Laraba 30 Satumba 2026 - 22:40
Mu Riƙa La’akari da Imam Zaman (AF) a Shawarwarin Rayuwarmu

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Husain Jushƙaniyan, mamba a kwamitin gudanarwa na Cibiyar Tarihin Shahidai ta Qum, ya bayyana cewa idan muka riƙa la’akari da ƙa’idar Allah tare da lissafin abubuwan duniya a cikin al’amuran rayuwarmu, matsaloli da fargaba da dama za su rasa tasirinsu, domin babu wani ƙarfi da ya fi ƙarfin ikon Allah

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a yayin wani jawabi da ya gabatar a Masallaci Mai Tsarki na Jamkaran, ya girmama tunawa da shahidan Yaƙin Kariya Mai Tsarki, shahidan Gwagwarmaya, musamman Shahid Sayyid Hasan Nasrullah, yana mai roƙon Allah Ya azurta kowa da kyakkyawan ƙarshe da mutuwa cikin ɗaukaka.

Hujjatul Islam Jushƙaniyan ya bayyana cewa duk da kasancewar wasu ƙa’idojin halitta, kamar yadda wuta take ƙone abu, ruwa yake kashe ƙishirwa, abinci kuma yake kawar da yunwa, ikon Allah yana saman dukkan waɗannan ƙa’idoji. Ya kawo misalin Annabi Ibrahim (AS), lokacin da aka jefa shi cikin wutar Namarud, inda Allah Ya umurci wutar da ta zama sanyi da aminci a gare shi.

Ya ƙara da cewa idan aka kalli abubuwan da suka faru a tarihin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fuskar lissafin duniya kawai, wasu al’amura ba za su bayyana ma’anarsu yadda ya kamata ba. Amma idan aka haɗa lissafin duniya da la’akari da nufin Allah, ana iya fahimtar abubuwa ta wata fuska daban.

Mumini Ba Ya Yanke Ƙauna Da Rahamar Allah

Hujjatul Islam Jushƙaniyan ya yi ishara da labarin Annabi Musa (AS) da mutanensa lokacin da suka fuskanci rundunar Fir’auna, teku kuma yana gabansu. A lokacin da mutanensa suka yi tunanin babu mafita, Annabi Musa (AS) ya ce: «كَلَّا إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ», ma’ana: “A’a, Ubangijina yana tare da ni, kuma zai shiryar da ni.”

Ya bayyana cewa mumini ba ya kallon matsaloli a matsayin ƙarshen mafita, domin idan mutum ya dogara ga Allah tare da kiyaye taƙawa, Allah zai buɗe masa hanyar fita daga matsalolinsa.

Shahidai Sun Yi Aiki Bisa Nauyin Da Ke Kansu

A wani ɓangare na jawabinsa, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin siffofin shahidai ita ce gudanar da rayuwarsu bisa nauyin da ke kansu, ba bisa son rai ba.

Ya kawo misalan shahidai da suka fifita sauke nauyin da ke kansu a kan sha’awarsu ta duniya, tare da jaddada cewa wannan hali bai taƙaita ga fagen fama kawai ba, har ma yana bayyana a mu’amala da iyali, abokai da kuma dukiyar jama’a.

Ya kuma yi ishara da rayuwar Shahid Mahdi Zainuddin da Shahid Ahmad Kazimi, inda ya bayyana yadda shahidai suke taka-tsantsan wajen amfani da dukiyar gwamnati, domin sun fahimci cewa amana ce da za a tambaye su a kanta.

Mu Riƙa La’akari da Imam Zaman (AF) a Rayuwarmu

Hujjatul Islam Jushƙaniyan ya jaddada cewa manufar ziyarar Masallacin Jamkaran ita ce kusantar Imam Zaman (AF), yana mai cewa idan muka yi imani da Imam a matsayin hujjar Allah, ya kamata mu riƙa la’akari da shi a cikin dukkan shawarwarin rayuwarmu.

Ya ce kafin mutum ya fita daga gidansa, ya kamata ya yi tunanin ko suturarsa da kamanninsa sun dace da abin da zai faranta wa Imam Zaman (AF) rai. Haka kuma, a maganganunsa da tunaninsa, ya kamata ya riƙa la’akari da abin da Imam yake so.

Ya bayyana cewa addu’ar “مَتَی نَرَاکَ وَ نَرَاهُ” ba tana magana ne kawai kan lokacin bayyanar Imam ba, tana kuma iya nufin mutum ya riƙa la’akari da abin da Imam yake so a cikin ayyukansa, maganganunsa, tunaninsa da zaɓinsa.

Taku Ɗaya Domin Allah, Taku Ɗaya Zuwa Ga Imam Zaman (AF)

Hujjatul Islam Jushƙaniyan ya kawo wani labari daga Sheikh Ja’afar Shushtari, inda a wani taro da babu isasshen wurin zama, ya nemi mutane su matsa gaba da mataki ɗaya domin su ba wa wasu damar zama. Daga nan sai ya bayyana cewa wannan shi ne saƙon jawabinsa: mutum ya ɗauki mataki ɗaya domin Allah a rayuwarsa.

Ya ce wannan ita ce manufar ziyarar Jamkaran, wato mutum ya kusanci Imam Zaman (AF) da manufofinsa, tare da tambayar kansa irin gudummawar da yake bayarwa wajen taimaka wa addini da al’umma.

Ya kuma kawo wasiyyar Shahid Ahmadreza Ahadi, wanda ya zo na farko a jarrabawar shiga jami’a ta ƙasa a shekarar 1364 a kalandar Hijirar Shamsiyya, inda ya jaddada cewa kada a bar umarnin Imam a baya ba tare da aiwatar da shi ba.

Shahidai Suna Kula da Dukiyar Jama’a

A ci gaba da jawabinsa, Hujjatul Islam Jushƙaniyan ya kawo misalin wani mayaƙi wanda, kafin ya shiga yankin da aka dasa nakiyoyi, ya cire takalmansa domin kada dukiyar gwamnati ta lalace idan ya rasa ransa, ta yadda wani mayaƙi zai iya amfani da su.

Ya bayyana cewa wannan yana nuna irin kulawar da shahidai suke yi wa dukiyar jama’a, domin suna ganin kansu masu ɗauke da nauyi ne a gaban Allah da al’umma.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi (AF), Ya ba wa waɗanda suka samu raunuka a fagen gwagwarmaya lafiya, Ya kiyaye Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ya kuma ba wa Gwagwarmaya nasara. Ya roƙi Allah Ya sanya dukkan muminai cikin sahihan mataimaka da masu share fagen bayyanar Imam Mahdi (AF).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha