Asabar 25 Yuli 2026 - 21:24
Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jagoranci Taron Tunawa da Shahidan Quds na Shekarar 2014 Karo na 12

Hauza/ An gudanar da taron tunawa da Shahidan Quds na shekarar 2014 karo na 12 tare da halartar dimbin al'umma, malamai, shugabannin addinai, iyalan shahidai da sauran baƙi a cibiyar Darur Rahma da ke yankin Dambo a birnin Zariya.

A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da wannan taro ne a ranar Asabar, 25 ga Yulin 2026 (11 Safar 1448H), inda Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya gabatar da muhimmin jawabi.

A farkon jawabinsa, Sheikh Zakzaky (H) ya bayyana alhininsa kan kwanakin Ashura, shahadar Imam Hasan al-Mujtaba (A.S.), da kuma tunatarwa kan arba'in da take gabatowa, tare da jana'izar Shahidin wannan al'umma, Shahid Sayyid Ali Khamene'i (Q).

Da yake magana kan dalilin gudanar da taron, ya ce: "Wannan taro, taro ne na tunawa da waƙi'ar da ta auku a ranar 28 ga watan Ramadan 1436, daidai da 25 ga watan Yulin 2014. Shekaru 12 ke nan cif-cif a ƙidayar Miladiyya."

Jagoran ya kuma yi bayani kan tarihin fara Muzaharar Ranar Quds ta Duniya a Najeriya, yana mai cewa an fara gudanar da ita ne a Zariya a Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan, sannan daga baya ta bazu zuwa sauran sassan ƙasar sakamakon ƙaruwa da yawan masu halarta. Ya ce wannan ya nuna yadda batun Falasɗinu ya samu karɓuwa a tsakanin al'umma.

Sheikh Zakzaky (H) ya jaddada cewa: "Muzaharar Quds ta Duniya nuna goyon baya ce ga al'ummar Falasɗinu waɗanda 'yan mamaya suke zalunta tsawon shekaru fiye da saba'in." Ya ƙara da cewa: "Ana nuna cewa, ba a yadda da zalunci ba ne."

Da yake tuna harin da aka kai wa Muzaharar Quds a shekarar 2014, ya ce: "A wannan shekarar, a nan Najeriya ne kaɗai aka kai hari kan Muzaharar Quds. Wannan abin da ya faru bai ɓoye wa al'umma ba. Ashe ba su daina ba, bayan shekara guda suka sake diran mana da nufin share kowa da kowa. Da ma manufar ke nan a waƙi'ar 25 ga watan Yulin 2014, sai dai ta tsaya a kan mutum 34."

Dangane da masu adawa da Muzaharar Quds domin nuna goyon baya ga Isra'ila, Jagoran ya ce: "Tunda mu muna nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan, sai ku ware wata rana ba Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan ba, ku nuna goyon baya ga Isra'iliyawa."

Ya kuma jaddada cewa barazana da kashe-kashe ba za su hana mabiyan wannan tafarki ci gaba ba, yana mai cewa: "Ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, za mu fito."

Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa shahada a tafarkin Allah ita ce mafi girman ɗaukaka, yana mai cewa: "Abin alfahari ne a kashe ka a tafarkin Allah." Ya ƙara da cewa: "Muna nan daram a wannan tafarki da aka kashe waɗannan shahidai. Ko a karrama mu ko mu mutu a kan wannan tafarki, ba za mu sauya ba."

A wani ɓangare na jawabinsa, ya yi kira ga waɗanda suka aikata kisan gilla da su tuba, yana mai gargadin cewa idan ba su tuba ba, "za su yi hasarar duniya da lahira."

A ƙarshe, Jagoran ya bayyana manufar taron da cewa: "Wannan taro namu alama ce ta so. Muna son waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a wannan tafarki. Muna tunawa da su kuma muna ganin muna samun lada ne."

Bayan kammala jawabin, Sheikh Zakzaky (H) ya gana da malamai, fastoci, baƙi da aka gayyata da kuma iyalan shahidai. Daga nan ya ziyarci ƙaburburan shahidan da aka binne a Darur Rahma tare da yi musu addu'a.

An fara taron ne da addu'a da karatun Alƙur'ani Mai Girma, sannan aka gabatar da shirye-shiryen al'adu, faretin girmama shahidai da kuma wasan kwaikwayo kan waƙi'ar Quds. An rufe taron da addu'ar Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jagoranci Taron Tunawa da Shahidan Quds na Shekarar 2014 Karo na 12

Zariya | Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jagoranci Taron Tunawa da Shahidan Quds na Shekarar 2014 Karo na 12

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha