Jummaʼa 26 Yuni 2026 - 15:10
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (45) | Matsayin Intizar A Al'adar Shi'a (Kashi Na Hudu)

Hauza/ Jiran bayyanar Imam Mahdi (A.S) ba ya nufin sauke nauyin da ke kan mutum, kuma ba ya ba da damar jinkirta ayyukan kwarai. Sakaci da nuna halin ko-in-kula ga ayyukan addini ba abin amincewa ba ne ta kowane fanni.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da wannan jerin bahasin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa" ga ku masu daraja, da nufin yaɗa koyarwa da ilimi mai zurfi da ke da alaƙa da Imam na Zamani (Allah Ya gaggauta bayyanarsa).

Duk da bayyanar da kuma tabbacin ma'ana ta gaskiya ta jiran bayyanar Imam (Intizar), akwai fassarori da fahimta mabanbanta da aka gabatar a kansa. Wani babban ɓangare na waɗannan ra'ayoyi ya shafi fahimtar masana da malamai, yayin da wani ɓangaren kuma ya shafi fahimtar wasu mabiya tafarkin Shi'a kan lamarin jiran bayyanar.

Akwai manyan fahimta guda biyu (2) a wannan fage:

1. Fahimta Ta Gari Kuma Mai Gina Al'umma

Zamanin jiran bayyanar Imam (Intizar) wanda ke kawo ci gaba, motsi, da riƙe amana, shi ne ainihin jiran gaskiya wanda a cikin riwayoyi aka bayyana shi a matsayin "mafi falalar ibada" kuma "mafi daukakar jihadi na al'ummar Manzo (S.A.W.W)."

Marigayi Allamah Muzaffar (1) a cikin wani ɗan gajeren bayani mai gamsarwa, ya fassara jiran bayyanar (Intizar) kamar haka: "Ma'anar jiran bayyanar mai gyara na gaskiya kuma mai ceto na Ubangiji, wato Hazrat Mahdi (A.S), ba ya nufin cewa Musulmi su nade hannayensu su zauna ba tare da gudanar da ayyukansu na addini ba, ko kuma su yi sakaci da abin da yake wajibi a kansu kamar taimakon gaskiya, raya dokoki da umurnin addini, jihadi, da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna; da sunan cewa wai suna jiran sarki daga zuriyar Muhammad (A.S) ya zo ya daidaita kowane abu. Kowane Musulmi yana da nauyin ganin kansa a matsayin mai riƙo da umurnin Musulunci; kada ya yi ƙasa a guiwa wajen neman sanin addini ta hanya ta gaskiya, kuma kada ya fasa umurni da kyakkyawa da hani da mummuna gwargwadon ikonsa; kamar yadda babban Manzo (S.A.W.W) ya ce:

«کُلُّکُمْ رَاعٍ وَ کُلُّکُمْ مسؤول عَنْ رَعِیَّتِهِ»;

"Dukanku masu kiwo ne kuma dukkan ku abin tambaya ne game da abin da aka ba ku kiwo." (Biharul Anwar, Juzu'i na 72, Shafi na 38) 

Bisa wannan, Musulmi ba zai iya barin ayyukansa na wajibi ko ya yi sakaci da su ba da sunan cewa yana jiran bayyanar Mahdi mai gyara; domin jiran bayyanar ba ya sauke nauyi kuma ba ya bayar da lasisin jinkirta aiki na gari. Kasala a cikin ayyukan addini da rashin damuwa da su ba abin amincewa ba ne ta kowane fuska. (Aƙa'idul Imamiyyah, Shafi na 118)

A takaice, ingantacciyar al'ada ta jiran bayyanar Imam tana tsaye ne a kan ginshiƙai guda uku (3):

 A. Rashin gamsuwa ko amincewa da yanayin da ake ciki na yanzu (na zalunci);

 B. Samun kyakkyawan fata na samun makoma mai kyau a gaba;

 C. Motsi da kokari don tsallake yanayin yanzu zuwa ga yanayi mai kyau da ake bukata.

2. Fahimta Ta Kuskure Kuma Mai Rushe Al'umma

Jiran bayyanar mai rushewa da hana ci gaba, wanda a zahiri yake zama wani nau'i na "halatta kowane zunubi" (Ibahiyyah), a koda yaushe manyan malaman addini suna suka da yin tir da shi, kuma sun gargaɗi mabiya makarantar Ahlul Baiti (A.S) da su nesanci wannan mummunar fahimta.

Allama Mutahhari (Q.S) ya rubuta a kan haka cewa: "[Wannan nau'in jiran bayyanar] fahimta ce ta duba na sama-sama na mutane game da Mahdawiyya da tawaye da juyin juya hali na Mahdi da aka yi alkawari (A.S), wanda suke ganin abin zai faru ne kawai ta hanyar lalacewar al'umma; wai kawai lokacin da zalunci, wariya, matsin lamba, murkushe hakki, da barna suka mamaye ko'ina.

Wannan irin fahimta game da bayyanar ta Imam Mahdi (A.S), da wannan irin jiran sauƙi wanda ke kaiwa ga dakatar da iyakoki da dokokin Musulunci, kuma wanda ya kamata a lissafta shi a matsayin halatta sabon zunubi, ba ya dacewa ta kowace hanya da mizanan Musulunci da na Alƙur'ani." (Kiyam da Inkilab-e Mahdi A.S, Shafi na 54) 

Babban wanda ya kafa tsarin Musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (Imam Khumaini), a cikin jawabansa masu daraja bayan ya fito da kuskuren waɗannan fahimta na Intizar, ya caccaki waɗanda ke da irin waɗannan tunani na banza. (Sahife-ye Noor, Juzu'i na 21)

Sabo da haka, mai jiran bayyanar gaskiya, ba zai taɓa zama mai kallon kallo kawai ba a gaban bayyanar da juyin juya halin Mahdi (A.S) da aka yi alƙawari.

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko ne daga littafin "Darsname-ye Mahdaviyyat" na Khodamurad Salimiyan, tare da ɗan gyara kaɗan

Bayanai Na Kasa:

(1) Muhammad Ridha al-Muzaffar (1322 - 1383 H.Q) sanannen Mujtahidi ne, masanin fikihu, usul, ilimin kalam, masanin falsafa, kuma daya daga cikin masu bincike na Shi'a a fagen fikihu, usul, mandik (logic), kalam da akida.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha