A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Ghulam Ali Safa’i Bushehri, memba na Majalisar Kwararru ta Jagoranci, ya bayyana haka a wajen taron sakatarorin Kwamitin Jagorancin I’itikafi na faɗin ƙasar Iran, inda ya jaddada rawar da i’itikafi ke takawa wajen ƙarfafa bangaren gwagwarmaya.
Ya ƙara da cewa, ya kamata a gudanar da i’itikafi tare da mayar da hankali kan gwagwarmaya da ƙarfafa bangaren gwagwarmaya, domin wannan babbar dama ta ruhaniya na iya zama wata muhimmiyar kariya da goyon baya ga ƙoƙarin jihadin bangaren gwagwarmaya da kuma samun nasarar mayaƙan Musulunci.
Wakilin Waliyyul Fakih a Bushehr ya kuma jaddada matsayin ikhlasi a cikin ibada, yana mai cewa: "Karɓuwar ayyuka a kowane matsayi tana da sharadin ikhlasi, domin ikhlasi shi ne jigon ibada. Haka kuma, ɗaukaka da ci gaban mutum suna samuwa ne ta hanyar ikhlasi, kuma mutum mai ikhlasi zai iya kai wa matakan kamala."
Da yake ishara da koyarwar Amirul Muminin (A.S) game da ikhlasi, ya ce Amirul Muminin (A.S) ya bayyana cewa mutum yana samun tsira ne ta hanyar ikhlasi.
Mamban Majalisar Kwararru ta Jagoranci ya bayyana ikhlasi, bauta da ibada a matsayin abubuwa masu alaƙa da juna, yana mai cewa sakamakon ibadoji irin su i’itikafi ya kamata ya kasance ƙarfafa ikhlasi a cikin mutum. Ya ce kiyaye ikhlasi a cikin wannan yalwar abubuwa da bayyanar abubuwa iri-iri na duniya aiki ne mai matuƙar wahala, yayin da Shaiɗan ma yake ƙoƙarin kai hari kan ikhlasin mutane.
Malamain Hauzar ya jaddada cewa, i’itikafi ya kamata ya kusantar da mutum zuwa ga bautar Allah cikin tsantsar ikhlasi, sannan ya zama wata hanya ta ƙarfafa ruhin jihadi, gwagwarmaya da tafiya a kan tafarkin gaskiya.
Ra'ayinka