A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a waɗannan kwanaki da darare, Iraniyawa masu kishin ƙasa suna cikin taruka daban-daban na bankwana da gangar jikin Imam da jagoransu Shahid, cikin wani yanayi na musamman. Suna cikin baƙin ciki da jimami, amma baƙin cikin da ke isar da saƙon jarumtaka da kuma neman ɗaukar fansa ga duniya.
Hakikanin gaskiya ita ce Shahid Ayatullah al-Uzma Imam Sayyid Ali Khamenei mutum ne wanda duk da wahalhalu, suka da zarge-zargen da ya fuskanta, bai taɓa ja da baya ko da na ɗan lokaci daga cika nauyin da ya ɗauka na addini da imani ba. Ya kasance mai cikakken imani da manufofinsa waɗanda suka kasance bautar Allah Maɗaukaki da hidima ga bayinSa, har zuwa lokacin da ya sadaukar da ransa saboda akidarsa, tare da wasu daga cikin masoyansa, inda mafi munin maƙiyan ƙasar Iran suka kashe su.
Saboda haka, shahadar Imam Khamenei, duk da cewa ta bar babban baƙin ciki ga al'ummar Iran da al'ummar Musulmi, ya kamata a sani cewa tarihi ba ya tuna manyan shugabanni ne kawai saboda shekarun mulkinsu, sai dai saboda tunaninsu, manufofinsu, al'adunsu da mutanen da suka tarbiyyantar.
Muhimman siffofin makarantar tunanin Imam Khamenei
Ba don komai ba ake cewa babban gadon da manyan shugabanni ke bari ba gine-gine ko abubuwan duniya ba ne, sai dai makarantar tunaninsu. Daga wannan mahangar, gadon Shahidin jagora yana bayyana a al'adar gwagwarmaya, ruhin neman 'yancin kai da yaƙi da girman kai, imani da jama'a da ya samo asali daga tauhidi, zurfin ruhaniya, da kuma tarbiyyar ƙarni mai imani, wayewa da jarumtaka wanda ke shirye da ɗokin ci gaba da wannan tafarki zuwa kololuwar gaba.
Ƙarfin ilimi; injin ci gaban ƙasa
Zainab Safa'i, marubuciya kuma mai bincike a fannin ilimin ɗan Adam, ta ce: "A cikin tsarin tunani da aikace-aikacen Shahidin jagoran juyin juya hali, wanda za a iya bayyana a matsayin makaranta, akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin jajircewar addini, hankali na kimiyya da dabarun siyasa. Wannan makaranta ba kawai tarin matsayai na akida ba ce, a'a, taswirar dabaru ce ta bunƙasa wayewa wajen fuskantar ƙalubalen zamani da rikitarwar duniyar yau."
Ta ƙara da cewa: "Babu shakka ɗaya daga cikin manyan nasarorin wannan makaranta shi ne karkatar da manufofin Jamhuriyar Musulunci zuwa ga ci gaban ilimi bisa dogaro da ilimin cikin gida da dogaro da kai. Imam Khamenei, wanda shi kansa masani ne kuma marubuci, ya kasance yana jaddada cewa ilimi shi ne kawai hanyar ceton al'umma a sabuwar duniya, kuma ya bayyana cewa ƙarfin ilimi shi ne injin ci gabanmu."
Ta yi nuni da gagarumin ci gaban ƙasar a fannonin ilimin dabaru cikin shekarun baya, tana cewa: "A cikin shekarun baya an samu ci gaba na musamman a fannoni masu muhimmanci; daga zama cibiyar yanki a likitancin nukiliya da fasahar nanotechnology zuwa bunƙasar masana'antun tsaro da samun cikakken dogaro da kai wajen ƙera na'urori masu rikitarwa. Wannan ci gaba ya samo asali ne daga ƙudurin ƙasa bisa hangen nesa na Shahidin jagora wanda yake kallon yaƙi da ilimi a matsayin wata makarkashiyar mulkin mallaka."
Bukatar kiyaye da ƙarfafa 'yancin kan ƙasa
Ta kuma tunatar da cewa: "Tsara dabarar 'Mutunci, Hikima da Maslaha' a manufofin ƙetare da ƙarfafa ƙarfin kariyar soja ba wai don kare ƙasa kawai ba ne, har ma domin kiyaye ikon yanke shawara cikin duniyar da ke da manyan ƙarfi da dama, ta yadda Iran za ta ci gaba da tafiya cikin mutunci da dogaro da kai har ta zama abin koyi ga sauran ƙasashe."
Ta ƙara cewa: "Babban ginshiƙin wannan makaranta shi ne ci gaba da jaddada haɗin kai. A cikin rayuwa da maganganun Shahidin jagoran, guje wa haifar da rabuwar kawuna a tsakanin al'umma da siyasa wata ƙa'ida ce ta asali wadda ke ba da damar haɗa mutane da yawa. Haka kuma jaddada asalin Iran ta Musulunci da girmama dukkan ƙabilu, mazhabobi da rukunin jama'a shi ne ginshiƙin gina Iran mai haɗin kai. A ganinsa, duk wata rarrabuwar kawuna tana raunana tsarin ƙasa a gaban maƙiya."
Hankalin addini a ƙarƙashin haɗin kai na ƙasa
Safa'i ta kuma ce: "Makarantar tunanin Shahid Khamenei ta tabbatar da cewa da dogaro da hankalin addini, ƙudurin ƙasa da haɗin kai, ana iya tsayawa tsayin daka a gaban mafi rikitarwar lamuran ƙasa da ƙasa, har ma a hanzarta ci gaban ƙasa. Kiyaye da bunƙasa wannan gado mai daraja yana buƙatar sabon ƙarni ya fahimci wannan makaranta tare da aiki da ruhinta na haɗin kai, ilimi da adalci, domin makomar Iran mai ƙarfi tana cikin ci gaba da wannan tafarki da kuma kare wannan gado."
Jaddada kare asalin Iran da Musulunci
Dokta Mahdi Islami, mamba a kwamitin ilimi na Cibiyar Bincike ta Imam Sadiƙ (AS), ya ce: "Gadon tunanin Shahidin jagora ya ƙunshi tarin ra'ayoyi da hanyoyi a fannoni daban-daban na siyasa, zamantakewa, addini da hulɗar ƙasa da ƙasa. Wannan gado yawanci yana bayyana ne ta cikin jawabai, rubuce-rubuce, littattafai, manufofi da umarnin gudanarwa."
Ya ƙara da cewa: "Daga cikin manyan abubuwan da wannan gado ya ƙunsa akwai jaddada batun ainihi, wato manufofi da shirye-shiryen ƙasa su kasance wajen kare da ƙarfafa asalinmu na Iran da Musulunci, domin mutuncin ƙasarmu yana da alaƙa da wannan batu."
Malamin jami'ar ya ci gaba da cewa: "Har ila yau, kamar yadda aka sha faɗi, ɗaya daga cikin ginshiƙan gadon tunanin Shahidin jagora shi ne yaɗa 'al'adar gwagwarmaya'. Wannan ya haɗa da jure wa takunkumin tattalin arziki, dogaro da kai a masana'antun dabaru da kuma rashin mika wuya ga matsin lambar maƙiya. Wannan ruhin 'yanci da neman 'yancin kai yana da tushe a tunanin Imam Khumaini, kuma Shahid Imam Khamenei ya ci gaba da wannan tafarki."
Ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan al'ummar Musulmi
Ya bayyana cewa: "A matakin duniyar Musulunci, ra'ayoyinsa sun wuce iyakokin Iran, suna mai da hankali kan kare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin Musulmi wajen fuskantar maƙiya, tare da wayar da kai game da fitintinu da makircin maƙiyan Musulunci."
Malamin jami'ar ya tunatar da cewa: "A makarantar tunanin Imam kuma jagoranmu shahidi, yaƙi da tsarin mamaya yana yiwuwa ne idan Musulmi sun haɗu tare da hikima wajen fuskantar ƙarfin kafirci da zalunci. Ya sha jaddada cewa duniyar Musulunci ta nisanci tsarin ƙasa da ƙasa da manyan ƙasashen masu girman kai ke mamaye, ta kuma yi ƙoƙarin samar da sabon tsari bisa adalci. Haka kuma ya kasance yana jaddada muhimmancin goyon bayan manufar Falasdinu da kuma fifita batun Kudus Mai Tsarki.
Ra'ayinka