Litinin 25 Mayu 2026 - 22:52
Bayani Kan Rayuwar Ilimi da Halayyar Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Talkhabi ya bayyana bangarori daban-daban na halayyar Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, inda ya ce: "Duk da cewa shi dan babban jagora ne (Agazadeh), amma ba a taba ganin halayyar girman kai ko nuna isa ta 'ya'yan manya a tare da shi ba. Tawali’unsa na gaskiya ne, kuma wadanda suka yi mu’amala da shi ne kadai za su iya bayyana zurfin wannan dabi'a tasa."

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a wani taro na malamai da aka gudanar a makatantar Hauzar Imam Kazim (A.S) da ke Qum, Hujjatul Islam Talkhabi ya jaddada matsayin ilimi na Ayatullah Mujtaba Khamenei da rawar da yake takawa wajen koyar da dalibai da rubuce-rubucen fikihu.

Matsayin Ilimi a Tsarin Karatun Hauza 

Hujjatul Islam Talkhabi ya bayyana cewa ana gane darajar malami ne ta hanyar malamansa, dalibansa, ko kuma ayyukan da ya rubuta. Ya kara da cewa Ayatullah Mujtaba ya kwashe shekaru yana karatu a gaban manyan maraji'ai kamar Ayatullah al-Uzma Wahid Khorasani da Ayatullah al-Uzma Shubairi Zanjani.

Horar da Shahararrun Dalibai

Yawancin daliban da ya koyar yanzu haka suna koyarwa a manyan matakan koli (Sutuhe Aliyah) a Hauzar Qum, wasu kuma suna koyar da "Darsul-Kharij" (matakin koli na fikihu). Har ila yau, bincikensa kan "Khabar Wahid" ya sami yabo sosai daga masana fannin bincike.

Halayyar Aiki da Tawali'u

Hujjatul Islam Wal Muslimin Talkhabi ya bayyana cewa Ayatullah Mujtaba ya kasance mai kiyaye mutuncin mahaifinsa (Jagora). Ya ambaci cewa lokacin da aka ba shi shawarar shiga majalisar kwararru (Khubrugan) ko wasu mukamai, yakan kin amincewa don kada ya haddasa surutu ko matsala ga Jagora.

Haka kuma, ya bayyana cewa shugaban kasa Dr. Pezeshkian ya samu matukar tasiri da ganin tawali’unsa. Ayatullah Mujtaba yakan raka baki har zuwa kofa idan za su tafi, wanda hakan ke nuna tsantsar kankan da kai.

Damuwa da Masu Karamin Karfi da Dalibai

Daya daga cikin muhimman siffofinsa ita ce kulawa da fakirai da mabukata a boye. A birnin Qum, yana bin diddigin matsalolin unguwannin da ba su da karfi ba tare da mutanen wurin sun san ko waye ke taimaka musu ba. 

Bugu da kari, yana da matukar damuwa kan yanayin rayuwar daliban addini. Hujjatul Islam Talkhabi ya ba da misalin yadda bayan ya kai masa kukan halin matsin tattalin arziki na dalibai, tun kafin ya koma gida, Ayatullah Mujtaba ya riga ya kira cibiyoyin da abin ya shafa don magance matsalarsu.

Sanin Al'amuran Tsaro, Siyasa da Zamantakewa

A karshe, Hujjatul Islam Talkhabi ya bayyana cewa Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei yana da cikakken sani da fahimta kan al'amuran soja, siyasa, da zamantakewa, wanda hakan ke bayyana ga duk wanda ya taba zama da shi.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha