A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Nasir Rafi'i ya bayyana hakan ne a wajen taron wa’azi na daren Talata a Haramin Sayyida Fatima Ma’asuma (SA), inda ya yi bayanin bambanci tsakanin ingancin aiki da karɓuwarsa a wajen Allah. Ya bayyana ikhlasi, imani, kiyaye haƙƙin wasu, neman halal da riƙo da wilayar Ahlul Baiti (AS) a matsayin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen karɓuwar ayyukan mutum a wajen Allah Maɗaukakin Sarki.
Malamin na Hauza da jami’a ya yi nuni da ayoyin Alƙur’ani da suka yi magana kan ƙarshen rayuwar mutane, inda ya bayyana cewa wani lokaci mutum kan aikata aiki wanda ya cika sharuɗɗan ingancinsa a zahiri da kuma ta fuskar shari’a, amma saboda rashin wasu sharuɗɗa, Allah ba Ya karɓarsa. Saboda haka, mumini bai kamata ya tsaya kawai ga gudanar da ibada da ayyukan alheri ba, dole ne ya kuma yi ƙoƙarin samar da sharuɗɗan karɓuwarsu.
Ya kuma yi nuni da addu’ar Annabi Ibrahim (AS) bayan gina ɗakin Ka’aba, inda ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (AS) da Annabi Isma’il (AS) sun ɗaga harsashin ginin Ɗakin Allah, amma bayan wannan babban aiki, sai suka roƙi Allah Ya karɓa daga gare su, suna cewa:
«رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّکَ أَنْتَ السَّمِیعُ الْعَلِیمُ»
“Ya Ubangijinmu! Ka karɓa daga gare mu, lallai Kai ne Mai ji, Masani.”
Ya bayyana cewa wannan addu’a tana nuna cewa hatta waɗanda suka gudanar da manyan ayyukan ibada ya kamata su kasance cikin damuwa kan ko Allah Ya karɓi ayyukansu, tare da roƙonsa Ya karɓa.
Ikhlasi yana taka muhimmiyar rawa wajen karɓuwar ayyukan alheri
Hujjatul Islam wal Muslimin Rafi'i ya bayyana cewa ikhlasi yana da muhimmiyar rawa wajen ƙayyade darajar ayyukan mutum. Ya kawo labarin Habila da Ƙabila, inda ya ce dukansu sun miƙa wani abu domin neman kusanci ga Allah, amma Alƙur’ani ya bayyana karɓuwar aikin ɗayansu.
Ya ce bambancin bai kasance a zahirin aikin ba, a’a, tsoron Allah da niyyar mai aikatawa ne suke da muhimmanci wajen karɓuwarsa. Idan mutum ya yi aikin alheri domin ya nuna kansa ko ya yi gogayya da wasu, zai iya rasa amfanin ruhaniya da ya kamata ya samu daga wannan aiki.
Ya kuma kawo misalin Masallacin Dirar, inda ya bayyana cewa gina masallaci abu ne mai daraja, amma idan aka gina shi da nufin haddasa rarrabuwar kai da cutar da al’ummar Musulmi, zahirin kasancewarsa masallaci ba zai iya halatta mummunar manufar da aka gina shi dominta ba.
Saboda haka, ya jaddada cewa, baya ga siffa da zahirin ayyuka, niyya da manufar wanda ya aikata su ma suna da matuƙar muhimmanci.
Imani da sallah: Muhimman sharuɗɗan karɓuwar ayyuka
Malamin ya yi nuni da wasu ayoyi daga Suratul Ali Imran da suka yi magana kan mutanen da suka yi imani, sannan suka koma ga kafirci. Ya bayyana cewa ƙarshen rayuwar mutum da tsayuwarsa a kan imani suna da muhimmanci sosai.
Ya ce, ya kamata mutum ya riƙa roƙon Allah Ya kiyaye zuciyarsa daga karkacewa bayan shiryar da shi, kuma Ya ba shi ikon ci gaba da tafarkin imani har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Ya lissafa imani a matsayin ɗaya daga cikin muhimman sharuɗɗan karɓuwar ayyuka, yana mai cewa ayyukan alheri da hidimomin jinƙai suna da daraja, amma a mahangar addini, imani da kuma fuskantar Allah a cikin ayyuka suna da tasiri wajen samun ladan Lahira.
Ya kuma jaddada muhimmancin bambance tambaya ko samun shakku daga ɗaukar matsaya da gangan domin yaƙar addini da yaɗa farfaganda a kansa. Ya bayyana cewa ba kowace tambaya ko shakku ba ce take nufin mutum ya fita daga addini.
Da yake magana kan muhimmancin sallah, Hujjatul Islam wal Muslimin Rafi'i ya ce sallah tana da matsayi na musamman a cikin ibadodi, kuma ruwayoyin Musulunci sun jaddada alaƙarta da karɓuwar sauran ayyuka.
Ya bayyana cewa bai kamata mutum ya wadatu da aikata wasu ayyukan alheri, halartar tarukan addini ko taimaka wa mabukata ba, sannan ya yi sakaci da sallah. Ya yi misali da cewa kamar yadda ake buƙatar takardun da suka wajaba kafin tafiya, haka nan a tafarkin bautar Allah, dole ne a kula da manyan wajibai.
Neman halal da kiyaye haƙƙin mutane
Hujjatul Islam wal Muslimin Rafi'i ya sake jaddada cewa neman kuɗin halal yana daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen karɓuwar ayyukan ibada. Ya ce aikin alheri dole ne a gudanar da shi da dukiyar halal, domin ba zai yiwu mutum ya yi amfani da dukiyar da ya samu ta hanyar haram ba, sannan ya sa ran samun lada ta ruhaniya daga gare ta.
Ya bayyana cewa kiyaye haƙƙin mutane, riƙon amana da sauke nauyin aiki yadda ya kamata duk suna cikin wannan ƙa’ida.
Malamin ya kuma yi nuni da muhimmancin biyan haƙƙoƙin kuɗi da suka wajaba, ciki har da Khumusi da Zakka. Ya jaddada cewa wajibi ne mutum ya san nauyin da ke kansa na kuɗi, sannan ya biya haƙƙoƙin da suka rataya a kansa.
Haka kuma, ya bayyana cewa yin sakaci da aiki a lokutan ofis, rubuta bayanan ƙarya game da lokacin da mutum ya halarci wajen aiki, da kuma amfani da kayan gwamnati ko na jama’a ta hanyar da ba ta dace ba, duk ba su dace da ɗaukar nauyi da kiyaye haƙƙin wasu ba.
Ɗabi’a, iyali da wilayar Ahlul Baiti (AS)
Hujjatul Islam wal Muslimin Rafii ya bayyana kiyaye kyawawan ɗabi’u a matsayin wani muhimmin abu da ke taimakawa wajen karɓuwar ayyukan ibada. Ya ce gulma, mummunan zato da cutar da wasu na iya shafar ladan da mutum zai samu daga ayyukansa.
Ya jaddada cewa mumini ya kamata, tare da gudanar da ibada da ayyukan alheri, ya kula da harshensa, halayensa da kuma haƙƙin mutanen da ke kewaye da shi.
Da yake magana kan matsayin iyali a koyarwar addini, ya bayyana cewa mutunta juna, kiyaye haƙƙin ma’aurata da ’ya’ya, da kuma sauke nauyin da ke kan mutum a cikin iyalinsa suna daga cikin muhimman batutuwan da ruwayoyin Musulunci suka yi magana a kansu.
Sai dai ya bayyana cewa dole ne a fahimci waɗannan haƙƙoƙi bisa tsarin hukunce-hukuncen Shari’a, domin babu wanda yake da ikon tilasta wa wani aikata zunubi ko barin wani wajibi.
A ƙarshen jawabinsa, mai wa’azin Haramin Sayyida Fatima Ma’asuma (SA) ya bayyana wilayar Ahlul Baiti (AS) da sanin Imamuz Zaman (AF) a matsayin muhimman ginshiƙan aƙida a tafarkin bautar Allah.
Ya yi nuni da ruwayoyin da suka yi magana kan sanin Imam Zaman (AF), inda ya jaddada muhimmancin ƙarfafa alaƙar aƙida da aiki da iyalan Manzon Allah (SAWA).
A daidai lokacin da ake dab da tunawa da ranar shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA), Hujjatul Islam wal Muslimin Rafi'i ya jaddada muhimmancin cin gajiyar damammakin ruhaniya da waɗannan ranaku suke bayarwa.
Ya bayyana cewa aikin ƙwarai zai iya kusantar da mutum ga Allah ne idan, baya ga ingancinsa na zahiri, ya kasance tare da imani, ikhlasi, kiyaye haƙƙin mutane da kuma riƙo da koyarwar Ahlul Baiti (AS).
Ra'ayinka