Litinin 5 Oktoba 2026 - 19:16
Yunƙurin Gwamnatin Bahrain na Kawar da Asalin Addini Daga Al’ummar Shi’a

Hauza/ Ministan harkokin cikin gida na kasar Bahrain ya yi barazanar tsananta matakan da yake dauka kan ‘yan Shi’ar kasar, tare da kara rikitar da fayil din malaman addini da ke tsare a gidajen yari.

Kamar yadda rukunin fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito, bisa labarin da shafin "Mir'at al-Bahrain" ya fitar; Rashid bin Abdullah, Ministan tsare-tsare da gidajen yari (wanda ake kira Ministan harkokin cikin gida), ya ƙara nuna kudurin ƙara tsananta matakan da yake dauka kan malaman da aka tura gidan yari bisa zarge-zarge da zalunci. Uzurin da yake amfani da shi shi ne, "yaki da Wilayatul Faƙih." A sabon jawabin da ya yi, Ministan ya ce: "Wakilan Waliyyul Faƙih sun yi kokarin mamaye al’ummar Shi’a a Bahrain da kuma kutsawa cikin hukumomin gwamnati da majalisar dokoki."

Maimakon ya nemi hanyar fita daga rikicin da ake ciki ko magance matsalolin da ke tattare da yanayin kasar Bahrain (wanda ya samo asali tun lokacin yakin da ake yi da Iran da kuma goyon bayan da gwamnatin Bahrain ke ba wa hakan), Rashid bin Abdullah ya fito da manufofi masu raba kan al’umma, wadanda kamar gwamnati na shirin ci gaba da su har zuwa karshen zango. Yakin da ake ci gaba da yi ba kakkautawa kan malaman da ke tsare alama ce ta rashin son sulhu; domin gwamnati na nacewa kan matakan da take dauka a kansu, kuma duk da dukkan sukar da ake yi wajen kin amincewa da kowane irin hujja ta doka ko tsaro kan wadannan kamun, gwamnati na ci gaba da manufofinta na zalunci.

Wasu suna ganin cewa furucin Rashid bin Abdullah na kwanan nan alama ce mara kyau matuka, kuma suna hasashen cewa fayil din malaman da ke tsare na iya fuskantar wani sauyi mai hadari, ganin yadda ake tunanin za a iya yanke musu hukunci mai tsanani. Maganar yanzu a fili take, wani yaki ne na ƙiyayya da ake gudanarwa kan akidun addini na asali a kasar. Laifantar da ayyukan addini na Shi’a ya zama babban abin damuwa na ma’aikatar; ma’aikatar da ake yanke shawarwari a cikinta karkashin jagorancin mai mulkin kasar.

Ministan tsare-tsare da gidajen yari yana son ya aike da sako na koda yaushe wanda gwamnati ta kasa sauya salonsa: wato tsoratar da al’umma da razana su domin nisantar da su daga imaninsu da aƙidunsu, har ma da yunkurin nesantar da su daga aƙidar [Wilayatul Faƙih], ta yadda ba za su sake jin sunan "Wilayatul Faƙih" a wani taro, darasin addini, masallaci, ko majalisar jaje ba.

Idan muka ji kalaman Rashid bin Abdullah, babu abin da ke zuwa mana a rai sai misalan fitina, musgunawa zamantakewar al’umma, da rusa bambancin ra’ayi tsakanin kungiyoyin jama’a daban-daban. Ana kokarin kafa wani yanayi na ware kai daga addinin Shi’a domin a samar da wadanda gwamnati za ta iya sarrafa aƙidarsu da kudurinsu yadda take so; amma jira! Abin da ya faru bayan wannan matakin tsanantawa da kamun malaman, yana nuna yawan juriyar mabiya Shi’ar da kuma yadda ba su mika wuya ba; wadanda suke ganin ayyukan malamai wani jan layi ne wanda ba za su taba yin sulhu a kansa ba, duk barazanar da za ta iya zuwa; bisa ka’idar cewa: "Idan har  za a tsare dukanmu, to a tsare; ba za mu yi sulhu kan addininmu da aƙidarmu ba."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha