A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, da safiyar yau Alhamis, 30 ga Yuli, 2026, al'ummar Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun fara tattakin Arba'in daga yankin Kano domin tunawa da cikar kwanaki arba'in da shahadar Imam Hussain (A.S.), iyalansa da sahabbansa a filin Karbala.
Rahoton wakilin Hauza ya nuna cewa, mahalarta tattakin sun fito ne daga Kano da sauran garuruwa da suka haɗa da Potiskum, Azare, Gashua, Jigawa da sauran yankuna, inda suka fara tafiyarsu daga ƙarƙashin gadar sama ta Kofar Nassarawa da ke cikin birnin Kano.
Kafin fara tattakin, an gudanar da taron manema labarai, inda wakilin almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Da'irar Kano da kewaye, Shaikh Dakta Sunusi Abdulkadir, ya yi bayani kan maƙasudi da muhimmancin tattakin Arba'in. Haka kuma ya yi bayani kan yadda al'amuran Ashura suka faru tare da bayyana manyan darussa da sakonnin da ake koya daga juyin Imam Hussain (A.S.).
Bayan kammala taron, mahalarta tattakin sun fara tafiya cikin tsari, inda suka bi hanyar Zaria Road zuwa Unguwa Uku, sannan suka wuce ta Na'ibawa zuwa Kasuwar Magani ta Dan Gauro.
Daga nan ne suka yada zango a Rukunin Gidajen Kwankwasiyya domin gudanar da sallar farilla da cin abinci, kafin daga bisani su ci gaba da tafiyarsu zuwa zangon kwana.
Ana gudanar da tattakin Arba'in a kowace shekara a sassa daban-daban na Najeriya, inda dubban masoya Ahlul Baiti (A.S.) ke shiga domin nuna biyayyarsu ga manufofin Imam Hussain (A.S.) da kuma raya sakon Ashura na adalci, gaskiya da tsayin daka wajen fuskantar zalunci.







Ra'ayinka