A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin darussa kan Mahdawiyya mai taken “Zūwa ga Al’umma Mai Manufa” domin yada koyarwa da ma’arifa game da Imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa).
Abu na farko da ya kamata a fahimta shi ne cewa “Ghaiba” na nufin “ɓoyewa daga ganin mutane”, ba wai rashin kasancewa ba. Wato ana nufin wani lokaci ne da Imam Mahdi (a.s) yake ɓoye daga idanun mutane, ba sa ganinsa, duk da cewa yana cikin mutane kuma yana rayuwa tare da su. Wannan gaskiya ta zo a cikin ruwayoyi da dama daga Imamai Ma’asumai.
Imam Ali (a.s) ya ce:
«فَوَ رَبِّ عَلِیٍّ إِنَّ حُجَّتَهَا عَلَیْهَا قَائِمَةٌ مَاشِیَةٌ فِی طُرُقِهَا دَاخِلَةٌ فِی دُورِهَا وَ قُصُورِهَا جَوَّالَةٌ فِی شَرْقِ هَذِهِ اَلْأَرْضِ وَ غَرْبِهَا تَسْمَعُ اَلْکَلاَمَ وَ تُسَلِّمَ عَلَی اَلْجَمَاعَةِ تَرَی وَ لاَ تُرَی إِلَی اَلْوَقْتِ وَ اَلْوَعْدِ.» (الغیبة نعمانی، ص ۱۴۴)
“Na rantse da Ubangijin Ali, Hujjar Allah tana nan tsaye a tsakanin mutane; tana tafiya a titunansu, tana shiga gidajensu da fadodinsu, tana yawo a gabas da yammacin duniya. Tana jin maganganun mutane kuma tana gaishe su. Ita tana ganin mutane amma su ba sa ganinta, har sai lokacin da aka ƙaddara ya zo.” (Alghaibatu Nu'umaniy, S:144)
Haka kuma, an ambaci wani irin boyuwa daban ga wannan Imami. Imam Ja’afar al‑Sadiq (a.s) ya ce:
«إِنَّ فِی صَاحِبِ هَذَا اَلْأَمْرِ سنن [سُنَناً] مِنَ اَلْأَنْبِیَاءِ عَلَیْهِمُ السَّلاَمُ ... وَ أَمَّا سُنَّتُهُ مِنْ یُوسُفَ فَالسِّتْرُ یَجْعَلُ اَللَّهُ بَیْنَهُ وَ بَیْنَ اَلْخَلْقِ حِجَاباً یَرَوْنَهُ وَ لاَ یَعْرِفُونَهُ.» (کمالالدین، ج ۲، ص ۳۵۰)
“A cikin Mai wannan al’amari akwai halaye daga Annabawa … daga cikin halayensa da ya gada daga Annabi Yusuf shi ne ɓoyewa; Allah zai sanya wani shãmaki tsakaninsa da mutane, ta yadda za su gan shi amma ba za su gane shi ba.” (Kamaluddeen, J:2; S:350)
Saboda haka, ghaibar Imam Mahdi (a.s) tana faruwa ta hanyoyi biyu; wani lokaci yana ɓoye gaba ɗaya daga ganin mutane, wani lokaci kuma mutane suna ganinsa amma ba sa gane cewa shi ne Imam Mahdi. Duk da haka, a kowane hali yana cikin mutane kuma yana rayuwa a tsakaninsu.
Tarihin Ghaiba
Rayuwa a ɓoye ba sabon abu ba ne, kuma ba ga Imam Mahdi kaɗai aka same ta ba. Ruwayoyi sun nuna cewa wasu manyan Annabawan Allah sun yi wani lokaci na rayuwarsu cikin ghaiba saboda hikima da maslahar Allah.
Daga cikin Annabawan da suka fuskanci irin wannan akwai: Idris, Nuhu, Salihu, Ibrahim, Yusuf, Musa, Shu’aib, Ilyas, Sulaiman, Daniyal da Isa (a.s). Kowannensu ya yi wani lokaci na rayuwarsa cikin ghaiba gwargwadon yanayin da ya same shi.
Saboda haka ne ruwayoyi suka bayyana cewa ghaibar Imam Mahdi (a.s) ma tana daga cikin sunnonin Annabawa, kuma ɗaya daga cikin dalilan boyuwarsa shi ne aiwatar da wannan sunnah ta Annabawa a rayuwarsa.
Imam Ja’afar al‑Sadiq (a.s) ya ce:
«إِنَّ لِلْقَائِمِ مِنَّا غَیْبَةً یَطُولُ أَمَدُهَا؛ فَقُلْتُ لَهُ وَ لِمَ ذَاکَ یَا اِبْنَ رَسُولِ اَللَّهِ؛ قَالَ إِنَّ اَللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ أَبَی إِلاَّ أَنْ یُجْرِیَ فِیهِ سُنَنَ اَلْأَنْبِیَاءِ عَلَیْهِمُ السَّلاَمُ فِی غَیْبَاتِهِمْ.
“Lalle ga Al‑Qa’im daga gare mu akwai boyuwa mai tsawon lokaci.” Sai aka tambaye shi: “Me ya sa hakan zai faru, ya ɗan Manzon Allah?” Sai ya amsa: “Saboda Allah Madaukaki ya ƙaddara cewa sunnonin da suka faru ga Annabawa a boyuwarsu su ma su faru gareshi.” (Ilalush-Sharayi'u, J: 1; S: 245)
Daga wannan magana ana fahimtar cewa batun boyuwar Imam Mahdi (a.s) an riga an ambace shi tun shekaru da dama kafin haihuwarsa. Shugabannin Musulunci daga Manzon Allah (s.a.w) har zuwa Imam Hasan al‑Askari (a.s) sun yi magana game da boyuwarsa, wasu siffofinta, abubuwan da za su faru a lokacin boyuwar, da kuma ayyukan da ya kamata muminai su yi a wancan lokaci.
Haka kuma Manzon Allah Muhammad (s.a.w.a) ya ce:
«اَلْمَهْدِیُّ مِنْ وُلْدِی اِسْمُهُ اِسْمِی وَ کُنْیَتُهُ کُنْیَتِی أَشْبَهُ اَلنَّاسِ بِی خَلْقاً وَ خُلْقاً تَکُونُ بِهِ غَیْبَةٌ وَ حَیْرَةٌ تَضِلُّ فِیهَا اَلْأُمَمُ ثُمَّ یُقْبِلُ کَالشِّهَابِ اَلثَّاقِبِ یَمْلَؤُهَا عَدْلاً وَ قِسْطاً کَمَا مُلِئَتْ جَوْراً وَ ظُلْماً.» (کمال الدین، ج ۱، ص ۲۸۶)
“Mahdi daga cikin zuriyata ne. Sunansa kamar sunana, kunyarsa kuma kamar kunyata. Shi ne mafi kama da ni a halitta da ɗabi’a. Zai yi wani lokaci na boyuwa da ruɗani wanda al’umma za su rikice a cikinsa. Bayan haka zai bayyana kamar tauraro mai haske, ya cika duniya da adalci da gaskiya kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya.”
(Wannan bahasi zai ci gaba.)
An tsakuro daga littafin Negin-e Afarinesh tare da dan gyara kadan
Ra'ayinka