A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza da aka samu daga shafin Dandalin Matasan Harkar Musulunci, Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), na Rasulul Akram Zone, Birnin Kudu Sub Unit, ya gudanar da taron ƙarawa juna sani na tsawon kwanaki biyu da yini ɗaya a garin Sara, ƙaramar Hukumar Gwaram, Jihar Jigawa.
An gudanar da taron ne a ranar Juma’a zuwa Lahadi, 11-13 ga Satumba, 2026, tare da halartar matasan Harkar Musulunci daga yankin, inda aka tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi addini, tarbiyya da zamantakewa.
Jaddada Muhimmancin Neman Ilimin Addini da na Zamani
A cikin jawabin rufe taron, Sheikh Sa’eed Ibrahim Birnin Kudu ya jaddada muhimmancin neman ilimi, yana mai cewa neman ilimi wajibi ne ga kowane matashi, ba tare da la’akari da ko ilimin zamani ne ko na addini ba.
Ya bayyana cewa: “A wajenmu, duk ilimi abu ɗaya ne. Mutane ne kawai suke rarraba shi zuwa ilimin zamani da na addini.”
Malamin ya kuma kawo wata magana da aka rawaito daga Imam Ali (AS), inda ya bayyana cewa da ba don tsoron mutane su faɗa cikin fitina ba, kamar yadda ya faru a kan ilimin Annabi Isa (AS), da ya nuna musu yadda ake fitar da wuta daga ruwa.
Ya ƙara da cewa ilimi yana ci gaba da bayyana a hankali, yana mai kawo misali da ci gaban kimiyya da fasaha, inda abubuwan da a baya ake ganin ba za su yiwu ba, a yau aka gano hanyoyin aiwatar da su.
Bayanin Tarihin Dandalin Matasa da Ayyukansa
A nasa ɓangaren, Malam Shamsuddeen Sabo ya gabatar da jawabi mai taken “Dandalin Matasa; Jiya da Yau”, inda ya yi bayani kan tarihin kafuwar dandalin da kuma ayyukan da matasan suka gudanar a shekarun baya.
Ya bayyana cewa matasan mabiya Sayyid Zakzaky (H) sun taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan jin ƙai da hidimta wa al’umma a ƙaramar Hukumar Birnin Kudu.
Malam Shamsuddeen ya kuma yi magana kan ayyukan tallafawa marayu, yana mai cewa matasan Harkar Musulunci sun kasance daga cikin waɗanda suka fara irin waɗannan ayyuka a faɗin Birnin Kudu, amma daga baya aka mayar da su wasu nau’o’in ayyukan siyasa da neman suna.
Ya ƙarfafi matasan da su ci gaba da ayyukan alheri da Jagora (H) ya ɗora musu, tare da jaddada muhimmancin riƙon jagora guda ɗaya da guje wa duk wani rikici ko husuma, musamman a kafafen sada zumunta.
Ƙarfafa Matasan Kan Mujahada da Kyawawan Ɗabi’u
Malam Abdulmuɗallib Adam ya gabatar da jawabi kan batun mujahada, inda ya ƙarfafi matasan da su rungumi ƙoƙarin gyaran kai da ibada.
Ya ce: “Mujahada ana farawa da kaɗan-kaɗan ne. Misali, mutum zai iya fara nafilar dare da raka’a biyu, sannan a hankali ya ƙara yawan raka’o’in har ya kai inda ake so.”
Ya kuma yi kira ga matasan da su kasance masu kyawawan ɗabi’u, musamman kasancewar su matasa masu riƙon addini.
Kira Ga Matasan Su Ƙara Himma Wajen Riko da Harka
A nasa jawabin, Prof. Safiyanu Sara ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu daga cikin matasa a yanzu suke nuna sakaci ko rauni wajen gudanar da al’amuran Harka, sabanin yadda matasan da suka gabata suka kasance masu jajircewa.
Ya yi nuni da yadda matasan da suka gabata suke ƙoƙarin samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan Harka da kuma halartar tarukanta, yana mai cewa a yanzu ana fuskantar ƙalubale wajen ƙarfafa wasu matasa su shiga irin waɗannan ayyuka.
A ƙarshe, ya ƙarfafi matasan da su ƙara himma wajen riko da hidimta wa Harkar Musulunci, tare da kasancewa masu haƙuri da juriya, yana mai bayyana cewa wannan hanya tana daga cikin hanyoyin samun tsira a duniya da lahira.
Kammala Taron da Yawon Buɗe Ido
A wani ɓangare na taron, mahalarta sun gudanar da hawa dutse da yawon buɗe ido, domin motsa jiki, nishaɗi da ƙarfafa haɗin kai da zumunci a tsakaninsu.
An kammala taron cikin nasara, inda mahalarta suka bayyana farin ciki da gamsuwarsu da yadda aka gudanar da shi. Daga bisani aka yi addu’a, sannan aka sallami mahalarta.













Ra'ayinka