A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a yayin darasin Akhlaƙ na mako-mako da ya gabatar a Masallacin A’azam da ke Qum, Ayatullah Jawadi Amuli ya bayyana cewa mutumin mai tauhidi ba shi ne wanda ya yarda da kaɗaitakar Allah kawai ba, a’a, tasirin tauhidi ya kamata ya bayyana a cikin dukkan ayyuka da mu’amalolin rayuwarsa.
Ya ce mutum ya kamata ya ga dukkan al’amuran rayuwarsa ƙarƙashin ikon Allah, tare da rayuwa bisa ma’anar “La hawla wa la quwwata illa billah”, wato babu dabara ko ƙarfi sai daga Allah.
Kada ilimi ya zama jahilci
Ayatullah Jawadi Amuli ya kuma jaddada muhimmancin aiki da ilimi, musamman ga ’yan Hauza, yana mai cewa ilimi babban jari ne da bai kamata a ɓata ba.
Ya yi nuni da maganar Imam Ali (AS) cewa:
إِذَا عَلِمْتُمْ فَاعْمَلُوا
“Idan kun sani, ku yi aiki.” Ya bayyana cewa ilimin da mutum bai yi aiki da shi ba yana rasa amfaninsa, don haka ya kamata malami ya kasance abin koyi ta hanyar ayyukansa, maganganunsa da rubuce-rubucensa.
Kyakkyawar mu’amala da mabuƙata
A bangaren zamantakewa, Ayatullah Jawadi Amuli ya yi kira da a kyautata mu’amala da mabuƙata. Ya ce idan mutum yana da ikon taimaka wa wanda ya zo neman taimako, kada ya ƙi; idan kuma ba shi da ikon taimakawa, ya sallame shi cikin girmamawa tare da nuna masa inda zai iya samun mafita.
Ya bayyana cewa wannan hali yana daga cikin tasirin kallon rayuwa bisa tauhidi, domin mai buƙata yana iya kasancewa “ɗan saƙon Allah” da ya zo neman taimako.
Kada ku yarda da zalunci
A wani bangare na jawabinsa, Ayatullah Jawadi Amuli ya jaddada cewa musulmi ya kamata ya kare mutuncinsa kuma kada ya zama mai yarda da zalunci.
Ya nakalto daga Imam Ali (AS) cewa:
لَا یَمْنَعُ الضَّیْمَ الذَّلِیلُ
“Wulakantacce ne wanda ba ya iya hana zalunci.”
Ya kuma bayyana cewa rayuwa cikin jarumta ba ta nufin zaluntar wasu, sai dai kare mutunci, yin rayuwa cikin hikima da ƙarfin hali, da kuma tsayawa a kan gaskiya.
Arziki yana wajen Allah
Ayatullah Jawadi Amuli ya kuma tunatar da al’umma cewa arzikin da yake wajen Allah ya fi abin da yake hannun mutum tabbaci da dorewa. Inda ya kafa hujja da ayar:
مَا عِندَکُمْ یَنفَدُ وَمَا عِندَ اللَّهِ بَاقٍ
Don haka, ya yi kira da kada a yanke ƙauna a lokacin ƙunci, sai dai a yi haƙuri tare da dogaro ga Allah.
Maryam (AS) abin koyi ga muminai
A ƙarshen jawabinsa, Ayatullah Jawadi Amuli ya kawo misalin Sayyida Maryam (AS), yana mai cewa Alƙur’ani ya gabatar da ita a matsayin abin koyi ga waɗanda suka yi imani, ba mata kaɗai ba.
Ya bayyana cewa wannan yana nuna cewa mace mai imani da tsoron Allah za ta iya zama abin koyi ga daukacin al’umma.
A ƙarshe, Ayatullah Jawadi Amuli ya yi addu’a ga waɗanda suka rasu, shahidai da dukkan mahalarta taron, yana roƙon Allah Ya azurta al’umma da mutunci, ɗaukaka, girma da kyakkyawar rayuwa a duniya da lahira.
Ra'ayinka