A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta shirya tare da gudanar da raya dararen Layalul Qadr (19, 21 da 23) na shekarar 1447.
A yayin wannan raya dararen, an gudanar da dukkan ayyukan dararen Layalul Qadr da suka zo a littattafan addu'o'in kamar su Mafatihul Jinan, wadanda suka hada da addu'ar Jaushil Kabir, salla raka'a dari, tawassuli da Alƙur'ani da sauran su.
An yi addu'ar neman kariya da dacewa ga sabon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei (H), Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), rundunonin muƙawama da kuma nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wannan fafatawa da ake. Haka nan kuma an yi addu'a ga shahidan gwagwarmaya.





Ra'ayinka