatimatuz Zahra (SA), na daga cikin muhimman nauyin da ke kan kowa, musamman mata masu tsoron Allah, ’yan mata masu kamun kai, da kuma ’yan’uwa maza da mata masu wa’azi da ilimin addini.

Ya kamata a yi amfani da dukkan damammakin kafafen yaɗa labarai da na zamani, tarukan al’adu da addini, da hanyoyin tarbiyya da wa’azi daban-daban, tare da damar ranakun Fatimiyya, domin rage matsalolin ɗabi’a, al’adu da zamantakewa.

Haka kuma, ya kamata a yi kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su nemo hanyoyin magance waɗannan matsaloli tare da ɗaukar matakan da doka ta tanada.

A ƙarshe, ina miƙa gaisuwa da yabo ga Annabawa, Waliyai da wasiyyai na Allah, musamman Cikamakin Annabawa (SAWA), da wanda muke jiran bayyanarsa, Hujjatul Asr (AF), da Imam Khumaini (Allah Ya yarda da shi), da dukkan shahidan Yaƙin Tilasci na Uku, musamman Jagora kuma Imam Shahid (RA), da manyan Maraji’ai, Jagoranci, dakarun soji da rundunar gwagwarmaya.

Ina roƙon Allah Ya ba al’ummar Iran mai juriya, al’ummar Musulunci da aka farfaɗo da ita, masu shiryar da al’umma (RA), da manyan malaman addini lafiya, ɗaukaka da nasara.

Ina fatan Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi dukkan zaman makoki da ƙoƙarin masu hidima a wannan fanni, Ya kuma ba su kulawa da falalarsa ta musamman.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai.

Ayatullah Alireza A‘arafi

Shugaban Makarantun Hauza na Ƙasar Iran

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha