Talata 22 Satumba 2026 - 21:30
Ku Kare Tushen Ƙasarku, Harshen Uwa da Tsarkakakkiyar Tutar Jamhuriyar Musulunci

Hauza/ Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i, a cikin wani saƙo da ya fitar yayin fara sabuwar shekarar karatu ta makarantu da jami’o’i, ya yi gaisuwa da girmamawa ga ɗalibai, malamai da farfesoshi da suka yi shahada a yaƙin da aka tilasta wa Iran a baya-bayan nan. Ya bayyana sake buɗe makarantu da jami’o’i a matsayin alamar farfaɗowar kuzari, fata da saurin tafiyar al’umma zuwa makoma mai haske. Ya kuma shawarci ɗalibai da su tanadi kansu da “ilimi da taƙawa, sani da ƙwarewa”, yana mai jaddada cewa su ɗauki makaranta da jami’a a matsayin gidansu na biyu, su kare mutuncinsu, su kuma mayar da su cibiyar ci gaban ƙasarsu.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamene'i (DZ) ya fitar da wani saƙo domin fara sabuwar shekarar karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ga fassarar cikakken saƙon na Jagoran Jamhuriyar Musulunci:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

“Allah zai ɗaukaka waɗanda suka yi imani daga cikinku da waɗanda aka ba su ilimi zuwa darajoji.”

Farkon sabuwar shekarar karatu da sake buɗe gidajen ilimi da tarbiyya a makarantu da jami’o’i, alama ce ta farfaɗowar kuzari, fata da kuma saurin tafiyar al’umma zuwa makoma mai haske da ɗaukaka. Makomar da za ta tabbata ne ta hannun ’ya’yan Iran ababen ƙauna da waɗanda suka samu tarbiyya a makarantar Musulunci da Juyin Musulunci. Su ne wannan ƙarni da Imam Khumaini da Ayatullah Khamene’i, Allah Ya ɗaukaka matsayinsu, suka sha bayyana fatansu a kansu.

Yanzu da aka buɗe ƙofar sabuwar shekarar karatu ga ɗimbin ɗalibai, masu neman ilimi da hikima za su fara wani sabon mataki na samun ilimi, sani da ƙwarewa, tare da fatan samun nasara daga Allah. Ya dace mu tuna da ɗaliban da suka yi shahada a yaƙin da aka tilasta wa Iran a baya-bayan nan, tare da iyaye mata da ubanni da suka rasa ’ya’yansu.

A wannan shekara, kwanakin farko na sabuwar shekarar karatu za su sake tunasar da mu baƙin cikin rabuwa da ’ya’yanmu da suka tafi. A makarantu da jami’o’i za a ji gibin wasu daga cikin ɗalibai, malamai da farfesoshi da suka yi shahada. Wannan baƙin ciki zai kuma tunasar da mu game da yaƙin da ake yi tsakanin alheri da sharri, da kuma tsakanin gaskiya da ƙarya.

Nauyin da ke kan ɗalibai a yau shi ne ƙoƙarin tanadar kansu da ilimi da taƙawa, fata da kyawawan ɗabi’u, sani da ƙwarewa, tare da kawar da labulen jahilci da duhu. Hakan zai ba su damar karya iyakokin ilimi da kaiwa ga kololuwar ci gaban kimiyya, domin su sauke nauyin tarihinsu na ɗaukaka Iran ta Musulunci.

Wannan muhimmin aiki yana faruwa ne a wurin da ya kamata su ɗauka a matsayin gidansu na biyu. Saboda haka, ina gaya wa waɗannan ƙaunatattun ɗalibai cewa ya wajaba su riƙa kare mutunci da tsaron makarantu da jami’o’insu yadda ya kamata. Su kuma ƙara inganta matakin sani da fahimtarsu, tare da kyautata ɗabi’u da halayensu, domin su mayar da makaranta da jami’a cibiyar ci gaban ƙasarsu.

Ku yi amfani da shekarun da kuke yi a wannan matsugunin ilimi, tarbiyya, annashuwa da fata wajen ƙara inganta kanku. Ku inganta dangantakarku da Mahalicci Mai girma, ku kyautata alaƙarku da sauran mutane, ’yan ƙasa da iyalanku, sannan ku ƙara himma wajen neman ilimi da koyon nau’o’in ƙwarewa daban-daban.

A wannan lokaci, ku yi atisaye wajen yin tunani mai kyau da ƙirƙire-ƙirƙire. Ku kasance masu kare tushen ainihin ƙasarku, mutuncinta da ’yancinta na al’adu, harshenku na uwa, da tsarkakakkiyar tutar Jamhuriyar Musulunci da sauran alamominta.

Ba da daɗewa ba lokaci zai zo da za ku samu matsayinku da rawarku a cikin al’umma. A lokacin, idan kuka gudanar da wannan rawar yadda ya kamata, za ku ɗaukaka kanku da ƙasarku.

A yau, a lokacin da zaluncin tsarin mulkin danniya, musamman gwamnatin Amurka da tsarin yahudawan sahyoniya, ke ƙaruwa, ƙarfin da ya samo asali daga ilimi tare da taƙawa da kyawawan ɗabi’u zai kasance kamar garkuwar ƙarfe da takobi mai kaifi, wanda zai dakile hannayen masu kai hari daga cutar da bil’adama.

A yanzu kuna halartar darussan da wasu tsararraki da suka gabace ku suka taɓa zama a kan kujerunsu na makaranta. Yau waɗannan mutane suna ƙirƙirar ɗaukaka da ƙarfi ga Iran ta Musulunci a fannoni daban-daban na kare ƙasa da mutuncinta. Su za su kasance abin koyi da fitila kuma jagora a gare ku. Kamar yadda kafin su akwai wasu da suka zauna a cikin waɗannan ajujuwa, waɗanda suka zama abin koyi na sadaukarwa, alamomin ɗaukakar ƙasa da gwarazan girma da karamci.

Kalma ta ƙarshe ta shafi malamai da farfesoshi. Dukkanmu muna da bashin malamai waɗanda suka koyar da mu a kowane mataki na karatunmu. Wannan rukunin mutane masu daraja da ƙauna, waɗanda galibi suke samun kyakkyawar ƙauna daga ɗalibansu, sun cancanci a riƙa girmama su a kowane lokaci da wuri.

Mutuncin kai da haƙurin rayuwa da ake yawan gani a tsakanin malamai, bai kamata ya sa masu ruwa da tsaki su gamsu da halin rayuwar da suke ciki a yanzu ba. Da yardar Allah, ta hanyar kyakkyawan tsari da hikima, za a yi ƙoƙari mai inganci wajen inganta rayuwarsu, musamman ganin cewa wannan lamari ya wuce kawai sauke wani nauyi na doka; lamari ne da ya samo asali daga zuciya.

Tsira da rahamar Allah da albarkarsa su tabbata ga farfesoshi, malamai, ɗalibai da ’yan makaranta shahidai na yaƙin da aka tilasta wa Iran na uku, musamman jagoranmu mai hikima kuma babban malaminmu da ya yi shahada, Allah Ya ɗaukaka matsayinsa, wanda yake da babban tasiri wajen saurin ci gaban ilimi a ƙasar.

Godiya ga dukkan masu tarbiyya, malamai da farfesoshi a fagen ilimi, sani da addini. Ina taya ɗalibai da ’yan jami’a masu kyakkyawar makoma na al’ummar Iran murnar wannan sabuwar shekarar karatu tare da yi musu barka da zuwa.

Ina fatan, da addu’ar shugabanmu Imam Mahdi, Allah Ya gaggauta bayyanarsa, za su samu ƙarin nasara wajen kaiwa ga kololuwar ilimi, adabi da ci gaba, in Allah Ya so.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i

31 ga Shahrivar 1405 (22 ga Satumba 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha