Litinin 18 Mayu 2026 - 23:28
Jaddada Rawar Iran a Cikin Samuwar Sabon Tsarin Yanki a Taron Bursa na Turkiyya

Hauza/ Jam'iyyar 'Vatan' ta Turkiyya a wani taro da ta gudanar a birnin Bursa mai taken "Sakamakon Juriya (muƙawama) ta Iran a cikin tsarin Asiya mai tasowa", ta jaddada rawar Iran wajen canza ma'aunin yanki. Dogu Perincek a wannan taron, ya dauki juriyar Iran a matsayin abin da ya karya burin Amurka da Isra'ila, kuma ya bukaci samuwar kawance tsakanin "Iran, Turkiyya, Rasha da Sin" a gaban tsarin yamma.

A cewar rahoton sashen kasa da kasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Jam'iyyar 'Vatan' ta Turkiyya a birnin Bursa ta gudanar da taro mai taken "Sakamakon Juriya ta Iran a cikin tsarin Asiya mai tasowa". A wannan taron, Dogu Perincek shugaban Jam'iyyar Vatan, Ali Ozgunduz wakilin majalisa na Istanbul a Majalisa ta ashirin da hudu, da Abulƙasim Tahmasebi babban jami'in diflomasiyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi jawabi. Wannan shiri ya samu karbuwa mai yawa daga mahalarta, kuma masu halarta sun gabatar da tambayoyi da dama ga masu jawabi. Abin lura shine, wannan taron ya kusan kai awa uku.

Wannan shiri ya fara ne da yin shiru na minti daya da karanta taken kasar Turkiyya. Dilek Cinar shugabar sashen lardi na Jam'iyyar Vatan a Bursa, a jawabinta na bude taron ta ce manufar wannan taro shine duba "Nasasar Iran" da rawar da Turkiyya take takawa a cikin sabbin sauye-sauyen yanki. Da take bayyana cewa Iran ta "durkusar da" Amurka da Isra'ila, ta kara da cewa: "Amurka ba ta cimma ko daya daga cikin manufofinta na siyasa ba. Sun sha kashi a Iran, kuma wannan lamari yana da muhimman darussa ga kasarmu."

Yankin Jarumai

Dogu Perincek a jawabinsa, yayin da yake nuni ga samuwar sabon tsarin duniya, ya ce: "Sabuwar duniya tana kan kafawa, kuma a sahun gaba na wannan sabuwar duniya akwai bangaren ɗan adamtaka. Iran tana yaki domin ɗan adamtaka (insaniyya), kuma tana yaki domin Turkiyya. Falasdinu, Hamas, Hizbullah, da Yaman su kuma suna yaki domin dukkan bil'adama. Yammacin Asiya yanzu ya zama yankin jarumai."

Ya kuma kwatanta Turkiyya a matsayin kasa da take sahun gaba a sauye-sauyen yanki, kuma ya yi ikirarin cewa Amurka, Isra'ila da Girka a gabashin Bahar Rum sun kafa kawance a kan Turkiyya. Perincek yayin da yake nuni ga atisayen soji na hadin gwiwa na wadannan kasashe, ya ce: "Atisayen tsallaka kogin Maritsa yana nufin shirye-shiryen shiga cikin kasar Turkiyya. Har yanzu bindigogi da tankokin Amurka da Isra'ila ba su zo bakin kofar gidanmu ba, amma wadannan shirye-shiryen soji suna yi mana gargadi game da makoma."

Ba za mu tsaya kallo daga baranda ba

Shugaban Jam'iyyar Vatan ya jaddada cewa: Turkiyya ba za ta iya tsayawa kallon yakin Falasɗinawa a Gaza, muƙawamar Yaman, da yakin Hizbullah ta Lebanon "daga baranda" ba, ya kara da cewa: "Idan an nufi Turkiyya da bututun bindigogi a yau, gobe kuma za a harba mana harsashinsu."

Lissafin Muƙawama 

Perincek ya dauki muƙawamar Iran a matsayin sakamakon "neman shahada, hankali da ilimi", kuma ya bayyana cewa Iran ta sami damar tsayawa tsayin daka a kan hare-haren Amurka da Isra'ila ta hanyar tsarin dabara mai kyau. Ya ce: "Tare da Iran, an samar da bangaren ƴan adamtaka; daga Rasha da Sin zuwa kasashen Larabawa, Nicaragua, Cuba, Mexico, har ma da Kiristocin Turai. Firaministan Spain dan Katolika ma yana cikin wannan bangare. Iran ta sami damar samar da dabara a kusa da ita, wanda mu ma ya dace mu koya da kyau."

Ya kara da cewa: "Iran ta fahimci ko wanene makiyinta da kuma wanene abokinta. Wannan lissafin siyasa ne, kuma Turkiyya ma don kare kanta daga barazanar Amurka da Isra'ila, dole ne ta samar da irin wannan ma'auni."

Amurka da Isra'ila suna tsoron wannan ma'auni

Perincek ya ce ra'ayin kawancen "Turkiyya, Rasha, Sin da Iran" shekaru ana ta gabatarwa daga Jam'iyyar Vatan, amma yanzu a cikin gwamnatin Turkiyya ma wannan ra'ayi yana kara karfi.

Ya kara da cewa: "Amurka da Isra'ila suna tsoron wannan ma'auni. Kamar yadda Mista Devlet Bahceli ma ya ce, a gaban kawancen mugunta na Amurka da Isra'ila, dole ne a samar da kawancen ɗan adamtaka na Turkiyya, Rasha, Sin da Iran."

Shirye-shirye uku kan makomar Turkiyya

Shugaban Jam'iyyar Vatan ta Turkiyya haka kuma ya bayyana manyan abubuwa uku na shirinsa na siyasa, ya ce Turkiyya: dole ne ta koma kan tattalin arzikin da ya dogara da samarwa, ta kuma dawo da jarin da aka tara a bankunan yamma cikin kasar. Ya yi ikirarin cewa kusan dala biliyan 500 na jarin attajiran Turkiyya ana ajiye su ne a bankunan London, New York da Switzerland, kuma gwamnati ta yi amfani da ikon doka ta dawo da wadannan jari a cikin samarwa na cikin gida.

Perincek yayin da yake nuni ga hadakar kasa a Turkiyya, ya ce: "Amurka da Isra'ila sun yi kokarin raba Turkiyya, amma yanzu Kurdawan mu ma sun shiga tsarin 'Turkiyya ba tare da ta'addanci ba' ko kuma a mafi daidai 'Turkiyya daya'. Za mu hada Turkiyya da gwamnati da al'umma daya."

Ya ci gaba da bukatar samuwar "Turkiyya ta mutane masu mutunci" ya ce: "Muna son Turkiyya inda mutane ke rayuwa da aiki da kokari, ba Turkiyya ta 'yan fashi da rashawa ba. Al'adun son kai da ra'ayin kansa sun shigo cikin al'ummarmu daga yamma, kuma dole ne mu sake farfado da al'adun sadaukarwa da ruhaniya."

Kawance da Iran, Rasha da Sin ba zabi mai sauki bane

Perincek a wani bangare na jawabinsa ya jaddada cewa: "Wannan kawance ba kawai zabin manufofin harkokin waje bane; a'a, hanya ce ta gina sabuwar Turkiyya; Turkiyya da ta ginu a kan 'yan uwantaka, samarwa, hadin kai da ruhaniya."

Sakon karamin jakadan Iran

A farkon taron, Ahmad Mohammadi karamin jakadan Iran a Istanbul, a cikin sakon Abulƙasim Tahmasebi da ya karanta, yayin da yake tunawa da shahidan makarantar 'yan mata ta Minab da sauran wadanda suka rasa rayukansu a yakin baya-bayan nan, ya ce: "A cikin kwanaki arba'in na juriya, gwamnatin Turkiyya da al'ummar Turkiyya sun nuna goyon baya da tausayawa a fili."

Ya gode wa Recep Tayyip Erdogan, Hakan Fidan ministan harkokin wajen Turkiyya, da Numan Kurtulmus shugaban majalissar Turkiyya, sannan kuma ya gode wa goyon bayan jam'iyyar Vatan da Dogu Perincek ga Iran. Ya kuma yaba wa rawar da jaridar Aydinlik da gidan talabijin na Ulusal suka takawa wajen yada labaran yakin Iran.

Duniya bayan wannan yakin ba za ta zama kamar da ba

Karamin jakadan Iran ya ci gaba da jawabinsa yana mai jaddada cewa yakin baya-bayan nan ya shigar da tsarin kasa da kasa a wani sabon mataki. Ya lissafta manyan sakamako uku na wadannan sauye-sauye, ya kara da cewa: Rage karfin masu iko, musamman Amurka da Isra'ila; rage amincewar wasu gwamnatocin yanki ga lamunin tsaro na Amurka; da karfafa matsayin Iran a tsarin tsaro na Gabas ta Tsakiya da kara karbuwar Iran a matsayin mai taka rawa a tsarin duniya mai tasowa, sune manyan sakamako uku na yakin da aka kallafawa Iran na uku.

Ya kara da cewa: "Tare da kara rawar da Asiya ke takawa a makomar tsarin kasa da kasa, kawancen Turkiyya, Rasha, Sin da Iran ya sami muhimmanci mai rai."

Dukkan matan Iran suna cikin bangaren nuna haƙƙin ɗan adamtaka

A bangaren tambaya da amsa na taron, an tambayi Abulƙasim Tahmasebi game da rawar da matan Iran suke takawa a muƙawama, sai ya amsa da cewa: "Makiya sun yi tunanin za su iya ruguza Iran a cikin kwanaki hudu, amma ba su san al'ummar Iran ba. Sakon matan Iran ga matan Turkiyya shine, cewa matan Iran, masu lullubi, masu karancin lullubi, da marasa lullubi, musulma da wadanda ba musulma ba, dukkansu suna cikin bangaren nuna haƙƙin bil'adama a kan mulkin mallaka."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha