Jummaʼa 30 Oktoba 2026 - 16:01
“Wannan Hukunci Hari Ne Kan ’Yancin Addini da Martabar Malaman Musulunci”

Hauza/ Ayatullah A’arafi ya yi Allah-wadai da hukuncin kisa da aka yanke wa Shaikh Husain Al-Ma’atouƙ, yana mai cewa wannan mataki hari ne kan asalin addini da haƙƙoƙin Musulmi, musamman ’yan Shi’a, da kuma ƙoƙari ne na raunana matsayi da martabar malaman Musulunci. Ya buƙaci gwamnatin Kuwait ta sake duba hukuncin cikin gaggawa domin hana aukuwar wannan mummunan lamari.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ga cikakken bayanin sanarwar da Ayatullah Alireza A’arafi, shugaban Makarantun Hauza na kasar Iran, ya fitar domin yin Allah-wadai da hukuncin zalunci da rashin adalci, wanda kotunan yankin suka yanke wa jama’a, matasa da manyan malaman addini, musamman hukuncin kisa da hukumomin Kuwait suka yanke wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Hujjatul Islam wal Muslimin Shaikh Husain Al-Ma’atouƙ, wanda ya shahara da jajircewa da hidimar al’ummar Kuwait.

Ga fassarar sanarwar kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai

Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa:

«مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَیٰ بَنِیٓ إِسْرَآئِیلَ أَنَّهُ مَنْ قَتَلَ نَفْسًا بِغَیْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِی الْأَرْضِ فَکَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِیعًا وَمَنْ أَحْیَاهَا فَکَأَنَّمَآ أَحْیَا النَّاسَ جَمِیعًا ۚ وَلَقَدْ جَآءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِالْبَیِّنَاتِ ثُمَّ إِنَّ کَثِیرًا مِنْهُمْ بَعْدَ ذَٰلِکَ فِی الْأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ»

Ma’ana: "Saboda haka, Mun wajabta wa Bani Isra’ila cewa duk wanda ya kashe wani rai ba tare da ya kashe wani ba, ko kuma ya yi ɓarna a doron ƙasa, to kamar ya kashe dukkan mutane ne. Kuma duk wanda ya ceci rai, to kamar ya ceci dukkan mutane ne. Lallai ManzanninMu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, amma duk da haka, da yawa daga cikinsu sun ci gaba da wuce gona da iri a doron ƙasa. (Suratul Ma’ida, aya ta 32)

A wannan lokaci da duniyar Musulunci ke fuskantar manyan ƙulle-ƙulle da maƙircin abokan gaban Musulunci, musamman gwamnatin Amurka mai nuna girman kai da kuma gwamnatin Isra’ila, labarin hukuncin zalunci da rashin tausayi da wasu kotunan yankin Gabas ta Tsakiya suka yanke wa jama’a, matasa da manyan malaman addini ya girgiza zukatan Musulmi.

Musamman hukuncin rashin adalci da hukumomin Kuwait suka yanke na kisa ga babban malamin addini, Hujjatul Islam wal Muslimin Shaikh Husain Al-Ma’atouƙ, wanda ya shahara da jajircewa da hidimar al’ummar Kuwait. Wannan lamari ya jefa al’ummar Musulmi cikin baƙin ciki da fushi, tare da tayar da hankula a tsakanin al’ummar Musulmi da cibiyoyin ilimi da Hauzazi a Iran da sauran sassan duniya.

Wannan mataki, wanda aka ɗauka ba tare da la’akari da ƙa’idojin shari’a, mutuntaka da matsayi mai girma na malaman addini ba, ya wuce batun hukuncin kotu kawai. A zahiri, hari ne kan asalin addini da haƙƙoƙin Musulmi da ’yan Shi’a, da kuma ƙoƙari bayyananne na raunana tasiri da martabar malaman Musulunci.

Ina mai dogaro da wannan aya mai girma da take cewa:

«أَنَّهُ مَنْ قَتَلَ نَفْسًا بِغَیْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِی الْأَرْضِ فَکَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِیعًا»

Ina kuma tunatar da cewa zaluntar muminai, waɗanda suke ’yan’uwa a ƙarƙashin tutar haɗin kai da kuma inuwar kalmar Allah Maɗaukaki, babban zunubi ne wanda ba ya cancantar a yi masa sassauci. Dole ne a kiyaye mutunci da martabar kowane ɗayansu.

Saboda haka, a madadin cibiyoyin karatun addini na Hauza, manyan maraji'an addini da kuma cibiyoyin da suke ƙarƙashinsu, ina yin Allah-wadai da wannan mummunan zalunci da hukuncin da aka yanke ba bisa ƙa’ida ba.

Ina kuma jaddada cewa wajibi ne gwamnatin Kuwait da jami’an da abin ya shafa su yi gaggawar sake duba wannan hukunci, bisa ƙa’idar ’yan’uwantakar Musulunci, tare da kiyaye muhimman haƙƙoƙin al’ummar Musulmin ƙasar, musamman ’yan Shi’a, da kuma girmama matsayi na ilimi da addini na fitattun mutane. Hakan zai taimaka wajen hana aukuwar wannan mummunan lamari da kuma kauce wa zaluntar adalci.

Haka kuma, yana da muhimmanci a fahimci cewa duk wani nuna wariya ga manyan malaman addini ba kawai yana tauye haƙƙoƙin mutum da na al’umma ba ne, har ma yana iya zama sanadin haifar da rarrabuwar kai da saɓani tsakanin ƙasashen Musulmi.

Wannan kuwa shi ne ainihin abin da abokan gaban Musulunci suke son cimmawa. Saboda haka, ya kamata dukkan gwamnatoci da al’ummomin Musulmi su guji duk wani mataki da zai haifar da irin wannan rarrabuwar kai.

Ina roƙon Allah Maɗaukaki Ya sa gwamnatocin Musulunci su farka daga barcin gafala, Ya kuma ba al’ummar Musulmi nasara a kan abokan gabansu na Amurka da Isra’ila.

Ayatullah Alireza A’arafi

Shugaban Makarantun Addini na Hauza.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha