Laraba 7 Oktoba 2026 - 21:52
Ya Kamata 7 ga Oktoba Ya Zama Ranar Farkawar Al’ummar Musulmi da Goyon Bayan Falasɗinu

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Jawad Naqawi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: “Ya kamata 7 ga Oktoba ta zama wata dama ta ci gaba da raya batun Falasɗinu, bayyana goyon baya da haɗin kai ga al’ummar Gaza da ake zalunta, da kuma ƙarfafa farkawar al’ummar Musulmi.”

A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, yayin ranar tunawa da “Guguwar Al-Aƙsa”, Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Jawad Naqawi, shugaban ƙungiyar Farkawar Al’ummar Musulmi ta Mustafa na Pakistan, ya jaddada muhimmancin tunawa da 7 ga Oktoba a matsayin ranar raya batun Falasɗinu, bayyana goyon baya ga al’ummar wannan ƙasa da ake zalunta, da kuma ƙarfafa farkawar al’ummar Musulmi.

Ya ce: “Operation ɗin Guguwar Al-Aqsa ta sake sanya batun Falasɗinu a sahun gaba a matakin duniya, kuma a yanzu ya zama wajibi a mayar da 7 ga Oktoba zuwa wata dama ta tallafa wa al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, tare da nuna adawa da matakan Isra’ila da Amurka.”

Shugaban ƙungiyar Farkawar Al’ummar Musulmi ta Mustafa na Pakistan ya ƙara da cewa: “Batun Falasɗinu da Gaza ba wai ya shafi al’ummar Falasɗinu kaɗai ba ne, illa dai batu ne da ya shafi daukacin al’ummar Musulmi da kuma duk wani mutum mai hankali da ’yanci. Saboda haka, ya kamata a gudanar da jerin gwano, taruka da shirye-shirye daban-daban a faɗin Pakistan, domin bayyana haɗin kai da al’ummar Falasɗinu da ake zalunta da kuma nuna goyon baya ga gwagwarmaya.”

Ya yi nuni da shiru da wasu gwamnatocin Musulmi suka yi da kuma raunin ayyukan hukumomin ƙasa da ƙasa dangane da rikicin Falasɗinu, inda ya ce: “Ci gaba da wannan yanayi ya ƙara faɗaɗa girman bala’in da ke faruwa a Falasɗinu. Bai kamata al’ummar Musulmi su takaita goyon bayansu ga Falasdinu da yin Allah-wadai da fitar da sanarwa kawai ba; a maimakon haka, ya kamata su ɗauki matakai na zahiri kuma masu tasiri domin tallafa wa al’ummar Falasɗinu da kare haƙƙoƙinsu.”

Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Jawad Naqawi ya jaddada a ƙarshe cewa: “Ya kamata 7 ga Oktoba ya zama ranar raya batun Falasɗinu, tsayawa tare da waɗanda ake zalunta, da yaɗa saƙon farkawa a tsakanin al’ummar Musulmi.”

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha