Laraba 1 Yuli 2026 - 17:54
Saƙon Nuna Goyon Baya Da Kira Ga Adalci Daga Fasto Yohanna Buru A Wajen Taron Ashura A Kaduna

Hauza/ A yayin gudanar da taron tunawa da Ashura wanda aka gudanar a ranar 10 ga watan Muharram 1448H (25 ga Yunin, 2026) a birnin Kaduna, Fasto Yohanna Buru ya jaddada muhimmancin adalci tare da nuna cikakken jajantawa kan musibar da ta afku a Waƙi'ar Karbala.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Fasto Buru a farkon jawabin nasa ya bayyana godiyarsa ga waɗanda suka shirya taron, inda ya bayyana alhininsa kan musibar da ta afku ga iyalan gidan Manzon Allah (SAWW). Ya ce: "Na ji daɗin kasancewa a wannan taro, kuma ina miƙa saƙon jajantawa ta zuwa ga iyalan gidan Manzon Allah da dukkan waɗanda suke cikin baƙin ciki kan wannan babban al'amari."

Fasto Buru ya yi nuni da matsayin ranar Ashura a tarihi da kuma addini, inda ya lura cewa ko da yake mabiyan addinai daban-daban suna kallon wannan rana ta fuskoki mabambanta, amma bincikensa ya nuna cewa abin da ya faru ga iyalan gidan Manzon Allah a Waƙi'ar Karbala, babban zalunci ne. Ya bayyana cewa: "A matsayina na malamin addinin Kirista, bayan binciken da na gudanar, na fahimci cewa an yi wa iyalan gidan Manzon Allah (SAWA) zalunci a Waƙi'ar Karbala."

Har ila yau, ya yi magana kan koyarwar Annabi Isa (AS) ta fuskar fahimtarsa, inda ya jaddada muhimmancin addu'a, azumi, da kuma dogaro ga Allah a lokutan tsaka-mai-wuya da kuma fuskantar ƙalubale.

A ƙarshen jawabin nasa, Fasto Yohanna Buru ya aika da saƙo ga al'ummar Najeriya, inda ya yi kira da a rungumi al'adun adalci da zaman lafiya. Ya bayyana cewa: "Zaman lafiya mai ɗorewa ba zai taɓa samuwa ba sai idan an tabbatar da adalci tsakanin dukkan al'ummar ƙasa."

A ƙarshe, ya yi addu'a ga ƙasar Najeriya, yana roƙon Allah Ya ba da tsaro, haɗin kai, da kuma ikon rayuwa cikin adalci da zaman lafiya ga dukkan al'ummar ƙasar.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha