A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ya tafi kasar Iraki domin halartar jana'iza da bankwana da Shahidin jagora, Ayatullah al-Uzma Shahid Sayyid Ali Hussaini Khamenei (Q) wanda za a gudanar a biranen Bagdad, Najaf da Karbala masu tsarki.
Bayan kammala tarukan bankwana da gangar jikin Shahidin Jagoran dai, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) zai kuma wuce birnin Mashhad na kasar Iran domin halartar taron jana'iza da bankwana na karshe inda a nan ne kuma za a binne gangar jikin Shahidin Jagoran a Haramin Imam Ridha (A.S).




Ra'ayinka