Alhamis 30 Yuli 2026 - 11:45
Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Hauza/ Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na ci gaba da gudanar da ayyukan hidima ga maziyartan Imam Hussain (A.S.) a hanyar tattakin Arba'in na shekarar 1448 Hijira.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, maukibin Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yana ci gaba da karɓar baƙuncin dubban maziyarta tare da samar musu da hidimomi daban-daban a yayin tattakin Arba'in daga Najaf zuwa Karbala.

Daga cikin hidimomin da ake bayarwa akwai raba ruwan sha, shayi, kayan marmari da kuma abinci mai zafi domin sauƙaƙa wa maziyarta gudanar da wannan ibada mai albarka.

Baya ga hidimomin jin daɗi, an kuma tanadi sashen al'adu inda aka shirya bajekolin hotunan Harkar Musulunci a Nijeriya da shahidan Harkar. Haka kuma, ana rarraba ƙananan littattafai da takardu masu ɗauke da tarihin Harkar Musulunci, tarihin Jagoranta Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da yaruka daban-daban (Larabci, Farisanci da Turanci), da sauran muhimman bayanai game da manufofi, ayyuka da kuma gudummawar Harkar.

An bayyana cewa maukibin Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yana a amudi na 1117 a hanyar Najaf zuwa Karbala, inda yake ci gaba da maraba da maziyartan Arba'in tare da yi musu hidima.

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky Na Ci Gaba da Yi Wa Mahajjatan Arba'in Hidima a Hanyar Najaf Zuwa Karbala

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha