Jummaʼa 25 Satumba 2026 - 18:13
Hankali Shi Ne Muhimmin Darajar Dan Adam da Tushen Fahimtar Ma’arifar Ubangiji

Hauza/ Mai girma Ayatullah Ja’afar Subhani ya bayyana cewa hankali da basira su ne mafi muhimmiyar daraja da Allah Ya bai wa dan Adam a kan sauran halittu, yana mai jaddada cewa daukakar kowane ilimi tana da alaka da girman abin da ilimin yake nazari a kansa. Ya kuma bayyana cewa amfani da hankali da falsafa ya zama dole domin fahimtar ayoyin Alkur’ani da ma’arifar Musulunci yadda ya kamata.

A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Tabriz, Ayatullahil Uzma Ja’afar Subhani ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon bidiyo da ya aika ranar Alhamis 2 ga Mehr (24 ga Satumba), yayin taron majalisar shugabannin Majalisar Koli ta Hikimar Musulunci karo na uku, wanda aka gudanar a matakin kasa a birnin Tabriz.

Ayatullah Subhani ya bayyana “hankali da basira” a matsayin mafi muhimmiyar daraja da dan Adam yake da ita a kan sauran halittu, yana cewa: “Idan aka kwace hankali da basira daga dan Adam, babban bambancin da ke tsakaninsa da sauran halittu masu rai zai gushe.”

Ya bayyana cewa girmama dan Adam da Alkur’ani Mai Girma ya yi, ya ta’allaka ne da wadannan siffofin na dan Adam da kuma yadda yake da hankali da basira. Ya ce Allah Ta’ala, ta hanyar bai wa dan Adam wannan baiwa, Ya sanya masa matsayi na musamman.

Ya kara da cewa, abin da ake nufi da koyar da sunaye (asma'a) ba wai koyar da kalmomi da sunaye kawai ba ne, face cewa ta hanyar wannan koyarwa ne dan Adam ya samu damar sanin hakikanin abubuwa, sannan ya kai ga wani matsayi na musamman ta fuskar ilimi da sanin hakika.

Wannan babban malamin addini ya yi bayani kan matsayin Hikimar Ubangiji, inda ya ce falsafar Ubangiji ba tayi nazarin wani bangare karami na samuwa ba, a maimakon haka, abin da take nazari a kansa shi ne “samuwar halittu”, kuma dukkan halittu, wadanda samuwarsu mai yiwuwa ce (mumkinul wujub) da kuma wadanda samuwarsu wajibi ce (wajibul wujub), suna cikin fagen wannan bincike.

Ya ce saboda haka, daukakar kowane ilimi tana dogara ne da daukakar abin da yake nazari a kansa. Duk lokacin da abin da wani ilimi yake nazari a kansa ya kasance mai fadi da muhimmanci, matsayin wannan ilimi ma zai kasance mafi girma.

Ya soki ra’ayin da ke hana hankali shiga cikin bahasin falsafa da ilimin Kalam, yana mai cewa idan aka cire hankali daga wadannan fannoni, za a fuskanci manyan tambayoyi wajen fassara ayoyin Alkur’ani da dama da suke magana kan siffofi da ayyukan Allah. Saboda haka, ya kamata a fassara irin wadannan ayoyi ta hanyar amfani da ilimi, hankali da falsafa.

Ya ci gaba da cewa a wasu ayoyin Alkur’ani an yi magana game da kusancin Allah da dan Adam, alhali Allah ba jiki ba ne kuma ba Shi da wani wuri da Ya kebanta da shi. Saboda haka, irin wadannan kalamai ba za a iya daukarsu da ma’anar cewa Allah Ya shiga cikin wani abu ko kuma yana da kasancewar jiki ba. Don haka, domin fahimtar wadannan ayoyi yadda ya kamata, akwai bukatar amfani da bahasin hankali da ilimin Kalam.

Ayatullah Subhani, yayin da yake ishara da Nahjul Balagha, ya ce huduba ta farko ta Nahjul Balagha cike take da bahasosin falsafa da ilimin Kalam game da sanin Allah da siffofinsa. A cikin wadannan bahasosi, ana tabbatar da siffofi kamar ilimi da iko ga Allah, amma wadannan siffofi ba sa nufin cewa akwai haduwa ko sassa daban-daban a cikin zatinsa. Bayyana wannan batu yana bukatar zurfafa bincike na falsafa da ilimin Kalam.

Ya jaddada cewa daya daga cikin abubuwan alfahari na Shi’a da malaman Shi’a tun daga zamanin baya har zuwa yau shi ne yadda suka mai da hankali kan bahasosin hankali, falsafa da ilimin Kalam. Ya ce bai kamata a takaita wadannan bahasosi kawai cikin tsarin wata makarantar falsafa guda daya ba, a maimakon haka, ya kamata a yi bincikensu ta hanyar amfani da damar hankali da kuma ma’arifar Musulunci.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha