Laraba 10 Yuni 2026 - 14:39
Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Hauza/ Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya jaddada muhimmancin yin amfani da kafafen sadarwa na zamani cikin balaga da sanin ya kamata, tare da yin kashedi kan karkatar da manufofinsu.

A cewar rahoton da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito daga shafin Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), Jagoran ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 23 ga watan Zhul Hijja, 1447 (9 ga Yuni, 2026), yayin da yake gabatar da jawabin rufe taron "Mu'utamar na Dandalin TikTok" wanda aka gudanar a gidansa da ke Abuja.

Sheikh Zakzaky ya bayyana kafafen sadarwa a matsayin daya daga cikin mafi muhimmancin hanyoyin isar da sako a wannan zamani. Ya yi ishara da yadda isar da sako ya taka rawar gani a tarihi, inda ya bada misali da lokacin Manzon Rahama (S), da zamanin Sheikh Usman Danfodiyo (R.A), da kuma nasarar da Imam Khumaini (QS) ya samu, yana mai nuni da cewa kowane zamani yana da irin salon da ake isar da kira.

Haka zalika, Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa wadannan kafafe "takobi ne mai kaifi biyu", inda ya ce ana iya amfani da su wajen yin kyakkyawan aiki ko kuma mummuna, kuma hakan ya dogara ne ga yadda mutum ya sarrafa su.

Daga cikin muhimman batutuwan da ya taɓo, akwai jan hankali kan yadda wasu ke ciro guntun magana ba tare da lura da farkonta ko karshenta ba. Ya ce: "Ya kamata magana ta zo daga tushenta, domin idan aka cire ta daga ma'anar da aka yi ta akai, to za ta rasa asalin manufarta." Ya yi kira ga masu amfani da kafar sadarwa da su rika kiyaye amincin sako yayin yada shi.

A karshen jawabinsa, Jagoran ya shawarci matasa da su guji yin zage-zage da kalaman batanci a shafukan sada zumunta. Ya kuma gargade su kan bin wasu abubuwa da ake yayatawa (trending) wadanda ba su da amfani, wadanda aka kirkiro su ne kawai don karkatar da hankalin mutane daga abubuwan da suka fi muhimmanci.

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Sheikh Zakzaky Ya Yi Kira Da A Yi Amfani Da Kafafen Sadarwa Ta Hanyar Da Ta Dace

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha