A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, lokacin hudubar sallar Juma'a a Tehran, Hujjatul Islam Muhammad Jawad Haj Ali Akbari ya bayyana cewa mashigar ruwa na Hormuz da Babul Mandab, sojojin kasar masu karfi, diflomasiyyar makwabtaka, hadin kan kasa, jihadin kiyaye tattalin arziki, da kuma tattalin arzikin gwagwarmaya, su ne ginshikan karfi da tsayayyen matsayin Iran wajen fuskantar makiya.
A cikin jawabin nasa, ya fara da shawarar tsoron Allah ga kansa da dukkan masu sallar, inda ya karanto ayar Alkur'ani mai girma (Suratu An-Nahl: 90) da take umarni da yin adalci, kyautatawa, da taimakon makusanta, tare da hanin aikata alfasha, munkari, da zalunci (wuce gona da iri). Ya bayyana cewa wadannan umarnai su ne tushen takawa.
Haj Ali Akbari ya ci gaba da magana kan falalar Sayyida Zainab (SA) bayan kammaluwar arba'in, inda ya jaddada cewa ita ce babban misali na kamun kai, hakuri, da jajircewa ga mata a tarihin Musulunci. Ya ce, "Idan magana ake ta tashi tsaye don Allah, jihadi a tafarkin Allah, da kuma yaki da dagutu (azzalumai), to Sayyida Zainab (SA) ita ce jagorar da ta nuna wa dan Adam cewa hujja ta tabbata ga kowa ta hanyar misalinta."
Ya kuma tabo batun "rayuwa mai cike da kamun kai da kunya", inda ya bayyana cewa wannan ba wani abu ba ne mai sauki, face yana da matukar muhimmanci wajen kare mutuncin al'umma da kuma kiyaye tsarin iyali. Ya zargi makiya da cewa suna amfani da dabarun yada rashin kunya da tsiraici domin dakile ci gaban al'ummar Musulmi, sannan ya bukaci hukumomi da al'umma su fuskanci wannan kalubale ta hanyar da ta dace, ba tare da motsin rai ba, domin kawar da wannan matsala.
A bangaren siyasa da tsaro, limamin sallar Juma'a ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da kasancewa mai karfi. Ya ce: "Mashigar Hormuz da Babul Mandab suna nan. Karfafa sojojinmu yana nan. Hadin kan kasar nan yana nan. Tattalin arzikin gwagwarmaya yana nan. Muna tsaye daram domin daukar fansar jinin Imam daga makiya, kuma insha Allahu ba za a yi mana bazata ba."
A karshen jawabin nasa, ya gode wa al'ummar Iraki bisa karbar bakuncin mahajjatan Arba'in, sannan ya jinjina wa 'yan jarida a ranar da aka kebe don tunawa da su, tare da girmama shahidan kare harami (mudafe-e haram).
Ra'ayinka