A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da taron ne a ranar Laraba, 20 ga Rabi’ul Awwal 1448, wanda ya yi daidai da 2 ga Satumba 2026, a ɗakin taro na Shahid Qasim Sulaimani da ke cikin Masallacin Jamkaran. Taron ya samu halartar ɗaliban Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da ke karatu a makarantun Hauza da jami’o’in Iran.
An fara taron da karatun Alƙur’ani Mai Girma, ziyara da addu’o’i, kafin mawaka su gabatar da waƙoƙin yabo ga Manzon Allah (S.A.W.A) da iyalansa tsarkaka. Haka kuma, ayarin waƙen Abna’u Ruhullah ta gabatar da nata shirin na musamman domin ƙara armashi ga taron.
Babban bako a wajen taron shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Al-Mustafa ta Duniya mai kula da harkokin al’adu da tarbiyya, Hujjatul Islam wal Muslimin Dakta Muhammad Ridha Salihi, wanda ya gabatar da jawabi mai cike da darussa kan muhimmancin haɗin kan al’ummar Musulmi.
A cikin jawabinsa, Dakta Salihi ya bayyana ɗaliban Jami’ar Al-Mustafa a matsayin wata alama ta haɗin kan Musulmi a duniya, yana mai cewa an kafa jami’ar ne da manufar ƙarfafa fahimtar juna da haɗin kai tsakanin mazhabobin Musulunci.
Ya bayyana cewa ma’anar haɗin kai ba ita ce mutum ya bar akidarsa ya rungumi akidar wani ba, sai dai sanin maƙiyi na bai ɗaya, tunkararsa tare, da kuma haɗuwa a kan abubuwan da suka zama abin haɗa kan dukkan al’ummar Musulmi.
Hujjatul Islam Salihi ya kuma bayyana wasu ginshiƙai uku na haɗin kai, waɗanda suka haɗa da ƙin bautar wanin Allah da kuma tsayawa kan yaƙi da dagutu da zalunci; tabbatar da bauta da biyayya ga Allah (S.W.T) kaɗai; da kuma ƙauna, tausayi da kulawa tsakanin Musulmi.
Ya bayyana Shahid Qasim Sulaimani a matsayin ɗaya daga cikin fitattun misalan haɗin kai, yana mai cewa ya taka rawa wajen haɗa kan al’ummar Shi’a da Ahlus-Sunna a ƙasashe daban-daban, ciki har da Iran, Iraki, Lebanon, Siriya da Yemen, wajen fuskantar zalunci da ta’addanci.
A wani ɓangare na jawabinsa, ya yi bayani kan hanyoyin da Musulmi za su bi wajen rayuwa cikin zaman lafiya da juna duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, yana mai kawo misalan wasu manyan malamai, ciki har da Allama Amini (R).
Haka kuma, ya tabo batun alaƙar shugabanni da mabiya, inda ya bayyana cewa daga cikin nauyin da ke kan shugaba da mabiyansa akwai yi wa juna addu’a. Ya kuma jaddada muhimmancin bin jagorori daga mabiyan da kuma yin biyayya gare su.
A ƙarshen jawabinsa, malamin ya yi addu’a ga shahidan gwagwarmaya daga ƙasashe daban-daban, tare da roƙon Allah Ya ba rundunonin Mukawama nasara.
Wani abin da ya kara kawata Mauludin shi ne tutar haramin Abul Fadlil Abbas da aka kawo wurin tare da zagayawa da ita a tsakanin mahalarta domin neman tabarruki.
Bayan kammala jawabin, an gudanar da kacici-kacici da gasar wasanni ga ɗaliban Fudiyya, inda aka bai wa waɗanda suka nuna ƙwazo kyaututtuka. Haka kuma, an yanka kek ɗin murnar zagayowar haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A) da Imam Jafar Sadik (A.S), ƙarƙashin jagorancin babban bako tare da taimakon Hujjatul Islam Abdullahi Ahmad Fudiyya da Hujjatul Islam Muhammad Sani Malafa.
A ƙarshe, an bai wa ‘yan wasa da rundunonin Harisawa da JASAZ kyaututtuka bayan gudanar da wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakaninsu, wanda ya ƙare da kunnen doki 3-3.
An rufe taron ne bayan raba walima, inda Sheikh Muhammad Sani Malafa ya jagoranci addu’ar rufe taron.















Ra'ayinka