Kamfanin Dillancin Labarai na Hauza | A tunanin Alƙur'ani, imani da ɗaukaka (izzah) tagwaye ne, kuma a ƙamusin Alƙur'ani babu gurbin Musulmi mai razana da rauni. Adawa tsakanin rundunar imani da rundunar kafirci wata sunnah ce da ba ta canzawa; domin kafirci a asalinsa yana gaba da bayyanar Musulunci na gaskiya, kuma yana amfani da dukkan ƙarfinsa wajen kashe hasken Allah (duk da cewa hasken Allah ba ya mutuwa). A irin wannan fafatawa, yin shiru, mika wuya da tsoron maƙiyi ba wai kawai a kira su "yin taka-tsantsan" ba ne, a'a, suna nufin fita daga tafarkin tauhidi.
Alƙur'ani Mai Girma, wajen bayyana siffofin mumini, ya gabatar da wata muhimmiyar ma'ana ta aikin alheri, wadda a cikin fahimtar yau ta muminai aka manta da ita:
«لَا یُصِیبُهُمْ ظَمَأٌ وَلَا نَصَبٌ وَلَا مَخْمَصَةٌ فِی سَبِیلِ اللَّهِ وَلَا یَطَئُونَ مَوْطِئًا یَغِیظُ الْکُفَّارَ وَلَا یَنَالُونَ مِنْ عَدُوٍّ نَیْلًا إِلَّا کُتِبَ لَهُمْ بِهِ عَمَلٌ صَالِحٌ.»
"Ba wata ƙishirwa, ko wahala, ko yunwa da za ta same su a tafarkin Allah; kuma ba su taka wani wuri da zai fusata kafirai, ko su sami wani abu daga maƙiyi ba, face an rubuta musu wani aikin alheri saboda haka." (Suratut Tauba, aya ta 120).
A fahimtar da ake yi a yau a cikin al'ummomin Musulmi, ana takaita aikin alheri ga ibadojin mutum kamar salla, azumi, zakka da makamantansu. Amma bisa ga ma'anar wannan aya, fusata maƙiyan Allah shi ma wani muhimmin aikin alheri ne. Wannan shi ne abin da rashin fahimtarsa ya jefa al'ummar Musulmi cikin rauni da rashin motsi tsawon tarihi.
Domin ƙarin fahimtar wannan aikin alheri da ayar ta ambata, sai mu koma ga Suratul Asr:
«وَالْعَصْرِ. إِنَّ الْإِنْسَانَ لَفِی خُسْرٍ. إِلَّا الَّذِینَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ.»
"Ina rantsuwa da lokaci. Lalle ne mutum yana cikin hasara. Sai waɗanda suka yi imani, suka aikata ayyukan alheri, suka yi wa juna wasiyya da gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da haƙuri."
Idan muka ɗauki maganar Allah Maɗaukaki a cikin Suratul Asr a matsayin ma'aunin samun tsira, za mu fahimci cewa fita daga hasara ta har abada ba ta yiwuwa sai da imani, wanda ɗaya daga cikin manyan siffofinsa shi ne aikin alheri. A mahangar Alƙur'ani, ɗaya daga cikin ayyukan da aka ɗauka a matsayin aikin alheri, wanda yake fitar da mai aikata shi daga cikin masu hasara, shi ne ɗaukar mataki a hanyar da ke fusata kafirai.
Wannan aya tana ɗauke da wata muhimmiyar gaskiya ta dabarun rayuwar al'umma, wadda ya kamata al'ummar Musulmi su koma gare ta domin kuɓuta daga ɗaurin mulkin mallaka da zalunci. Yin watsi da wannan ƙa'ida ba wai kawai yana haifar da hasarar duniya da lahira ba ne, har ma yana lalata asalin martabar Musulunci.
A tsarin Alƙur'ani, Musulmi mai rauni, mai kasala da mai tsoro ba ya cikin sahun mayaƙan rundunar gaskiya; domin ɗaukaka tana ga Allah da Manzonsa da muminai. Saboda haka, duk wani motsi a gaban gaskiya da ba ya fusata maƙiyan addinin Allah, to ya dace a yi shakku kan sahihancinsa na juyin-juya-hali da na imani.
— Mustafa Amini
Ra'ayinka