Litinin 12 Oktoba 2026 - 21:23
Sahifar Rayuwa | Addu’ar da Take Kusantar da Matasa Zuwa Ga Bautar Allah

Hauza/ Dan adam yana fuskantar hanyoyi da zaɓuka daban-daban a rayuwarsa, amma wace hanya ce za ta fi taimaka masa a kan tafarkin bautar Allah?

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Imam Sajjad (A.S) yana roƙon Allah Madaukakin Sarki da wannan addu’a:

اللَّهُمَّ ... اسْتَعْمِلْنِی بِمَا تَسْأَلُنِی غَداً عَنْهُ 

"Ya Allah! Ka yi amfani da ni a cikin ayyukan da za Ka tambaye ni a kansu gobe (a ranar lahira)."¹

Sharhi:

Irin wannan addu’ar ta zo daga Sayyida Zahra (S.A) da kuma Imam Sadiƙ (A.S). Wannan addu’ar tana iya zama tamkar fitila mai haskaka hanya ga matasan da suka damu da addini, musamman ma waɗanda suke farkon tafarkin bautar Allah.

Dan adam yana fuskantar hanyoyi da zaɓuka daban-daban a rayuwarsa, amma wace hanya ce za ta fi taimaka masa a kan tafarkin bautar Allah?

Ta hanyar wannan addu’a, muna roƙon Allah ne cewa: "Ya Allah! Ka sanya ƙaunata, baiwata, ƙarfina, da damammakin da suke gabana, dukansu a kan hanyar da take gamsar da Kai." Kuma tabbas, don cimma wannan muradi, dole ne mutum ya bayar da dukkanin ƙarfinsa. Don haka ne ma Amirul Muminin Ali (A.S) ya roƙi Allah:

یَا رَبِّ یَا رَبِّ یَا رَبِّ، قَوِّ عَلی خِدْمَتِکَ جَوارِحِی، وَاشْدُدْ عَلَی الْعَزِیمَةِ جَوانِحِی.

"Ya Ubangijina, Ya Ubangijina, Ya Ubangijina! Ka ƙarfafa gabban jikina don bautar Ka, kuma ka ƙarfafa zuciyata a kan manufata."²

Idan za mu yi fassarar zamani ta kalamin Amirul Muminina (A.S), za mu iya cewa: "Ya Allah! Ka sanya dukkanin 'hardware' (gaɓɓan jiki) da 'software' (zuciya da tunani) na rayuwata a kan hanyar bautar Ka."

Kuma wataƙila abin da zai iya tattara dukkan waɗannan addu’o’in shi ne kalaman Manzon Allah (S.A.W.A) da ya ce:

اَللَّهُمَّ لاَ تَکِلْنِی إِلَی نَفْسِی طَرْفَةَ عَیْنٍ أَبَداً.

"Ya Allah! Kada Ka bar ni ga kaina ko dai da ƙyafta ido ɗaya har abada."³

Manazarta:

1. Sahifa Sajjadiyya, Addu’a ta 20 (Addu’ar Makarimul Akhlaq).

2. Addu’ar Kumayl.

3. Al-Manaqib, Juzu’i na 1, shafi na 57.

An shirya a sashin ilimi da al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha