Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya kawo cikakken bayanin muhimmin sako kuma mai cike hangen nesa na Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun Hauza na kasar Iran, a daidai lokacin bankwana da jana'izar tarihi ta gangar jiki mai tsarki na Shugaba Ayatullah al-Uzma Imam Khamenei (Q), inda ya bayyana nauye-nauye da sakwannin shahadar Imam Shahid ga Iran, duniyar Musulunci, da dukkan 'yantattun duniya kamar haka:
Bismillahir Rahmanir Rahim
﴿وَلَا تَحْسَبَنَّ الَّذِینَ قُتِلُوا فِی سَبِیلِ اللَّهِ أَمْوَاتًا بَلْ أَحْیَاءٌ عِنْدَ رَبِّهِمْ یُرْزَقُونَ﴾
﴿مِنَ الْمُؤْمِنِینَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَیْهِ فَمِنْهُم مَّن قَضَیٰ نَحْبَهُ وَمِنْهُم مَّن یَنتَظِرُ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِیلًا﴾
Ya ku babbar al'ummar Musulmi, 'yantattu da raunana na duniya, al'ummomin da suka farka lamirai ma'abota ilimi a duk fadin duniya:
A yau duniyar Musulunci, har ma da dukkan bil'adama masu kishirwar adalci, suna alhinin juyayin babban mutumin da bai takaita ga iyaka guda ko al'umma guda ba, a'a, ya kasance jigo na hadin gwiwa ga al'umma baki daya kuma magajin tafarkin Annabawa da waliyyai. Shahadar zalunci da aka yi wa jagora mai hikima, babban marja'i kuma jagoran juyin juya halin Musulunci, Hazrat Ayatullah al-Uzma Imam Khamenei (R), ba lamari ne da za a fahimta a cikin kuntaccen yanki ba; a'a, dole ne a dubi wannan lamari a ma'aunin duniyar Musulunci da kuma hangen nesa na manyan sauye-sauyen bil'adama. Wannan babban mutum ya kasance babban tauraro mai falaloli marasa iyaka da siffofi na musamman wadanda haskensu ya haskaka a Iran da duniya, kuma ya canza tsarin duniya tare da zama sanadin ci gaba daban-daban da daukakar Iran da al'ummar Musulmi.
Imam Shahid ya kasance abun koyi ga tunanin duniya baki daya. Tunaninsa ya tsallake iyakokin kabilanci da na kasa, kuma ya gina tsari na duniya inda dabi'un bil'adama na hadin gwiwa, mutuncin dan adam, adalci, da gwagwarmaya a gaban masu girman kai suka sami murya guda. Ya fahimci kalubale da barazanar duniya daki-daki, kuma ya yi magana da yaren da ya dace da zamanin wayewar kai. Akidar da ya gabatar ita ce akidar 'yantar da duniya baki daya; kalami ne da ke kawo sani ga Allah a cikin rayuwar raunana kuma yake mayar da imani ya zama karfin 'yancin al'umma. Babban matsayinsa na marja'iyya shi ma yana cikin wannan tafarki ne: marja'iyyar da ta hada ilimin fikihu da nauyin tarihi da damuwar al'umma. Shi ne uban al'umma, ruhin juriya, jagoran al'umma, kuma rayuwar kasa.
Babban laifin da bakaken fuskokin Amurka da Isra'ila suka tafka wanda ya kai ga wannan shahada, a cikin gurbataccen tunanin masu tsara shi, an yi shi ne da nufin yin babban naushin mutuwa ga jikin wannan harka, al'umma, da gwamnati, da nufin ruguza su farat daya. A daidai nan ne daya daga cikin sassan girman jagorancinsa yake bayyana. Ya shafe shekaru yana gina al'umma da kuma gina gwamnati; ya hada mutane ba da kansa ba, a'a, ya hada su da Allah, da madaidaitan ginshiki, da manyan manufofi na ba da rai da rayuwa. Shugabannin da suka gina tafarkinsu a kan kwarjinin kansu na kashin kai, da zaran wannan kwarjini ya gushe, tsarin al'ummarsu da gwamnatinsu na rugujewa ne. Amma tsarin jagorancin Imam Shahid ya kasance ta yadda duk da hasashen da makiya suka yi na ganin an shiga rudani da rushewa, sai gashi komai ya tafi cikin dorewa da hadin kai cikin yanayi na ban mamaki. Wannan wata shaida ce ta daban kan gaskiya da zurfin wannan makaranta da ta hada mutane da Allah ba da daidaikun mutane ba.
Ya ku al'umma madaukakiya! Dole ne kishin daukar fansar wannan jini mai tsarki ya kasance mai rai kuma mai dorewa a cikin zukata; ba a matsayin wutar lokaci kalilan ba, a'a, a matsayin kudiri mai dorewa na bin wannan tafarki da ya shayar da shi da jininsa. Jinin shahidai shi ne hasken tafarki, kuma nuna damfaruwa da sadaukarwa a kan manufofinsu shi ne ainihin daukar fansa. Daukar fansar Imam Shahid ba abu ne na bugun zuciya ko garaje ba; a'a, ci gaba ne na yaki da zalunci da girman kai a cikin sabon salo, kuma yana daya daga cikin muhimman ayyuka na ƙungiyoyin gwagwarmaya (Axis of Resistance).
Shahadarsa tana dauke da bayyanannun sakwanni da nauye-nauye ga sassa daban-daban na duniyar Musulunci da Iran:
Sako na Farko: Shi ne cewa shahada jari ce ga al'umma ba asara ba, kuma tana kawo kaskanci da halaka ga makiya ba wai nasara a gare su ba. Makiya sun zata cewa ta hanyar kashe masani kuma jagoran Iran ta Musulunci za su iya karya karsashin al'umma; alhali tsarin Ubangiji yana nuna cewa jinin shahidai masu tsarki yana kara sa jijiyoyin imani zurfi, yana karfafa gwiwar al'umma, kuma yana haskaka tafarkin gaskiya.
Sako na Biyu: Shi ne rugujewar lissafin tsarin mulkin mallaka da girman kan duniya. A cikin wannan kallafaffen yaki na uku, makiyi azzalumi kuma mai laifi ya zuba ido wajen cimma wasu manufofi wadanda suka zama kamar mafarki maras kyau da bai cika ba. Shirin raba kan Iran, kifar da tsarin mulki, sallamawar al'ummar Iran, mamaye arzikin kasa, samar da tsaro ga haramtacciyar daular sahyoniyawa, da ruguza kungiyoyin muƙawama, duka sun rushe albarkacin jinin Imam, kwamandoji, shahidan Minab, da dubban shahidai na al'ummar Iran mai bin tafarkin Imam Hussaini. Makiya ba su cimma ko daya daga cikin wadannan manufofi ba, sai ma, sun tafka manyan asarori. Rushewar sansanonin sojin Amurka a yankin, lalata sansanonin dabarun yaki na Isra'ila, karfafa gwiwar kungiyoyin muƙawama, iko da mashigar Hormuz, farkawar al'ummar Iran, karyata shirin tsoratarwa da sunan Iran, karuwar goyon bayan duniya ga Iran, da bayyana mummunar fuskar Amurka da sahyoniyawan dake kashe yara, duka suna nuna bayyanar Iran a matsayin babbar daula ta duniya.
﴿إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ یَنْصُرْکُمْ وَیُثَبِّتْ أَقْدَامَکُمْ﴾
Sako na Uku: Shi ne bayyana hadin kan al'umma. A yau, an kafa hadakar bai-daya ta Hizbullah na Lebanon, Ansarullah na Yemen, Hashdus Sha'abi na Iraki, da gwagwarmayar Falasdinu, wacce dole ne ta kara hadewa da dankon zumunci kowace rana.
Yana da kyau a gane cewa wannan lokaci, lokaci ne mai kaddarawa da muhimmanci. Sabon zamani na ikon Iran, Musulunci, da ƙungiyoyin muƙawama ya fara. Wadannan manyan sauye-sauye sune sakamakon shekaru aru-aru na kokari da gwagwarmayar malamai na kwarai da al'umma masu muƙawama, wanda aka fara daga babban Imam (Khumaini) kuma ya ci gaba da Imam Shahid (Khamenei); gadon da ya nuna kansa domin 'yantar da al'umma da raunana daga radadin shekaru aru-aru, da kuma gina sabbin rukunoni na iko da wayewar kai ta Musulunci, da share fage ga bayyanar rana madaukaki ta shugabanci (Imam Mahdi).
Babban Taron Jana'iza da Ci Gaban Tafarki
Taron jana'izar wannan gangar jiki mai tsarki dole ne a rubuta ta a matsayin wani taro na musamman da ba shi da tsara a tarihi. Wannan halartar babban taro da kanta za ta kasance babbar murya ga gaskiyar wannan tafarki da sabunta alkawari da tsarin imani, adalci, 'yanci, daukaka, juriya, da fatan gobe na gari.
Ina gayyatar dukkan sassa na mutane, masoyan makarantar Khumaini da Khamenei, da dukkan masu juyayin wannan babban rashi, da su halarci wannan babban taro da dumi-duminsu domin nuna matsayin wancan masoyi a cikin zukatan mutane masu daraja, tare da bayar da sakon cewa tafarkin juyin juya hali da wancan shahidi na watan Ramadan zai ci gaba, kuma za a dauki fansar jinin mutane da na shahidai masu daraja.
A wannan lokaci, ta yaya ba za mu tuna da babban injiniyan wannan harka, wato Hazrat Imam Khumaini (Q) ba; wannan mai raya addini wanda da tunaninsa madaukaki ya gina tushen kungiyoyin gwagwarmaya kuma ya motsa ayarin shahidai. Imam Shahid ya kasance mai ci gaba na gaskiya a kan wannan tafarki da wannan makaranta, kuma har zuwa numfashinsa na karshe, ya tsaya a kan manufofin juyin juya halin Musulunci kuma ya sadaukar da kansa ga mutane da Iran ta Musulunci.
Ci gaban tafarkin Imam Shahid yana cikin yin biyayya ta gaskiya, tare da sani, da imani da kwararren masanin shari'a (Wilayatul Faƙih) na wannan lokaci. Mataimakin Imamuz Zaman, Hazrat Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, shi ne bayyanannen tafarki mai haske na ci gaban wanzuwa, tunani, da kuma tsarin jagoranci mai albarka na wannan Imam Shahid.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka darajar wannan shahidi masoyi, ya hada shi da waliyyan Allah, ya ba al'umma hakuri da basira, ya karfafa hadin kan al'ummar Musulmi, ya karfafa kungiyoyin gwagwarmaya, ya farkar da al'umma, kuma ya share fage ga cikar alkawuran Ubangiji.
Tafarki a bayyane yake, kuma ayari yana kan tafiya.
﴿وَاللَّهُ غَالِبٌ عَلَیٰ أَمْرِهِ وَلَٰکِنَّ أَکْثَرَ النَّاسِ لَا یَعْلَمُونَ﴾
Wassalamu Alaikum wa Ibadillahis Salihin.
Ra'ayinka