A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal Muslimin Muhammad Mahdi Mundigari, a yayin jawabinsa a taron murnar zagayowar ranar da Sayyida Fatima Ma'asuma (S) ta zo Qum, yana mai nuni da yin koyi da tarihin rayuwar Sayyida Fatima Ma’asuma (A.S), ya bayyana muhimman alamomi guda biyar na taimakon Waliyyin Allah. Ya kuma bayyana hijirarta daga Madina zuwa Iran domin taimakon Imam Rida (A.S) a matsayin abin koyi mai ɗorewa na hijira, gwagwarmaya da kare Wilaya.
Ya ce, tsayin daka a gaban ɓangaren kafirci da zalunci, karewa da tausayi ga muminai da waɗanda ake zalunta, fifita son Allah da addini a kan son kai da abubuwan duniya, tawali’u ga muminai tare da tsayin daka a gaban makiya, da kuma yin jihadi a tafarkin Allah ba tare da tsoron zargin mutane ba, su ne alamomi biyar na haƙiƙanin mataimakan Waliyyin Allah.
Hujjatul Islam Mundigari ya jaddada cewa gwagwarmaya ba ta takaitu ga fagen soja kawai ba, domin kowane ɓangare na al’umma zai iya taimakawa wajen yi wa addini da al’umma hidima ta hanyar gudanar da nauyin da ya rataya a kansa. Ya kuma bayyana tarbiyyar zuri’a masu imani da ƙwarewa a matsayin ɗaya daga cikin muhimman fannoni na wannan gwagwarmaya.
A ƙarshe, ya bayyana cewa tasirin hijirar tarihi ta Sayyida Fatima Ma’asuma (A.S) har yanzu yana ci gaba bayan ƙarnuka masu yawa, musamman a birnin Qum da kuma wajen yaɗuwar koyarwa da ilimin Ahlulbaiti (A.S).
Ra'ayinka