A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Tehran, an gudanar da taron cikar kwanaki 40 da binne Jagoran Shahidan Juyin Juya Halin Musulunci a Musalla Imam Khumaini da ke birnin Tehran, inda dubban al’umma daga sassa daban-daban suka halarta domin tunawa da Shahidin Jagora tare da sabunta mubaya’a ga Waliyyul Faƙih.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na addini, da ’yan uwa da iyalan Jagoran Shahid, da kuma ɗimbin al’ummar birnin Tehran. Rahotanni sun bayyana cewa yara, matasa da samari sun taka muhimmiyar rawa wajen halartar taron.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin akwai Shugaban ƙasar Iran, Dakta Mas'ud Pezeshkian, Shugaban Majalisar Dokokin Musulunci, Mohammad Baqer Qalibaf; Shugaban Hukumar Shari’a, Hujjatul Islam Mohseni Eje'i; kwamandan Rundunar Quds, Janar Ismail Qa'ani; Ali Nikzad, mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Musulunci; Hujjatul Islam Qomi, shugaban Hukumar Yaɗa Harkokin Addinin Musulunci; Mohammad Mokhber, mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Hali; da Mohammad Reza Aref, mataimakin farko na shugaban ƙasar.
An ɗaga tutocin “Ya Litharatil Khamenei”
Al’ummar Tehran sun fara isa Musalla Imam Khumaini tun kusan ƙarfe 4 na yamma, inda suka ci gaba da kasancewa a wajen har zuwa dare. Mahalarta taron sun riƙe tutocin “Ya Latharatil Khamenei”, tare da jaddada buƙatar ɗaukar fansar jinin Shahidin Jagora da sauran shahidan Juyin Juya Halin Musulunci.
Gwagwarmaya na daga cikin manyan darussan makarantar Shahidin Jagora
A cikin jawabinsa, Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Jawad Haj Ali-Akbari, shugaban Majalisar Tsare-tsaren Limaman Juma’a ta ƙasa, ya ce ɗaya daga cikin manyan darussan da Shahidin Jagora ya bari shi ne gwagwarmaya da tsayin daka.
Ya bayyana cewa sabon matakin gwagwarmaya ya ƙunshi cimma cikakkiyar kariya da hana abokan gaba kai hari, karɓar diyya da asarar da aka jawo, da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifuka.
Hujjatul Islam Haj Ali-Akbari ya kuma bayyana “ramuwar gayya” a matsayin muhimmin buri da al’umma da masu fafutukar gwagwarmaya suke ɗauka, yana mai cewa za a cimma wannan buri ta hanyar tsayin daka, juriya da ci gaba da bin tafarkin Shahidin Jagoran.
Ya kuma yi kakkausar suka ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump, inda ya yi kira da a kawar da tasirin Amurka daga yankin tare da hanzarta faɗuwar mulkin girman kai na duniya.
Shahidin Jagora! gwarzon ilimi, ɗabi’a da jihadi
Hujjatul Islam Wal Muslimin Haj Ali-Akbari ya bayyana Shahidin Jagora a matsayin malami mai zurfin ilimi, zuhudu, kyawawan ɗabi’u da jajircewa wajen gwagwarmaya.
Ya ce Shahidin Jagora ya kai matsayi mafi girma a fannin fikihu da ijtihadi, sannan ya samu babban matsayi a tafiyar ruhaniya, ɗabi’a, haƙuri da jihadi.
Ya kuma bayyana irin alaƙar da ke tsakanin Shahidin Jagora da Imam Khumaini, yana mai cewa Shahidin Jagora ya amfana sosai daga ilimi, ruhaniya, ƙuduri da kuma salon gwagwarmayar Imam Khumaini.
Ya shiga fagen gwagwarmaya tun yana matashi
A cewar Hujjatul Islam Haj Ali-Akbari, Shahidin Jagora ya shiga fagen gwagwarmaya tun farkon shekarun ƙuruciyarsa, inda ya bi tafarkin Imam Khumaini mataki-mataki.
Ya ce daga bisani ya zama amintaccen Imam da al’umma, sannan ya karɓi babbar amanar jagorancin al’umma da tuta daga hannun malaminsa.
Halartar Malaman Hauza
Daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a bikin akwai yawan halartar malaman Hauza.
Hujjatul Islam wal Muslimin Reza'i, limamin Masallacin Amirul-Muminin Ali (AS) da ke Shahrak-e Gharb, ya bayyana cewa malaman Hauza suna tare da al’ummar Iran wajen fuskantar masu girman kai, yana mai cewa malaman Hauza suna ɗaukar kansu a matsayin sojojin Sayyid Mujtaba Khamenei.
A yayin taron, Haj Morteza Taheri, ɗaya daga cikin masu waƙar yabo da makokin Ahlul Baiti (AS), ya gabatar da makokin Shahidin Jagora, lamarin da ya sanya mahalarta taron cikin yanayin jimami da kuka.
Taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila” ya mamaye taron
A yayin bikin, an rika jin taken “Mutuwa ga Amurka”, “Mutuwa ga Isra’ila”, “Mutuwa ga munafukai” da kuma “Mutuwa ga masu ɓarnatar da tattalin arziki.”
Har zuwa kusan ƙarfe 8 na dare, titunan da suka haɗa da Musalla Imam Khomeini sun kasance cike da mahalarta taron, yayin da taken juyin juya hali ke ci gaba da amsa-kuwwa.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Iran sun ce bikin ya zama wata babbar dama ta tunawa da Shahidin Jagora, da kuma jaddada ci gaba da bin tafarkin juriya da gwagwarmaya da ya bari a matsayin wani muhimmin ɓangare na gadonsa.
Ra'ayinka