Laraba 23 Satumba 2026 - 22:51
Me Ya Sa Wilayatul Faƙih Ta Zama Buƙata Ce ta Hankali? (4)

Hauza/ Kafa gwamnati a kowace al’umma wata buƙata ce ta hankali da ɗabi’ar ɗan Adam wadda ba za a iya guje mata ba. Ɗan Adam “madaniyyun biɗɗabi’i” ne, wato a dabi’ance yana buƙatar rayuwa tare da jama’a. Ba zai iya ci gaba da rayuwarsa ba sai a ƙarƙashin tsayayyar rayuwar zamantakewa.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | A ci gaba da kawo fassarar muƙalar Me Ya Sa Wilayatul Faƙih Ta Zama Buƙata Ce ta Hankali, yau zamu kawo muku sashe na huɗu na wannan muƙalar.

Ambaton Mataimakan Imam Zaman (A.F) Guda Uku 

Hujjar hankali mai tattare da dukkan dalilai ta kai mu ga wannan sakamako:

“Ba zai yiwu a aiwatar da hukunce-hukuncen Musulunci ba tare da Waliyyul Faƙih ba.”

A tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mataimakan Imam Zaman (A.F) guda uku sun tabbatar da wannan gaskiya:

Imam Khumaini (Q): Ta hanyar kafa gwamnatin Musulunci, ya fitar da aiwatar da hukunce-hukuncen zamantakewa na Musulunci daga matsayin dakatarwa, kuma ya nuna cewa Faƙihi zai iya zama cikakken mai aiwatar da hukunce-hukuncen Allah.

Shahid Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Q): Ta hanyar ci gaba da wannan tafiya, ya aiwatar da hukunce-hukuncen iyaka, kisasi da kare martabar tsarin Musulunci a cikin yanayi mafi wahala, tare da tabbatar da cewa Waliyyul Faƙih shi ne mai tabbatar da aiwatar da hukunce-hukuncen Allah.

Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i (DZ): A yau, ta hanyar “gudanarwa irin ta jihadi” da kuma “bayar da labarin ƙarfi”, yana tabbatar da yiwuwar aiwatar da hukunce-hukuncen zamantakewa na Musulunci a zamanin yaƙin haɗaka, tare da nuna cewa Wilayatul Faƙih ita ce hanya ɗaya tilo ta aiwatar da ingantaccen Musulunci a lokacin gaiba.

Sashe na Biyar: Cikakkiyar Hujjar Hankali Don Tabbatar da Wilayatul Faƙih (Tare da Muhimman Tambayoyi)

Me Ya Sa Tabbatar da Wilayatul Faƙih Ta Hanyar Hankali Yake Da Muhimmanci?

Domin amsa shubuhohi da gamsar da mutane, muna buƙatar bayyananniyar hujjar hankali wadda ba za a iya musanta ta ba.

Hujjar hankali, ba kamar hujjojin ruwayoyi ba, ana iya fahimtar ta kuma ta samu karɓuwa ga kowa, har ma ga waɗanda ba su yarda da wasu ruwayoyi na musamman ba.

A wannan sashe, za a gabatar da cikakkiyar hujjar hankali don tabbatar da Wilayatul Faƙih. Wannan hujja za ta fara ne daga abubuwan da hankali ya riga ya fahimta, sannan ta kai ga sakamako tabbatacce.

Tambaya

Shin muna buƙatar hujjar ruwaya domin tabbatar da wata buƙata ta zamantakewa, ko kuwa hankalinmu ma zai iya kai mu ga fahimtar hakan?

Amsa

Hankali yana iya fahimtar wannan buƙata yadda ya kamata. Wannan shi ne ƙarfin hujjar hankali.

Gabatarwa ta Farko: Buƙatar Samuwar Gwamnati Ƙa’ida Ce Bayyananniya ta Hankali

Kafa gwamnati a kowace al’umma wata buƙata ce ta hankali da ɗabi’ar ɗan Adam wadda ba za a iya guje mata ba. Ɗan Adam “madaniyyun biɗɗabi’i” ne, wato a dabi’ance yana buƙatar rayuwa tare da jama’a. Ba zai iya ci gaba da rayuwarsa ba sai a ƙarƙashin tsayayyar rayuwar zamantakewa.

Tambaya

Shin al’ummar da babu wani shugaba a cikinta za ta iya samun zaman lafiya?

Amsar a bayyane take: A’a. Domin a irin wannan al’umma, rikici da rashin tsari za su jefa zaman tare da hakkokin mutane cikin haɗari. Wannan ƙa’ida dukkan mazhabobi da tsarin siyasa sun amince da ita.

Hatta Ibn Abil-Hadid, wanda yana daga cikin malaman Ahlus-Sunnah, ya ce: “Malaman ilimin kalam sun ɗauki Imama da shugabanci a matsayin wajibi.”

Imam Ali (A.S) ma, yayin da yake amsa wa Khawarij waɗanda suka ɗaga taken “La hukma illa lillah”, ya ce:

«لَا بُدَّ لِلنَّاسِ مِنْ أَمِیرٍ بَرٍّ أَوْ فَاجِرٍ»

Ma’ana: “Dole ne mutane su kasance da shugaba, ko nagari ne ko fajiri.”(1)

Wannan magana tana nuna cewa hatta samun shugaba fajiri ya fi rashin shugabanci, domin rashin shugabanci yana haifar da rikici da rashin tsari.

Tambaya

Idan Musulunci yana iya jure wa shugaba fajiri, to me ya sa muke buƙatar Faƙihi mai adalci?

Amsa

Jure wa shugaba fajiri ba yana nufin amincewa da shi ba ne. Ana yin hakan ne saboda tilas. Amma Musulunci yana tsara shugaba mai adalci da masaniya a matsayin tsarin da ake so. Wannan kuwa shi ne Faƙihin da ya cika sharuɗɗa.

Gabatarwa ta Biyu: Musulunci Addinin Ɗabi'a da Hankali Ne

An saukar da Musulunci bisa buƙatu da sha’awoyin ɗan Adam na dabi’a, waɗanda suke da ma’ana kuma suka dace da hankali.

Allah Maɗaukaki Ya ce:

«فَأَقِمْ وَجْهَکَ لِلدِّینِ حَنِیفًا فِطْرَتَ اللَّهِ الَّتِی فَطَرَ النَّاسَ عَلَیْهَا»

“Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini kana mai karkata zuwa gaskiya, kana bin ɗabi’ar Allah wadda Ya halicci mutane a kanta.”(2)

Ma’ana: Musulunci addinin dabi’a ne, kuma ya dace da asalin halittar ɗan Adam.

A Musulunci, an fahimci buƙatar shugabanci ta hankali da dabi’a yadda ya kamata. An amince da shugabanci a matsayin ɗaya daga cikin manyan buƙatun al’ummar ɗan Adam, tare da sanya wasu sharuɗɗa da siffofi na musamman a gare shi.

Tambaya

Shin addinin da yake ikirarin cewa shi ne addinin dabi’a zai iya yin watsi da buƙatar ɗan Adam ta dabi’a na samun shugabanci?

Amsa

Tabbas ba zai yiwu ba. Wannan kansa hujja ce ta hankali a kan wajibcin shugabanci a Musulunci.

Gabatarwa ta Uku: Buƙatar Shugabanci A Ra’ayin Malaman Shi’a da Ahlus-Sunnah

Malaman Shi’a da Ahlus-Sunnah duk sun yi imani da wajibcin samuwar shugabanci.

Kamar yadda aka ambata, Ibn Abil-Hadid, malamin Ahlus-Sunnah, ya bayyana cewa: “Imama da shugabanci wajibi ne.”

Imam Ali (A.S) ma, a cikin hudubar Nahjul Balaga, ya bayyana wannan buƙata a matsayin ƙa’ida tabbatacciya.

Tambaya

Idan malaman dukkan mazhabobi sun yi ittifaki a kan wajibcin shugabanci, to a ina ne bambancin yake?

Bambancin yana cikin tambayar cewa: “Wa ya kamata ya zama shugaba?”

Shi tsarin Shi’a, ta hanyar hujjar hankali da ruwayoyi, ya kai ga zaɓar Faƙihin da ya cika sharuɗɗa.

Gabatarwa ta Huɗu: A Lokacin Gaiba, Wa Ke Da Alhakin Kafa Gwamnati?

Yanzu da aka tabbatar da wajibcin kafa gwamnati, tambaya mafi muhimmanci ita ce: “A lokacin gaibar Imam Zaman (A.F), wa ke da alhakin kafa gwamnati?”

Bisa ka’idar Wilayatul Faƙih, kafa gwamnati yana kan malaman Fikihu.

Hujjar hankali a kan wannan magana ita ce: “Aiwatar da dokar Allah na iya kasancewa ne ta hannun mutumin da yake da siffofi biyu: sanin doka, wato Fikihu, da kuma adalci.”

Tambaya

Shin za a iya miƙa shugabanci ga mutumin da bai san dokokin Allah ba, kuma ba shi da adalci?

Amsar a bayyane take: A’a. Saboda haka, dole ne a nemi mutumin da yake da waɗannan siffofi guda biyu.

Gabatarwa ta Biyar: Siffofin Shugaban da Ya Cancanta a Lokacin Gaiba

Mutumin da zai iya ɗaukar nauyin shugabanci a lokacin gaiba dole ne ya kasance yana da muhimman siffofi guda uku.

Siffa ta Farko: Sanin Doka

Wato cikakken ilimi game da dokokin Musulunci da ikon fitar da hukunce-hukuncen addini daga ingantattun tushe, kamar Alƙur’ani da Sunna.

Ana kiran irin wannan mutum da suna Faƙih.

Siffa ta Biyu: Adalci

Wato samun cancantar ruhaniya da ɗabi’a, ta yadda ba zai kasance ƙarƙashin tasirin son zuciya, barazana ko jan hankali da dukiya ba.

Siffa ta Uku: Ƙwarewa Wajen Gudanar da Al’umma

Wato iya fahimtar al’amuran siyasa da zamantakewa, sanin batutuwan duniya, ƙarfin hali wajen fuskantar maƙiya da kuma iya tantance abubuwan da suka fi muhimmanci.

Tambaya

Shin waɗannan siffofi guda uku sun fi kasancewa ne a tare da Faƙihin da ya cika sharuɗɗa, ko kuma a tare da wasu mutane?

Amsar a bayyane take: Faƙihi mai adalci da ƙwarewa shi ne ya fi haɗa waɗannan siffofi, domin yana da ilimin doka, adalci da ƙwarewar gudanarwa.

Za mu ci gaba...

Madogara 

1. Nahjul Balaga, huɗuba ta 40

2. Suratul Rum: 30

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha